Attajirin duniya, Elon Musk, ya sami kwatankwacin kudin Dangote a awa 8

A cikin awa takwas, attajirin da ya fi kowa kudi a duniya, Elon Musk, ya sami Dalar Amurka biliyan 14, wato Naira tiriliyan shida, kwatankwacin ilahirin abin da wanda ya fi kowa kudi a Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya mallaka. Kudin dai, wadanda ya samu ranar Laraba, sun haura Dala biliyan 13.9 da Dangote ya […]

Attajirin duniya, Elon Musk, ya sami kwatankwacin kudin Dangote a awa 8

Aliko Dangote da Elon Musk

A cikin awa takwas, attajirin da ya fi kowa kudi a duniya, Elon Musk, ya sami Dalar Amurka biliyan 14, wato Naira tiriliyan shida, kwatankwacin ilahirin abin da wanda ya fi kowa kudi a Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya mallaka.

Kudin dai, wadanda ya samu ranar Laraba, sun haura Dala biliyan 13.9 da Dangote ya mallaka, wanda shi ne na 65 a jerin attajiran duniya.

Tattalin arzikin Dangote ya ragu a ranar Talata, bayan ya tafka asarar Naira biliyan 105.33, lamarin da ya sa kudin nasa suka ragu da kashi -1.78.

A cewar jaridar Bloomberg, kaso 86 cikin 100 na kudin Dangote na cikin kamfanin simintinsa na Dangote Cement, wanda ya sami kudin shigar Naira tiriliyan 1.38 a shekarar 2021.

Sai dai duk da haka yana harkar sukari da gishiri da mai da takin zamani da kuma abinci.

Kazalika, Dangote na daya daga cikin masu hannun jari a bankin UBA.

Sarakunan Nijar sun kai wa Gwamnatin Yobe ziyarar jaje

Ɗan majalisa ya yi jinjina kan naɗa Danyaya Sarkin Ningi

’Yan Sanda sun kama gungun ’yan fashi 7 a Katsina

Zaɓen Edo: Ana ci gaba da ƙirga ƙuri’u