Attajirin Duniya yana son dambacewa da Shugaban Rasha kan mamayar Ukraine
Ya fito mu gwabza maimakon labewa a bayan dakarunsa.
Attajirin Duniya Elon Musk ya kalubalanci shugaban Rasha Vladimir Putin da ya fito su gwabza dambe tsakaninsu don duniya tasan karfin da ya ke tunkaho da shi maimakon labewa a bayan dakarunsa yana kisan kiyashi a Ukraine.
Cikin wani sako da Musk ya wallafa a shafinsa na Twitter ya ce yana kalubalantar Putin da ya fito tare da daura damararsa don dambacewa tsakaninsu, da nufin samar da mafita ga zaman lafiyar Ukraine.
Attajirin kuma ma’assasin kamfanin SpaceX ya wallafa cewa yana kalubalantar Putin don su yi fito-na-fito tsakaninsu don dambacewa sabanin amfani da karfin soji kan Ukraine.
A cewar Elon Musk, nasararsa kan Putin ce za ta fayyace makomar Ukraine daga karfa-karfar da ta ke gani a hannun Rasha kamar yadda Gidan Rediyon Faransa ya ruwaito.
Cikin rubutun na Musk da ya yi da harshen Rashanci ya tambayi ko shugaba Putin ya karbi tayin fadan?
Guda cikin mabiyan Musk a Twitter miliyan 77 ya mayarwa attajirin martini da ko ya na da masaniya kan rikicin da ya ke kokarin sayowa kansa, kuma nan take Musk ya mayar da martanin cewa da gaske ya ke.
A cewar Musk yanzu abu daya ya rage shi ne martanin Vladimir Putin kan bukatar don sanin waje da kuma lokacin dambacewar.