Attajirin Hadaddiyar Daular Larabawa ya sayi lambar mota ta Naira miliyan 310
Wani hamshakin attajirin Hadaddiyar Daular Larabawa Majid Mustafa, wanda ya mallaki lambobin mota na musamman har dubu biyar, ya sake sayen wata lambar ta musamman a kan kudi Dirham miliyan uku da dubu 100, wato daidai da Naira miliyan 310. Wannan lamba dai ya saye ta ne a wajen gwanjon da Hukumar kula da hanyoyi […]
Wani hamshakin attajirin Hadaddiyar Daular Larabawa Majid Mustafa, wanda ya mallaki lambobin mota na musamman har dubu biyar, ya sake sayen wata lambar ta musamman a kan kudi Dirham miliyan uku da dubu 100, wato daidai da Naira miliyan 310. Wannan lamba dai ya saye ta ne a wajen gwanjon da Hukumar kula da hanyoyi da hada-hadar sufuri ta Dubai (RTA) ke shiryawa a shekara-shekara.
Hukumar ta RTA a karshen wannan sheekarear, ta tara dirhami 12.75, inda aka yi gwanjon lambobi tara na musamman, wadanda suka hada da 12, 50 da 100, 333 da 786 da 1000 da 8888 da 11111, da 55555 wadda har yanzu ana hada-hadar gwanjonta a kasuwa.
A wata tattaunawa da Mustafa ya yi da jaridar Khaleej Times kadai, ya bayyana cewa, zai ajiye lambar AA10 don amfanin kashin kansa, inda zai daurata a jikin daya daga motocinsa na hawa.
Mustafa, wanda ya saba shiga hada-hadar gwanjon RTA tun daga shekarar 2002, ya ce ya mallaki lambobi na musamman da suka kai dubu biyar, wadanda da yawansu ya sake yin hada-hadar kasuwancinsu, inda ya samu riba gwaggwaba. Kuma mafi tsadarsu ita ce wadda yake da ita a halin yanzu da kimar kudinta ya kai miliyan shida.
Ta biyu a rukunin lambobin masu tsada, wadda aka yi hada-hadar gwanjonta ranar Asabar din makon jiya, wani ne Essa Al Habai ya sameta, wato AA12 a kan kudi Dirham miliyan biyu da dubu 210. Sai wani Balaraben Hadaddiyar Daular Larabawan da ya sayi ta uku a jerin lambobi masu tsadar, AA50 kan Dirhami miliyan guda da dubu 840, yayin da wani dan kasar Lebanon, Zaherchafie ya sayi wata lambar motar kan AA11111 for Dh1.21m.
Shi ma wani hamshakin dan kasuwar, Jaber Khamis, dan asalin Hadaddiyar Daular larabawan wanda ya yi hada-hadar cinikin lamba mafi tsada a rukuni na biyu, ya sayi tasa lambar AA3333 kan kudi Dirhami dubu 700. Kuma a bara ma ya taba sayen wata lambar kan kudi Dirhami dubu 500, wadda ya samu ribar Dirhami dubbu 200 a kanta bayan wasu watanni.
“Hhakika wannan lambar (AA333) ta musamman ce. Zan daurra ta ne kan mota kirar Lamborghini, amma ta yiwu ma in sayar da ita idan na smau mai saye kan farashi na hakika,” kamar yadda ya bayyana wa jaridar Khaleej Times.
A wajen gwanjon lambobin na musamman Hukumar RTA ta fito da sabon fasalin zayyanar lambobin mota a Dubai, wanda ke dauke da tambari da haruffa da dige-dige launin fari da baki.
Ahmed Bahrozyan Shugaban Hukumar bayar da lasisi ta RTA, cewa ya yi, RTA za ta fara maye gurbin lambobin da ake amfani da su a halin yanzu, da wadanda ke dauke da haruffa biyu-bbiyu tun da Fabrairun 2018, saboda an kai ga karshen lambobin mota masu lamba guda.
“Sai dai masu lambobin masu haruffa biyu za su samu damar amfani da sabon tsarin har tsawon shekara biyu. Mun bullo da sababbin lambobin na musamman guda 10, wadanda suka fara AA, kuma za mu tabbatar da crewa wadannan lambobin ba a sayar da su ba nan da shekara guda, saboda su kebanta kawai ga wadanda suka saye su,” inji shi.
Jerin lambobin 10 su ne:
AA10 kan kudi – Dh3,120,000
AA12 kan kudi – Dh2,720,000
AA50 kan kudi – Dh1,840,000
AA11111 kan kudi – Dh1,210,000
AA100 kan kudi – Dh910,000
AA333 kan kudi – Dh700,000
AA55555 kan kudi – Dh670,000
AA1000 kan kudi – Dh630,000
AA8888 kan kudi – Dh500,000
AA786 kan kudi – Dh450,000