AU ta ba Kwamitin PCNI tallafin Dala dubu 100, ta kuma yaba da ayyukan da take yi a Yankin Arewa Maso Gabas

kungiyar hada kan kasashen Afirka (AU) ta ba Kwamitin Sake Farfado da Yankin Arewa maso Gabas (PCNI) tallafin Dala dubu 100 a kokarin ganin an sake farfado da yankin. Tawagar kungiyar ce ta bayar da wannan tallafi a lokacin da ta kai wa Mukaddashin Sakataren Gwamnatin Tarayya Dokta Habiba Lawal ziyara a ofishinta da ke […]

AU ta ba Kwamitin PCNI tallafin Dala dubu 100, ta kuma yaba da ayyukan da take yi a Yankin Arewa Maso Gabas

kungiyar hada kan kasashen Afirka (AU) ta ba Kwamitin Sake Farfado da Yankin Arewa maso Gabas (PCNI) tallafin Dala dubu 100 a kokarin ganin an sake farfado da yankin.

Tawagar kungiyar ce ta bayar da wannan tallafi a lokacin da ta kai wa Mukaddashin Sakataren Gwamnatin Tarayya Dokta Habiba Lawal ziyara a ofishinta da ke Abuja a ranar Alhamis 12 ga  watan Oktoba, 2017. Tawagar dai tana karkashin jagorancin Ambasada Chirtau ne yayin da Ambasadan Malawi ya samu wakilci daga Ambasada Olabisi Dare, Shugaban Sashen Kula da ’Yan Gudun Hijira na kungiyar AU.

A jawabin maraba, Dokta Habiba ta yaba wa kungiyar hada kan kasashen Afirka (AU) a game da ziyarar da suka kawo Najeriya.  Ta ce ko shakka babu hakan zai ci gaba da karfafa zumuncin da ke tsakanin kasashen Afirka musamman damuwar da kungiyar ta yi a game da ganin an sake farfado da yankin Arewa maso Gabas.

A nasa jawabin, Shugaban tawagar Ambasada Chirtau, ya ce sun kawo ziyara Jihar Borno ne don su ganewa idanunsu abubuwan da suke faruwa.  Ya ce wannan shi ne karo na biyu da suke kawo irin wannan ziyara baya ga wacce suka taba kawowa a bara.  Ya yaba da kokarin kwamitin PCNI yake gudanarwa na sake farfado da yankin.  “Mun yaba da yadda muka ga kungiyoyin bayar da agaji da dama wadanda suka zo yankin Arewa maso Gabas don bayar da tasu gudunmawa a kan haka ne muka bayar da tallafin Dala dubu 100 don su ci gaba da gudanar da ayyukan raya yankin.”

A nasa jawabin, shugaban Kwamitin PCNI Mista Tijjani Tumsah ya yaba da tallafin da kungiyar AU ta ba kwamitinsa inda ya bukaci kungiyar da ta ci gaba da aiwatar da irin wannan aiki a sauran sassan da shafi ya shafa a daukacin Nahiyar Afirka ba ta takaita aikin a wane sashe na Afirka kadai ba.