AU ta zama mamba ta dindindin a kungiyar kasashen G-20

India ta nemi a bai wa Tarayyar Afirka gurbi na dindindin na zama mamba a kungiyar G-20.

AU ta zama mamba ta dindindin a kungiyar kasashen G-20

Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta zama sabuwar mamba a kungiyar kasashen G-20 masu karfin tattalin arziki ranar Asabar bayan Firaiministan India Narendra Modi ya gayyace ta.

Fadada kungiyar babbar nasara ce ta fannin diflomasiyya ga Modi, wanda zai sake fafatawa a zaben kasar a shekara mai zuwa kuma ya yi amfani da damar karbar bakuncin taron wajen kara wa kansa kima a idanun duniya.

Kafin ya bude taron, Modi ya gaishe da shugaban Tarayyar Afirka kuma shugaban kasar Comoros Azali Assoumani inda ya rungume shi.

“India ta nemi a bai wa Tarayyar Afirka gurbi na dindindin na zama mamba a kungiyar G-20.

“Na yi amannar cewa kowa ya amince da hakan,” a cewar Modi a jawabinsa ga mahalarta taron.

“Ina kira ga shugaban Tarayyar Afirka ya zo ya zauna a kujerarsa ta dindindin a G-20 bayan amincewar kowa da kowa,” in ji shi, inda ya doka sandar da ke hannunsa wacce ke nuna an yarda da matakin.

Daga nan ne Assoumani ya je ya zauna a wurin da shugabannin kungiyar suka zauna bayan Ministan Harkokin Wajen, India S. Jaishankar ya yi masa iso.