‘Audu mai rashin ji’

Barkanmu da warhaka Manyan Gobe. Da fatan kuna lafiya. A yau na kawo muku labarin  ‘Audu mai taurin rashin ji’. Labarin na kunshe da yadda Manyan Gobe ya kamata su zama masu natsuwa, da bin iyaye daidai gwargwado, an ce ‘duk wanda bai ji bari ba, zai ji hoho’. A sha karatu lafiya Taku, Amina […]

‘Audu mai rashin ji’

Barkanmu da warhaka Manyan Gobe. Da fatan kuna lafiya. A yau na kawo muku labarin  ‘Audu mai taurin rashin ji’. Labarin na kunshe da yadda Manyan Gobe ya kamata su zama masu natsuwa, da bin iyaye daidai gwargwado, an ce ‘duk wanda bai ji bari ba, zai ji hoho’. A sha karatu lafiya

Taku, Amina Abdullahi


Akwai wani yaro mai suna Audu yana son cin kwallon yazawa (kashu) sosai. Kullum sai ya damu mahaifiyarsa da ta ba shi kwallon yazawa. Idan ta ba shi sai ya ce ta  kara masa. Abin ya damu mahaifiyarsa yadda yake yawan cin kwallon yazawar ya wuce misali.

Ran nan sai ta ce da shi “ Audu, ya kamata ka rage cin kwallon yazawa don zai iya yi maka illa idan ya yi yawa.”  Sai ta boye sauran ta tafi kasuwa don yin cefane. 

Da Audu ya ga mahaifiyarsa ba ta nan, sai ya je ya sayo wata yazawar ya ci gaba da sha. 

Washegari, sai Audu ya kamu da ciwon ciki. Da suka je asibiti da mahaifiyarsa, sai likita ya ce Audu ya kamu da ciwon ciki ne sakamakon kwallon yazawa  da ya yi masa yawa a ciki.  Hakan ta sa Likita ya yi wa Audu allurai na tsawon kwanaki da hakan ta sa ya samu sauki.

Tun daga wannan lokaci ne Audu ya daina shan kwallon yazawa.  

Da  fatan Manyan Gobe sun dauki darasi daga wannan labari.