Audu mai satar naman Sallah

Barkanmu da warhaka Manyan gobe tare da fatan ana lafiya. Ya ya shirin Sallah? Allah Ya sa a yi a cikin sa’a amin. A yau na kawo muku labarin ‘Audu mai satar naman Sallah’. Labarin ya kunshi irin halin da mutum ke shiga bayan ya ci abin sata. A sha karatu lafiya: Taku: Amina Abdullahi […]

Audu mai satar naman Sallah
Audu mai satar naman Sallah

Barkanmu da warhaka Manyan gobe tare da fatan ana lafiya. Ya ya shirin Sallah? Allah Ya sa a yi a cikin sa’a amin. A yau na kawo muku labarin ‘Audu mai satar naman Sallah’. Labarin ya kunshi irin halin da mutum ke shiga bayan ya ci abin sata. A sha karatu lafiya:

Taku: Amina Abdullahi

Audu yaro ne mai mugun kwadayi da rashin ji. Iyayensa kuma suna iya kokarinsu domin ganin sun raba shi da irin wannan halin amma  ya ki.
Ranar Sallar Layya bayan sun dawo daga masallaci tare da mahaifinsa, sai mahaifin ya yanka  rago. Aka aika wa makwabta da abokan arziki naman layyar don su ma su sanya albarka.
Mahaifiyar Audu ta yi masa gargadin ya rage cin nama don gudun kada ya tsure amma ya ki ji. Da ma akwai alkawarin da mahaifin ya yi musu na zuwa hutu Jihar Legas. Koda aka bai wa Audu nasa kason naman, sai ya cinye. Bayan kowa ya yi barci cikin dare sai ya lallaba ya bude kwanon da mahaifiyarsa ta ajiye nama ya yi ta ci har sai da ya yi nak!
A daren kuwa Audu bai yi barci ba. Babu abin da yake sai zawo.
Gari na wayewa sai mahaifiyarsa ta ce a kai shi asibiti domin jikinsa ya yi zafi. Suna isa asibiti sai aka kwantar da shi na mako daya.
Kafin makon dayan ne sai sauran ’yan uwansa suka fara shirin tafiya Legas hutu.   Ga Audu yana son zuwa amma yana gadon asibiti. Haka ’yan uwansa suka tafi suka bar shi a kwance a asibiti.
Don haka Manyan gobe a yi hattara kuma kada a zama kamar Audu.