Aure da zaman iyalin Kirista (11)

Yayin da muke ci gaba da koyarwarmu a kan aure da zaman iyalin Kirista, ina so in nanata cewa, dalilin da ya sa iyalai da dama suke fuskantar kalubale a yau; ba domin komai ba ne, sai rashin bin ka’idar da Allah Ya shirya domin samun nasarar zaman aure. Muddin mutum bai yi la’akari da […]

Aure da zaman iyalin Kirista (11)
Aure da zaman iyalin Kirista (11)

Yayin da muke ci gaba da koyarwarmu a kan aure da zaman iyalin Kirista, ina so in nanata cewa, dalilin da ya sa iyalai da dama suke fuskantar kalubale a yau; ba domin komai ba ne, sai rashin bin ka’idar da Allah Ya shirya domin samun nasarar zaman aure. Muddin mutum bai yi la’akari da maganar Allah ba, babu yadda za a samu zaman lafiya cikin zaman gidansa. Mun dasa aya ne a kan binciken nauyin da ke kan maigid; abu na biye wanda ya kamata mu gani shi ne:
Kowane miji yakan ciyar da iyalinsa:
Maganar na Allah na koya mana cewa: “Gama babu mutum wanda ya taba kin jiki nasa; amma yakan ciyar da da shi yakan kiyaye shi, kamar yadda Kiristi kuma yakan yi da eklesiyya; domin mu gababuwa ne na jikinsa.”(Afisawa:5: 29–30). Akwai fannoni guda biyu da za mu duba da za su taimaki ganewar mu sosai, su ne, ciyarwa cikin ruhu da kuma ciyarwa cikin jiki.
Yaya miji zai ciyar da matarsa cikin ruhu? Ta wurin yin addu’a domin matarsa a koyaushe da kuma binciken Littafi Mai tsarki tare; haka nan matar za ta ginu cikin ban-gaskiya ta kuma yi kwazo cikin bin umarnin Allah. Mazaje da dama sun yi sakaci da wannan sashin rayuwa, ba su lura da bukatun matansu ba a wannan fanni; yawancin lokaci ba su da lokacin da za su zauna da matansu balle su koya musu maganar Allah. Abu na biye shi ne – kowane miji ya kamata ya goyi bayan matarsa; ya kuma ba ta damar bunkasa. Kada miji ya yi kuskuren kuntata wa matarsa; ba daidai ba ne miji ya zama dalilin rashin ci gaban matarsa, ka bar Allah kadai Ya sha kanta: kowane namiji ya kamata ya iya yin komai da zai karfafa matarsa; haka kuma, idan Ubangiji Allah Ya ba da damar sayen Littafi Mai tsarki da sauran takardun da za su taimaki matarka ta ginu cikin ruhaniya. Ba ciyar da ita cikin ruhaniya kadai ba ne; amma ciyar da ita cikin jiki da kuma sosuwar ranta. Miji zai iya yin wannan ta wurin lura da bukatun matarsa na jiki kamar isasshen abinci da sutura da lafiyar jikinta da sauran bukatun da ke cikin gida. Dole ka zama da imani ka yi tunani game da abin da take bukata ka kuma roki Allah Ya taimake ka domin ka iya aiwatar da su gwargwadon karfinka. Idan har ba za ka iya yin wadansu abubuwa domin ba ka da shi ne; za ka iya kiranta ku yi addu’a tare, kuna ba da gaskiya tare domin Ubangiji Allah Ya ji Ya kuma biya muku bukata. Ka tuna fa, maganar Allah na koya mana cewa: “Amma idan wani ba ya yi tattalin nasa ba, balle na iyalinsa, ya musanci imani, gwamma mara ban-gaskiya da shi.”(1Timothawus:5:8).
Kada ka hana ta jima’i ko kadan, idan har kana da aure, ba lokaci ba ne na cin abinci barkatai a waje ba tare da sanin matarka ba. Yawancin lokaci; mazaje masu cin abinci a waje, sukan ci abin da zai gina jikinsu sosai, amma idan ka je gidajensu; za ka iske matan da yara ramammu, domin ba abincin da zai gina jikinsu ne suke ci ba. Ya bar su da tuwon masara da miyan kuka wadda ko kifin nan da ake kira ‘hana kiss’ babu a ciki, amma shi yakan iya zama ya cinye balangu ko tsire na Naira 600 zuwa dubu; ya kuma samo Maltina mai sanyi ya dora a kai, idan ya isa gida; ba zai ma kula da abincin da aka kawo masa ba.
Sai ka tuna cewa rana na zuwa wadda dukanmu za mu bayyana a gaban dakalin Shari’ar Allah mu ba da lissafin abin da muka yi a wannan duniya har da rayuwar iyalinmu. Mace wadda ba ta samu biyan bukata na ruhaniya ko na jiki ba; za ta shiga yin wadansu ayyukan da ba su dace ba; maganar Allah na cewa: “Duk da wannan sukan koyi su zama raggaye, suna yawo suna bin gidaje; ba kuwa raggaye kadai ba, amma masu tsegumi kuma, masu shishigi, suna fadin abin da bai kamata a gare su ba.”(1Tim.5:13).
Duk lokacin da mace ba ta samu biyan bukata a gida ba; musamman cikin ginuwa a ruhu da kuma jiki, za ta soma zama mai fitina, kuma mai masifa ko jidali, yawancin lokaci takan zama mai shishigi, sai yawo da tsegumi. Idan ba ta da sutura takan ji kunyar shiga tsakanin sauran mata; ba za ta iya ji da kanta ba ko kadan. Wannan kadai zai iya kawo mata rashin lafiya. Shi ya sa kowane magidanci ya kamata ya lura da dukan muhimman bukatun matarsa. Kada maza su manta cewa idan ba su zauna da matansu bisa ga sani ba, babu shakka nasu rayuwar za ta samu damuwa kwarai “Haka nan kuma ku maza, ku zauna da matanku bisa ga sani, kuna ba da girma ga mace, kamar ga wadda ta fi rashin karfi da kuma masu tarayyar gado na alherin rai: domin kada addu’o’inku su hanu.”(1Bitrus:3:7).

Kowane miji uba ne ga dukan iyalinsa:

Wannan nauyi ne mai muhimmanci sosai, zama matsayin uba ba abu ne mai sauki ba ko kadan. Idan mun duba zamaninmu na yanzu; za mu ga cewa yara da yawa sun bijire, sun zama masu taurin kai; marasa dabi’a, dalilin ba zai zama da nisa ba, rashin horarwa ne cikin gida musamman ma daga wurin uba. Yawancin iyaye ba su da lokacin lura da irin halayen da ’ya’yansu suke ciki; an bar su kawai kamar tumakin da ba mai kiwonsu; duk abin da suke so su yi shi za su yi, ba mai ce musu kala. Maganar Allah na koya mana cewa: “dana, ka ji koyarwar ubanka. Dokar uwarka kuma kada ka yar da ita.”(Misalai 1: 8). “Mai rai, mai rai, shi ne zai yi yabonka, kamar yadda nake yau. Uban zai sanar wa ’ya’yansa da gaskiyata.” (Ishaya:38:19). “Wauta tana nan kunshe a zuciyar yaro. Amma sandar horo za ta kore masa ita nesa.”(Misalai: 22:15).
Girmar da yaro bisa tafarkin Allah aiki ne sosai; idan uba yana so ya yi aiki mai cikakke a kan ’ya’yansa; dole ne ya san maganar Allah sosai yadda ya kamata. Kowane magidanci;  priest ne bisa iyalinsa. Duk iyali za su saurare ka, shi ya sa dole ne ka san maganar Allah ka iya horar da ’ya’yanka.
Zaman aure a cikin iyalin Kirista, abu ne mai dadi sosai idan mun bi nufin Allah; addu’ata, ita ce, iyalan da suke fuskantar kalubale a yanzu, su iya komawa ga Allah ta wurin addu’o’i da binciken Littafi Mai tsarki. Allah Yana da shiri mai kyau domin iyalan da suka san Yesu Kiristi. Yaya naka iyalin suke?
Kada mu gaji da yin addu’a domin kasarmu. Ubangiji Allah Ya ci gaba da tsare mu duka, amin.