Aure da zaman iyalin Kirista (4)
Ubangiji Allah kuma ya che, ba ya yi kyau ba mutum shi kasanche shi daya; sai in yi masa mataimaki mai dachewa da shi. Daga chikin kasa kuma Ubangiji Allah ya sifanta kowane dabba na jeji, da kowane tsuntsu na sama; ya kawo su wurin mutumen ya ga abin da za ya che da su: […]
Ubangiji Allah kuma ya che, ba ya yi kyau ba mutum shi kasanche shi daya; sai in yi masa mataimaki mai dachewa da shi. Daga chikin kasa kuma Ubangiji Allah ya sifanta kowane dabba na jeji, da kowane tsuntsu na sama; ya kawo su wurin mutumen ya ga abin da za ya che da su: iyakar abin da mutumen ya kira rayayyen halitta, shi ne ya zama sunansa. Mutumen kwa ya bada sunaye ga dukan bisashe, da tsuntsayen sama, da kowane dabba na jeji; amma ba a samo ma mutum mataimaki mai dachewa da shi ba.” Hakanan a chikin Farawa 1 : 27 – 28, maganar Allah na koya mana chewa “Allah ya halitta mutum chikin suratasa, a chikin surar Allah ya haliche ; na miji da ta mata ya haliche su, Allah ya albarkache su kuma: Allah ya che masu, Ku yalwata da yaya, ku ribu, ku mamaye duniya, ku mallake ta; ku yi mulkin kifaye na teku, da tsuntsaye na sarari da kowane abu mai rai wanda ke rarrafe a kasa.”
I. Lokachin da Allah halichi mutum, ya yi domin ya chika dalilin da ke chikin zuchiyarsa. Mutum bisa ga shirin Allah, ya kamata ya yi mulki a bisa dukan abin da Allah ya halitta; Allah ya sanya shi a chikin gonar Adnin domin ya aikache ta, shi kuma tsare ta. Wannan ba karamin aiki ba ne ko kadan. Yayin da Adamu yana fama da aikin da Ubangiji ya damka a hannunsa, Allah da kansa ya lura da chewa bai kyautu ba mutum shi kasanche shi daya chikin aikin da an ba shi, ba wai kadaitaka bane, in da kadaitaka ne, da maiyuwa Allah ya yi wani mutum kamar Adamu, amma sai ya che, bari in yi ma shi Mai taimako, ashe idan mun duba a hankali, zanchen na bukatan taimako ne a chikin aikin da Allah ya sa a hannun mutum. Sabili da wannan, aure shirin Allah ne domin ya taimaki mutum chika nufin Allah game da rayuwarsa. A matsayin mu na masu bada gaskiya ga Yesu Almasihu, Allah ya ba ma kowane dayanmu aikin yi ta wurin Ruhu Mai Tsarki, a Litafin Afisawa 2 : 10, maganar Allah na koya mana chewa “Gama mu kirassa ne, halittattu chikin Kristi Yesu zuwa kyawawan ayuka, wadanda Allah ya rigaya ya shirya da za mu yi tafiya a chikinsu”. Idan har muna so mu chika nufin Ubangiji Allah a zaman mu na masu Bi; dole ne mu sani chewa Aure, hanya ne na chika wannan. Duk mai bi wanda bai san wannan asiri ba, to lallai zai sami damuwa chikin aurensa, domin bai yarda da taimakon da Allah ya kawo ma shi ba, wannan taimako kwa Matarka che. Akwai mazaje dayawa wanda suna ganin matayen su kamar tarin wahala ne a gidansu, wani lokachi ma suna ganin matayen su kamar su ne damuwarsu, alhali kwa, idan aka duba a hankali, za a ga chewa mazaje dayawa sun ki kula da taimakon da Allah ya sa domin su a chikin wannan matar nasu.
Akwai wadanda suka yi tambayoyi da dan dama, ina so in roke ku ku yi hakori, sai bayan na kammala wannan koyaswa idan Allah Madaukakin Sarki ya bar a chikin masu rai. Nagode, kada mu manta mu chi gaba da yin addu’a domin wannan kasa namu. Dabarar mutum kam ta kare, sai dai Allah chikin alherinsa kadai ke da asirin kawo ga karshe irin wahalan da a ke fuskanta a yau.