Aure da zaman iyalin Kirista (5)

Dalilin ko niyyar aure:-   Muna ci gaba da wannan koyarwa domin idan ba mu gane manufar Allah game da aure ba, ba za mu iya morar aure cikakke ba.II.    Domin samun abokin tarayya. Maganar Ubangiji Allah na koya mana a cikin Littafin Mai Wa’azi: 4 :9 – 12  cewa, “Gwamma biyu da daya; domin […]

Aure da zaman iyalin Kirista (5)
Aure da zaman iyalin Kirista (5)

Dalilin ko niyyar aure:-  

Muna ci gaba da wannan koyarwa domin idan ba mu gane manufar Allah game da aure ba, ba za mu iya morar aure cikakke ba.
II.    Domin samun abokin tarayya.
Maganar Ubangiji Allah na koya mana a cikin Littafin Mai Wa’azi: 4 :9 – 12  cewa, “Gwamma biyu da daya; domin suna da arziki cikin aikinsu. Gama idan sun fadi, daya za ya daga dan uwansa: amma kaiton wanda shi ke shi kadai sa’adda ya fadi, ba shi da wanda za ya tashe shi. Kuma idan biyu sun kwanta wuri daya, za su ji dumi; amma kaka mutum shi daya za ya ji dumi? Kuma idan mutum ya rinjaye wanda shi ke shi kadai, biyu za su iya tsaya masa; igiya ribi uku kuma ba ta tsunkuwa da sauri.”  Allah Ya shirya cewa aure zai zama sanadin tarayya tsakanin mutum da matarsa. Kamar yadda Littafi Mai tsarki ke koya mana, babu wanda yaKe yin shiri domin ya fadi, amma idan har daya ya fadi ko duka su biyu suka fadi, daya zai taimaki dayan ya tashi, amma kaiton wanda yana nan shi kadai, ba ya da mai taimako kusa. Ka tuna fa; matarka jikinka ne kuma abokiyar zamanka ce ita: Maganar Allah na cewa “….Amma kun ce, Don me? Domin Ubangiji Ya zama shaida tsakaninka da matarka ta kuruciya, wadda ka ci amanarta, koda ta ke abokiyar zamanka, matar alkawarinka.” (Malaci 2:14). Ina so mu tuna a kullum cewa Allah shi ne shaida tsakanin ka da matarka na aure; idan har ka ci amanarta, ka sani Allah Yana gani. Mazaje da dama ba su gane wannan asirin ba cewa duk lokacin da ka ci amanar matarka, Allah ba zai kula da addu’arka ba. “Haka nan kuma ku mazaje, ku zauna da matanku bisa ga sani, kuna ba da girma ga mace, kamar ga wadda ta fi rashin karfi da kuma masu tarayyar gado na alherin rai: domin kada addu’o’inku…” (1Bitrus 3 : 7). Akwai masu bi da yawa da halin al’adunsu na gargajiya ne suka sa a gaba fiye da koyarwar Littafi Mai tsarki; masu bi da dama ba su sani cewa yadda suke rayuwa da matansu na da muhimmanci sosai musamman ma idan suka zo ga yin addu’a. Addu’a tana da muhimmanci a cikin rayuwar kowane mai bi, shi ya sa ya zama dole mu lura da duk abin da zai sa Ubangiji Allah Ya ki jin addu’armu; daya daga cikin dalilan da za su sa Allah ba zai kula da addu’arka ba, shi ne rashin ba da girma ga matarka kamar ga wadda ta fi rashin karfi. Mai yiwuwa kana ta addu’a na tsawon lokaci amma ba ka samu amsa daga wurin Allah ba har yanzu, watakila ma ka yi tunani ko mai yiwuwa ka yi zunubi shi ya sa Allah bai ji ka ba; sai ka kawo kanka gaban Allah domin ka roke shi gafara, watakila ma ka hada har da azumi, amma duk da haka ba ka samu biyan bukata ba. Akwai wuri guda da ya kamata ka sake dubawa, wato yadda kake zama da matarka, idan har ba bisa ga shirin Allah ba ne, ko kuwa kana musguna wa matarka, ya isa Allah Ya ki jin rokonka cikin addu’a. Kuma ka sani cewa duk abin da zai shafi rayuwarka na addu’a; hadari ne sosai.
III.    Allah Ya shirya aure domin samun zuriya mai Ibada:
A cikin kowane aure Ubangiji Allah Yana so Ya samu iri mai kyau, zuriya mai ibada; tunanin Allah a kullum shine, a cikin kowane auren masu bi, yana so Ya ga yaya masu jin tsoronSa; masu ibada kuma. A cikin Littafin Malaci: 2:15, maganar Allah na cewa, “A cikin wadanda suka yi wannan ba wanda yake da sauran ruhu. Yaya ke nan? Akwai ko daya wanda yake neman zuriya mai ibada? Domin wannan ku yi lura da ruhunku, kada kowa ya ci amanar matar kuruciyarsa.”  Abu guda a cikin aure da zai faranta wa Ubangiji Allah zuciya shi ne Ya ga cewa ’ya’yan da ya ba mu sun girma cikin bauta maSa, ’ya’ya masu ibada. Dukan iyayen da suka yi lura da wannan nufin Allah na tada zuriya masu tsoronSa, za su cika daya daga cikin dalilin yin aure. Idan kana da aure kuma Allah cikin alherinSa Ya ba ku albarkan ’ya’ya. Tambayar ita ce, wani irin ’ya’ya ne su? Wani irin zuriya za ka bari a baya? Idan kuwa ba ka da aure, shin, mene ne tunaninka ko tunaninki game da wannan shiri na Allah?
Ib.    Allah Ya shirya aure domin gamsuwa da jin dadin jima’i: