Aure da zaman iyalin Kirista (6)

Nauyin da ke kan mace a cikin zaman iyalin Kirista: Wani lokaci akan samu sabani a cikin zaman gida, ba domin komai ba, sai saboda rashin fahimtar juna. Sau da dama mukan manta da dalilin da ya sa Allah Ya kafa aure, idan muka soma dubawa daga farkon farawa; inda Allah da kanSa Ya ga […]

Aure da zaman iyalin Kirista (6)
Aure da zaman iyalin Kirista (6)

Nauyin da ke kan mace a cikin zaman iyalin Kirista:
Wani lokaci akan samu sabani a cikin zaman gida, ba domin komai ba, sai saboda rashin fahimtar juna. Sau da dama mukan manta da dalilin da ya sa Allah Ya kafa aure, idan muka soma dubawa daga farkon farawa; inda Allah da kanSa Ya ga budatar cewa bai yi kyau ba mutum ya kasance shi daya. Allah Ya duba cikin dukan halitta, amma bai samo wa mutum mataimaki mai dacewa da shi ba, haka nan ne Allah Ya shirya Ya yi wa mutum mataimaki mai dacewa da shi, wato mace. Kodayake za mu dubi nauyin da ke kan maigida da uwargida a sashi daban-daban, amma ba wai muna so mu sa iyaka tsakanin aikin maigida da na uwargida ba ne ko kadan, domin cikin ruhun soyayya; dukansu biyu za su iya taimakon juna a cikin daukar nauyin gida.  
“Wanda ya samu mata ta kirki ya samu, Yana kuwa samun alheri wurin Ubangiji.” (Misalai: 18:22). “Gida da dukiya gado ne daga wurin ubanni: Amma mace mai hankali daga wurin Ubangiji ne.” (Misalai:19:14).
Ina so mu soma duban wannan koyarwa kamar haka; a yau, idan ka tambayi maza da yawa game da matansu, yawancinsu sun rigaya sun gaji da zaman auren, suna ganin matansu kamar matsifa ce a gidan, kullum suna cikin damuwa, har ya kai ga mutum yana tsammani cewa matarsa ce ke kawo masa irin wahalhalun da suke kansa a yau. Amma ina so mu sake duba abin da maganar Allah ke cewa: “wanda ya samu mata, ta kirki ya samu ‘alheri wurin Allah’. Abin lura shi ne wannan matar taka, ALHERI ne zuwa gare ka daga wurin Allah da kanSa. Allah bai shiryata ta zama maka bala’i ba, abin kirkin da ka samu ke nan daga wurin Allah, ka tuna cewa Allah ne Ya ce, “…ba ya yi kyau ba mutum ya kasance shi daya ba…” duk abin da Allah Ya ce ba ya da kyau, to gaskiya ba ya da kyau. Ashe duk wanda ya isa yin aure kuma bai yi ba, a gaban Allah zama haka ba ya da kyau. Dole ne tunaninka game da matarka ya zama mai kyau. Idan har mun gane cewa matarka – Alheri ne daga wurin Allah, za ka iya daunarta ba da guna-guni ba. Mace mai hankali ba gadon ta ake yi ba; amma daga wurin Ubangiji Allah take. Samun alherin nan daga wurin Allah ne ba daga wurin mutum ba. Ina son mu sani cewa babu yadda mace za ta iya zama ta kirki da kuma hankali, rayuwarta kuma ta zama abin alheri ga mijinta, sai dai tare da addu’a. Abin da ya sa ake samun dalubale cikin aure a yau – rashin yin addu’a ne. Shaidan ba ya so ya ga mutum yana biyayya ga umarnin Allah, kuma wuri daya da ya fuskanta a yau shi ne Iyalin Masu bi; babu shakka idan ba a tsaya da addu’a ba, lallai Shaidan zai yi nasara cikin lalatar da iyalai da dama.
Mai Taimako: “Ubangiji Allah kuma Ya ce ba ya yi kyau ba mutum ya kasance shi daya, sai in yi masa mataimaki mai dacewa da shi.” ( Far. 2:18). “Gwamma biyu da daya domin suna da arziki cikin aikinsu. Gama idan sun fadi, daya zai daga dan uwansa: amma kaiton wanda yake shi kadai sa’adda ya fadi, ba ya da wanda zai tashe shi. Kuma idan biyu sun kwanta wuri daya za su ji dumi; amma dada mutum shi ddaya za ya ji dumi? Kuma idan mutum ya rinjaye wanda yake kadai, biyu za su iya tsaya masa; igiya ribbi uku kuma ba ta tsunkuwa da sauri.” (Mai Wa’azi: 4:9 –12).
Wane ne mai taimako? Wanda yake da amfani ga wani: idan kana da aikin yi, za ka ga amfanin wanda zai zo ya sa maka hannu, aikin yakan zama da saudi sosai, wanda zai iya taimakonka yin aiki ba rago ba ne ko kadan. Dole wanda zai yi wannan taimako ya zama mai darfi kusan kamar naka; haka nan Allah cikin alherinSa Ya kawo wa mutum matarsa ya ce: “Sai in yi masa mataimaki mai dacewa da shi.”  Ashe ainihin aikin mace na farko cikin gida shi ne ta zama mai taimakon mijinta cikin dukan abin da yake yi. Mace, Allah bai yi ki domin ki zama damuwa ga maigida ba, a’a; amma domin ki taimake shi ya iya zama abin da Allah Ya shirya shi ya yi. daya daga cikin dalilan da Allah Ya yi ki ke nan. Tambayar ita ce: Kina taimakon maigidanki bisa ga maganar Allah domin ya zama mutum cikakke, ko kuwa kina dodarin gurguntar da shi ta wurin halayenki marasa kyau? A yau, babu yadda mace wadda ba ta da ceto a cikin Yesu Kiristi da za ta iya taimakon mijinta yadda ya kamata, wannan kuwa domin zunubin da ya shigo duniya ne. Shi Shaidan ya so ya lalata harkar aure tun daga farko, shi ya sa ya zo ya rudi macen ta aikata abin da Allah Ya hana su yi. Tun daga lokacin ne aure ya soma lalacewa; amma godiya wa Allah Wanda Ya aiko da Yesu Kiristi domin ya cece mu daga la’ana wadda muka shiga ta wurin rashin biyayya: “Kiristi ya fanshe mu daga la’anar shari’a, da ya zama la’ana maimakonmu: gama an rubuta, Kowane wanda aka rataye shi ga itace la’ananne ne: domin albarkar Ibrahim ta sauko wa al’umma cikin Kiristi Yesu; domin mu karbi aldawarin Ruhu ta wurin ban-gaskiya.” (Gal. 3 :13–14).   Ta wurin rashin yin biyayya ga maganar Allah a cikin gonar Adnin, mutum ya jawo wa kansa la’ana; hakan ya sa kansa cikin dunci da wahala. Amma abin murna a yau shi ne, Kiristi ya fanshe mu daga wannan la’anar da muka shiga. Yau kowane mai bin Yesu yana da cikakken izini ya yi rayuwar da zai kawo daukaka ga sunan Allah. Ki sani cewa ke ce mataimakiya mai dacewa ga maigidanki; cikin rayuwarku ta yau da kullum, cikin aikin hidimar da Allah Ya damda wa maigidanki, cikin tafiyar da ayyukan cikin gida, cikin addu’a da sauransu.
A cikin Littafin Afisawa:2:10, maganar Allah tana cewa: “Gama mu kirassa ne, halittattu cikin Kiristi Yesu zuwa kyawawan ayyuka, wadanda Allah Ya rigaya ya shirya da za mu yi tafiya a cikinsu.” To sai mu sani cewa kowane mutum yana da irin aikin da zai yi a cikin rayuwarsa, idan mun gane namu aikin, sai mu ci gaba a ciki. A cikin shirin Allah, bayan Ya ba ka aikin yi sai ya ba ka mace domin ta zama mai taimakon ka.
Ina so mu yi binciken wadannan wurare a gida domin kamu: 1Samaila: 25:4–37 da Misalai:31:10 –28 da Ayyukan Manzani: 18: 24–26.
Za mu ci gaba mako mai zuwa idan Allah Ya bar mu cikin masu rai. Mu ci gaba da gode wa Allah domin irin taimakon da Yake kawo mana a cikin dasarmu; musamman ma game da zaman lafiya cikin al’umma. Allah Ya ci gaba da tsare mu, amin.