Aure da zaman iyalin Kirista (7)
Nauyi/aikin mace cikin zaman iyalin Kirista: Za mu ci gaba da wannan koyarwar kuma ina so mu tuna cewa muna duba aikin da ya rataya a kan mace cikin zaman iyali. Idan har za mu ci nasara cikin zamanmu a matsayin masu bin Yesu Kiristi, dole ne mu dauki wadannan matakai da muhimmanci sosai, idan har […]
Nauyi/aikin mace cikin zaman iyalin Kirista:
Za mu ci gaba da wannan koyarwar kuma ina so mu tuna cewa muna duba aikin da ya rataya a kan mace cikin zaman iyali. Idan har za mu ci nasara cikin zamanmu a matsayin masu bin Yesu Kiristi, dole ne mu dauki wadannan matakai da muhimmanci sosai, idan har mun ki bin su kamar yadda suke cikin Littafin Rai, to babu shakka muna shirin shiga cikin mawuyacin hali ne kwarai.
Zaman biyayya ga mijinta:
Ina so mu yi karatu daga cikin Littafi Mai tsarki domin mu samu cikakkiyar ganewa game da wannan. Mata da dama suna fitowa da nasu ra’ayi da ya bambanta da maganar Allah. A cikin Afisawa, Sura 5 Aya 22, Maganar Allah Ta ce “Mataye, ku yi zaman biyayya ga mazanku; kamar ga Allah.” Haka nan a cikin Littafin 1Bitrus 3:1–6; Maganar Allah na cewa “Haka nan, ku mata kuma, ku yi zaman biyayya ga mazajenku; domin koda akwai wadansu da ba su yin biyayya da magana, su rinjaye ban da magana saboda halayen matansu; suna lura da halayenku masu tsabta tare da tsoro. Kada adonku ya zama ado na waje, wato su kitson gashi da su ado na zinariya, ko yafa tufafi masu kawa; Amma ya zama boyayyen mutum na zuciya, cikin tufafi wadanda ba su lalacewa na ruhu mai ladabi mai lafiya, abin da ke da tamani mai girma a gaban Allah. Gama haka nan ne tsarkakan mata kuma na da, wadanda suna kafa bege ga Allah suka yi wa kansu ado, suna zaman biyayya ga mazajensu: kamar yadda Saratu ta bi maganar Ibrahim, tana ce da shi Ubangiji: ku ne kuwa ’ya’yanta yanzu, idan kuna aika nagarta, ba ku cikin tsoro ga kowane abin firgitawa kuma.”
Idan mun lura sosai a inda muka yi karatu, Allah ta wurin ikon Ruhu Mai tsarki Yana koya wa matan Kirista wadanda suna da aure cewa “ku mat, ku yi zaman biyayya ga mazajenku, abin da ya kamata ke nan cikin Ubangiji.” Babu yadda zaman iyali zai cika nufin Allah ba tare da kiyaye wannan umarni ba. Muna cikin wani zamani ne wanda mata suna neman “’yancin kansu,” duk taron mata a fuskar duniya a yau ya kunshi tattaunawa game da samun zarafi domin su yi abin da suka ga damar yi kamar maza, gaskiyar ita ce, abu na farko ga kowace mace da take da aure, shi ne yin biyayya ga mijinta. Yin biyayya ko kuwa nuna ladabi ya kunshi kaskantar da kai, mu iya barin nufinmu ko ra’ayinmu; mu dauki ra’ayin wani ya zama namu, kuma mu yi shi da yardarmu ba tilas ba; wannan shi ne Allah Yake bida ga kowace mace a wurin mijinta. Yawancin mata suna ganin kamar bauta ne, kamar ba su da ’yanci kuma, gaskiyar ita ce ba za ki iya cika nufin Allah cikin aurenki ba in babu wannan. Shi Allah Wanda Ya halicce ki Ya san abin da zai yi miki kyau. Ado na waje wanda ya kunshi sa tufafi masu kawa, kitson gashi da kowane irin kwalliya na da kyau, amma kwalliya mai kyau ita ce a iske mace cike da Ruhu mai tsarki, kuma tana sanye da “…tufafi wadanda ba su lalacewa na ruhu mai ladabi mai lafiya, abin da ke da tamani mai girma a gaban Allah.” Babu wata kwalliya da ta fi wannan a gaban Allah. Koda mijinki bai karbi Yesu Kiristi a matsayin mai cetonsa ba, koda mijin naki yana ‘wulakanta ki’ shi ne mijinki, bisa ga maganar Allah maimakon ki yi damara domin fada, ki yi masa ladabi da biyayya, wannan asiri mata kadan ne suka sani; kuma gaskiya wannan irin halin ne zai kawo nasara har ki iya rinjayar maigidanki. Mai yiwuwa kina fuskantar wahala da mijinki, watakila ma kina tunanin rabuwa da shi, ko za ki sake tunani ki yi biyayya ga maganar Allah – ki nuna masa halin Kiristi, tare da yi masa addu’a; za ki ga irin canjin da Allah zai yi a cikin rayuwarsa. Za ki ga wani lokaci kamar cutarki ake so a yi, amma ba haka ba ne: hanya ce ta kawo nasara cikin zaman iyali.
Tambaya daya mai muhimmanci ita ce: shin har zuwa wane lokaci ne mace za ta ci gaba da yin ladabi da biyayya ga mijinta? A cikin Littafin Afisawa 5: 22, 24 Kalmar Allah na cewa “Mata, ku yi zaman biyayya ga mazanku, kamar ga Ubangiji; Amma kamar yadda Ekilisiyya take zaman biyayya ga Kiristi, haka nan mata su yi ga mazansu cikin dukkan abu.” Idan har muna so mu bi maganar Allah; to, babu lokacin da mace za ta ce ta daina yin biyayya ga mijinta. Misalin da aka ba mu shi ne na Ekilisiyya da Kiristi: duk wanda ya ce shi mai bin Yesu Kiristi ne, babu lokacin da za mu iya cewa mun fasa yi wa Yesu Kiristi biyayya; komai tsananin da muka shiga yayin da muke bauta masa, haka nan Ubangiji Allah ke bukata ga kowace mace, ladabi da biyayya ga mijinta; Wannan ba tare da guna-guni ba domin ki yi ne ‘kamar ga Allah.’ Kowane halin da kika nuna wa mijinki – ko nagari ko mugu, kamar ga Allah ne kika yi. Shi ya sa dole ki yi tunani game da irin halayen da kike nunawa.
Girmama mijinta da yabonsa:
Misalai:3:1–12; 23 “Zuciyar mijinta tana dogara gare ta, Ba kuwa za ya rasa riba ba, Takan yi masa alheri ba mugunta ba dukan muddar ranta.” “Mijinta sananne ne a kofar gari, Yayin da yana zaune a tsakiyar dattawan gari.” Haka cikin Misalai:12:4: Maganar Allah na cewa “Mace mai tsabtar rai kambi ce ga mijinta, Amma mai aikin kunya tana kamar rubewa cikin kasusuwansa.” Koda a ce mijinki ba ya da hali mai kyau, amma idan kina ba shi girmansa domin kin san Allah ne Ya sa shi bisanki, za ki ga irin abin al’ajabin da zai faru ba da dadewa ba, balle a ce shi ma mai jin tsoron Allah ne, gidanku lafiya kawai.