Aure dole
Wani Saurayi ne yana son wata yarinya, rannan sai ya shirya zai je su gaisa da mahaifinta, domin idan ya amince ya turo iyayensa a yi maganar aure. Ya isa gidan surukan nasa yana shan taba. Ga yadda hirarsu ta kwashe da mahafin yarinyar:Saurayi: Baba ina kwana?Baba: Lafiya lau, ashe da ma kana shan taba?Saurayi: […]
Wani Saurayi ne yana son wata yarinya, rannan sai ya shirya zai je su gaisa da mahaifinta, domin idan ya amince ya turo iyayensa a yi maganar aure. Ya isa gidan surukan nasa yana shan taba. Ga yadda hirarsu ta kwashe da mahafin yarinyar:
Saurayi: Baba ina kwana?
Baba: Lafiya lau, ashe da ma kana shan taba?
Saurayi: A’a, ba halina ba ne, na saba ne idan na sha giya ba na jin dadi, sai na sha taba.
Baba: Tabdi! Wato har giya ma kake sha ke nan?
Saurayi: A’a, idan na je gidan rawa ne kawai nake sha.
Baba: To, har gidan rawa kake zuwa?
Saurayi: Eh! Amma da can ba na zuwa, sai da na dawo daga gidan yari ne na fara zuwa.
Baba: Gidan yari fa ka ce, kai kuma me ya kai ka can?
Saurayi: kaddara ce ta sa na je, kisan kai na yi.
Baba: Kisan kai, wa ka kashe?
Saurayi: Wani baban budurwata na kashe saboda na tambayi auren ’yarsa ya hana ni.
Baba: Kai, Lale marhabin da saurayin ’yata. Gobe ka turo iyayenka mu yi maganar aure. (Mahaifin ya yi haka ne saboda tsoro, ya ji zancen kisa).
Daga Isah Ramin Hudu Hadeja, 08060353382.