Aure nake so —Adam Zango ya lashe amansa
Adam A Zango ya bayyana dalilin da ya ja baya a harkar Kannywood
Fitaccen mawaki kuma jarumin Kannywood Adam A Zango ya lashe amansa kan batun rashin kara aure a rayuwarsa.
Adam A. Zango, ya bayyana a hirar da Sashen Hausa na BBC ya yi da shi ranar Lahadi cewa a halin yanzu burinsa shi ne samun mace ta gari domin ya sake komawa daga ciki.
A cewarsa, ya janye kalamansa na watannin da suka gabata, bayan rabuwarsa da matarsa ta shida, saboda ya yi su ne cikin bacin rai da tsananin damuwa.
“Wadancan magnaganun na yi su ne ina cikin bacin rai da damuwa, don sai da na dinga ganin likitan tsananin damuwa (depression) yana ba ni shawarwari.”
Idan za a iya tunawa dai Zangon ya rabu da matar tasa ne kan amfani da soshiyal midiya ta hanyar da a cewarsa ba ta dace ba, da sunan tallata sana’arta.
Jim kadan bayan hakan ya fito soshiyal midiya yana neman shawarar mutane kan ko ya auri Ahlul Kitabi ne ya huta?
To sai dai a tattaunawarsa da BBC ranar Lahadi, Zangon ya ce sam ba har zuciyarsa ya yi wadannan maganganun ba, hasalima babban burinsa a rayuwa shi ne samun mace ta gari ya aure ta.
Dalilin da na ja baya a Kannywood —Adam Zango
Jarumin ya ci gaba da cewa, saboda halin da ya shiga a wancan lokaci, “sai da na dinga ganin likitan tsananin damuwa (depression) yana ba ni shawarwari, shi ya sa na ja baya da harkar Kannywood gaba daya.
“Sannan ga girma da ya zo min, don haka na matsa don bai wa ‘yan baya dama su ma su ci kasuwar”.
Hukumar tace finafinai ba ta da hurumin tantance ’yan fim
Game da harkar Kannywood da halin da take ciki, musamman zargin lalata tarbiyya, Adam Zango, ya ce, Hukumar Tace Finafinai da Dab’i ta Jihar Kano ba ta da hurumin tantance ’yan fim.
Adam Zango ya ce hurumin da hukumar ke da shi ya tsaya ne akn tantance finafinai kadai, wanda hakan ya sanya matsalolin masana’antar ke kara ta’azzara.
A cewarta, wannan kadai ya isa ya sanya al’umma su dinga yi musu uzuri kan rashin da’ar da wasu matan masana’antar ke nunawa, domin kuwa iyayensu ma ba su isa da su ba, balle kuma su.
“Kusan dukkanin jaruman nan mata, iyayensu ba da son ransu suke barinsu yi fim ba.
“Wasu don sun dage ne, wasu matan aure ne ma, akwai wadanda ma sai sun fara sannan iyayen ke zuwa su kwashe su.”
To sai dai a tattaunawarsa da BBC ranar Lahadi, Zangon ya ce sam ba har zuciyarsa ya yi wadannan maganganun ba, hasalima babban burinsa a rayuwa shi ne samun mace ta gari ya aure ta.