Auren Dole: kalubale ga ’ya’ya mata (2)

Ita kuma uwar za ta zauna da ’yarta ta rarashe ta, ta gaya mata cewa ita babu yadda za ta iya, kawai ta bar wa Allah komai. Wani lokacin ta shawo kan ’yar tata, wani lokacin kuma ta bijere wa uwar; a samu matsala. Wani lokacin kuma ita uwar ce za ta kekashe kasa ta […]

Auren Dole: kalubale ga ’ya’ya mata (2)
Auren Dole: kalubale ga ’ya’ya mata (2)

Ita kuma uwar za ta zauna da ’yarta ta rarashe ta, ta gaya mata cewa ita babu yadda za ta iya, kawai ta bar wa Allah komai. Wani lokacin ta shawo kan ’yar tata, wani lokacin kuma ta bijere wa uwar; a samu matsala. Wani lokacin kuma ita uwar ce za ta kekashe kasa ta ce ga wanda take so, ko don wani abin duniya, ko kuma domin kila wata alaka da take son hadawa da wadanda take son aura wa ’yar tata.
Kuma akan samu matsala, wani lokacin uba ya dage da sai an auri wanda yake so, ita kuwa uwa ba ta son auren, kila domin ita ma akwai wanda take son a aura wa ’yar tata, ko kuma ba ta da wani wanda take son a aurar wa, kawai dai ita ba ta son wanda za a aura wa ’yar tata, kila domin ta samu labari a kan mummunar dabi’arsa ko kuma wani hali nasa wanda ba ta so, irin hakan uwa takan iya shiryawa da ’yar domin ’yarinyar ta tsere, ta bar gida, ta je wani gari wurin wasu ’yan uwanta amma da masaniyar uwar, ko kuma ta shiga duniya ba a san inda ta je ba. Amma kuma duk da masaniyar uwar a cikin shirin, wannan ma ya fi faruwa domin ni kaina dalilin wannan rubutun hakan ya taba faruwa a gare ni. Wata ta baro wani gari zuwa wajena a garinmu da sanin mahaifiyarta. Da kyar Allah Ya taimake ni, da ni da mahaifana muka lallabata ta yarda muka koma tare da ita gidansu, muka je muka sanar wa hukuma, aka shiga tsakani domin sulhunta al’amarin.
To, shawarata ga mahaifa da kuma ’ya’yansu mata dai a kan wannan al’amarin ita ce, mahaifi dai a cikin gidansa tamkar sarki ne a gari amma kuma kada wannan sarautar ta zamanto hanyar da za ta sanya ya koma tamkar dodo ga matansa da ’ya’yansa. A’a, ka zauna da su ka yi kyakyawar mu’amala da iyalinka wajen sakar musu fuska da kuma zaunawa kana sanya su nishadi, wani lokaci har da zama ana yin hira, wanda ta nan za ka fahimci halayen ’ya’yanka munana da kyawawa. Kuma sai ka san hanyar da za ka gyara halayensu. ’Ya’yan yau, ka haife su ne ba ka haifi halinsu ba. Idan ka yi hakan za ka shaku da iyalanka kuma za su kasance suna gaya maka korafe-korafensu. Wani lokacin ma za su iya gaya maka matsalolin da suke ciki, domin neman tallafinka wajen fitar da su daga cikin matsalar.
Haka ku mata, musamman budare, ku lura da cewa mahaifa wasu gimshikin rayuwar al’umma ne, Allah Ya ba su daraja da girma. Kuma Ya nemi da a yi ladabi da biyayya a gare su a kan kowane al’amari, matsawar bai saba wa shari’ar Allah ba. Haka kuma ki lura, tun kina karamarki, wallahi ba ki da kamarsu kuma yanzu haka da kika girma, wallahi mahaifiyarki ko mahaifinki sun fi kowa son ki zama abar kwarai, sun fi kowa son su ga kin auri wanda za ki samu kwanciyar hankali a gidansa, sun fi kowa son ki auri wanda za ki samu ci gaba da kwanciyar hankali a rayuwa amma kuma yanzu wai sai ki bijere wa zabinsu, ki watsa musu kasa a fuska, ki kunyata su; ki ce wai sai wanda kike so, wanda idan ma aka ce ya kawo kudin aurenki ba zai kawo ba.
Kawai yana zaune da ke yana bata rayuwarki, idan kika shiga wata matsala kuma ga iyayenki za ki dawo. Kuma idan ya tashi yin auren kuma iyayensa za su ce ba zai auri ’yar iska karuwa ba. Kuma alhali shi ne ya mayar da ke ’yar iskar, ko kuma ta dalilinsa ne kika koma karuwa.
Idan wani abin kunya ya faru gare ki, iyayenki ne za a yi wa maganar da kila za ta kona musu rayuwa. Idan ba a yi hankali ba ma su hadi zuciya su mutu su bar maki duniyar sai ki tsinci abin da za ki tsinta din.
Wanda idan haka ta faru to, hakika za ki tsinci kaskancin rayuwa ne domin abin da kika shuka shi ne za ki girba. Kuma kin saba wa Allah kin saba wa Manzon Allah (S.A.W.) a kan haka ko bayan kaskancin da kika samu a duniya idan kika je kabari nan ne uwa-uba. To, balantana kuma ki je can lahira, wanda can kan babu dadi.
Akan iya rabuwa da miji amma daga baya a sami wanda ya fi shi, akan iya rasa dukiya daga baya a sami wacce tafi ta, akan rasa lafiya daga baya a same ta, a kan iya rasa mukami daga baya a sami wani wanda ya fi shi. Akan iya rasa jin dadi daga baya jin dadin ya dawo, akan rasa komai amma daga baya kuma a sami abin da aka rasa din. To, amma mahaifi da mahaifiya su kam kwaya daya-daya ne, idan aka rasa su wallahi ba za a sami wasu tamkarsu ba.
A karshe, nasihata da ke ita ce, ki sani, wallahi, billahi, tallahi! Idan ana canza kowa a duniya, to ban da mahaifa; idan kin rasa su, to, kin rasa su har abada. Idan ma tun farko ba ki da mahaifi, to har duniya ta nade ba ki da mahaifi ke nan har abadar abada.
Allah Ya shiryar da mu, Ya ba mu abu mai kyau a duniya kuma a lahira Ya tsare mu daga azabar wuta.
Nata’ala Sambo Babi (Nasaba), 08063673656