‘Auren dole ya sa na kashe jaririn kishiyata dan mako biyu’

Wata matar aure mai suna Hindatu Abdullahi ta ce ta kashe jaririn kishiyarta dan mako biyu ta hanyar ba shi maganin kashe kwari ne saboda an yi mata auren dole da mahaifinsa.  Hindatu mai shekara 19 ta bayyana haka ne lokacin da take amsa tambayoyin manema labarai a Bauchi, bayan da ’yan sandan Jihar Bauchi […]

‘Auren dole ya sa na kashe jaririn kishiyata dan mako biyu’

Wata matar aure mai suna Hindatu Abdullahi ta ce ta kashe jaririn kishiyarta dan mako biyu ta hanyar ba shi maganin kashe kwari ne saboda an yi mata auren dole da mahaifinsa. 

Hindatu mai shekara 19 ta bayyana haka ne lokacin da take amsa tambayoyin manema labarai a Bauchi, bayan da ’yan sandan Jihar Bauchi suka gabatar da ita da wadansu mutum 22 da ake tuhuma da aikata laifuffuka daban-daban. 

Hindatu wadda take zubar da hawaye a lokacin ta ce, “Ni na kashe jaririn mako biyu bayan haihuwarsa, na aikata haka ne saboda na kasance cikin kunci a tsawon shekara biyu da na yi a gidan mijina. Domin an yi min auren dole ne da shi a matsayin matarsa na biyu, kuma ban taba kaunarsa ba ko kadan, saboda  shi da uwargidana suka rika gallaza mini.  Don haka na yanke shawarar kashe yaron domin bakin ciki.”

Ta ce bayan kashe shi an kama ta aka kai ta wajen ’yan banga wadanda suka yi mata bulala 80 da dorinar dukan doki kafin su kai ta wurin ’yan sanda, “Na yi da-na-sanin wannan danyen aiki, ina rokon gafara wajen mijina da matarsa da kuma jami’an tsaro,” inji ta. 

Kakakin Rundunar, DSP Kamal Datti wanda ya gabatar da wadanda ake zargin ya ce an kai rahoto ofishin ’yan sanda na Mainamaji cewa matar da ke kauyen Wuro Bogga a Gundumar Duguri a karamar Hukumar Alkaleri, da mijinta Abdullahi ya tafi aikin Hajji bana, ta karbi jaririn ne mai suna Muhammad Abdullahi daga hannun mahaifiyarsa Fatima ta shiga da shi cikin dakinta ta dura masa maganin kashe kwari da ake kira fiya-fiya, ya fita daga cikin hayyacinsa, kuma bayan kai shi wani karamin asibiti ya rasu. 

Kamal ya ce an samu saura maganin kashe kwarin da ta bai wa jaririn, kuma ana bincike a kai da zarar an kammala za a kai ta kotu. 

Ya ce sun kuma kama mutum biyu masu suna Abubakar Suleiman da Jamilu Usman bisa zarginsu da yunkurin yin fashi a wani gida da ke GRA a Bauchi, kuma sun same su da karamar bindiga da harsasai uku.