Auren Gata: Gwamnatin Kano ta sanya ranar aurar da mutum 1,500

Za a gudanar da walima bayan ɗaura auren waɗanda za su ci gajiyar shirin.

Auren Gata: Gwamnatin Kano ta sanya ranar aurar da mutum 1,500

Gwamnatin Jihar Kano, ta sanar da cewa za a gudanar da auren mutum 1,500 waɗanda za su ci gajiyar shirin auren gata daga ranar 6 zuwa 9 ga watan Agustan 2026.

Babban Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne, ya bayyana hakan a ranar Asabar.

Ya ce shirin zai gudana ne bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya amince da fitar da Naira biliyan 1.5 domin gudanar da shi.

A jadawalin shirin, za a fara da bai wa waɗanda za a aurar shawarwari a ranar 6 ga watan Agusta, sannan a yi ɗaurin aure a ranar 7 ga watan Agusta.

Za a yi walima a ranar 8 ga watan Agusta, yayin da za a raba musu kayan ɗaki da tallafin dogaro da kai a ranar 9 ga watan Agusta.

An tsara shirin ne domin tallafa wa marasa galihu, zawarawa, waɗanda aurensu ya mutu da kuma masu ƙaramin ƙarfi wajen sauƙaƙa musu ɗaukar nauyin aure.

Hukumar Hisbah ta ce kowace amarya za ta samu Naira 100,000 domin fara ƙaramar sana’a, yayin da kowane ango zai samu Naira 100,000 domin taimaka masa wajen biyan sadaki.

Haka kuma za a bainwa ma’auratan kayan ɗaki, kayan abinci da sauran kayayyakin da za su taimaka musu wajen fara rayuwar aure.

Sama da mutum 5,000 ne suka nemi shiga shirin, amma mutum 3,000 aka zaɓa bayan yi musu gwaje-gwajen lafiya da suka haɗa da cuta mai karya garkuwar jiki, cutar hanta, ƙwayoyin halitta, gwajin juna biyu da kuma amfani da miyagun ƙwayoyi.

Hukumar Hisbah ta gargaɗi jama’a da su guji biyan kuɗi domin shiga shirin, tana mai jaddada cewa shirin kyauta ne gaba ɗaya, kuma gwamnatin jihar ce ke ɗaukar nauyinsa.

Hukumar ta kuma ce ma’auratan za su fara gabatar da matsalolinsu ga Hisbah domin sasanci kafin su ɗauki matakin neman saki, a wani yunƙuri na ƙarfafa zaman lafiya da ɗorewar auren.

Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya ce shirin na daga cikin ƙoƙarin gwamnatinsa na tallafa wa marasa galihu da kuma rage matsalolin zamantakewa a jihar.