Auren jinsi: Mugabe ‘zai nemi auren Obama’

Shugaban kasar Zimbabwe Mista Robert Mugabe ya soki halatta aure a tsakanin ’yan luwadi da ’yan madigo (auren jinsi) da Kotun koli ta Amurka ta yi, inda ya sha alwashin zai je Fadar Shugaban Amurka domin neman auren Shugaba Obama. Mugabe ya bayyana haka ne a hirar mako-mako da yake yi da gidan rediyon kasar, […]

Auren jinsi: Mugabe ‘zai nemi auren Obama’
Auren jinsi: Mugabe ‘zai nemi auren Obama’

Shugaban kasar Zimbabwe Mista Robert Mugabe ya soki halatta aure a tsakanin ’yan luwadi da ’yan madigo (auren jinsi) da Kotun koli ta Amurka ta yi, inda ya sha alwashin zai je Fadar Shugaban Amurka domin neman auren Shugaba Obama.

Mugabe ya bayyana haka ne a hirar mako-mako da yake yi da gidan rediyon kasar, inda ya ce zai je birnin Washington DC ‘ya durkusa a kan gwiwoyinsa ya nemi aurensa (Obama).’
Shugaba Mugabe ya fadi a ranar Asabar cewa: ‘Na yanke shawara tunda Shugaba Obama ya amince da auren jinsi, yana goyon bayan ’yan luwadi, ina ganin wajibi ne in tafi Washington, DC, in durkusa a kan gwiwoyina in nemi aurensa.”
Shugaba Mugabe ya kara da cewa: “Na kasa gane yadda wadannan mutane suke fito-na-fito da umarnin Almasihu domin shugabanmu ya hana mutane luwadi,” inda ya zargi gwamnatin Amurka da kasancewa “zagin masu bautar Shaidan wadda ta zubar da mutuncin kasar Amurka,” inji shi.
Ya ce duk da cewa an gina kasar Amurka a kan ginshikin addinin Kirista ne, ‘lalatattun ’yan siyasa’ a yanzu suna kokarin hallaka ta.
Bayanin na Mugabe ya zo ne bayan awoyi da Kotun koli na Amurka ta yanke hukuncin halatta auren jinsi adaukacin jihohi 50 na kasar.
Yanke wannan hukunci ya jawo gudanar da bukukuwa a ranar Asabar, inda magoya bayan auren jinsi suka gudanar da fareti da bukukuwa a harabobin ginin Empire State da Niagara Falls da Fadar Shugaban Amurka ta White House.

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna