Auren jinsi ya haramta a Burkina Faso

Burkina Faso ta bi sahun ƙasashe 22 cikin 54 na nahiyar Afrika da suka haramta aure ko neman jinsi guda.

Auren jinsi ya haramta a Burkina Faso

Burkina Faso ta ayyana dukkan ayyukan ’yan luwaɗi da maɗigo a matsayin babban laifi a ƙasar.

Gwamnatin mulkin sojin Burkina Faso ta ce ta amince da wani kuduri bayan ganawa da masu ruwa da tsaki da zai ayyana auren jinsi a matsayin babban laifi a ƙasar.

Kasar da ke Yammacin nahiyar Afirka ta bi sahun ƙasashe 22 cikin 54 na nahiyar ta Afrika da suka haramta aure ko neman jinsi guda da ya kasance laifi da zai kai ga kisa ko ɗauri na dogon lokaci.

Gwamnatin mulkin sojin ƙasar ce ta sanya hannu kan dokar a lokacin taron majalisar zartaswar ƙasar.

Ministan Shari’a na ƙasar, Edasso Rodrigue Bayala ya ce sabuwar dokar ta amince ne da auren al’ada da na addini kawai cikin kundinta.

Za a miƙa dokar ga majalisar ƙasar domin saka hannu kafin shugaban mulkin sojin ƙasar, Kyaftin Ibrahim Traore ya tabbatar da ita.

A watan Mayun shekarar da ta gabata ne, Uganda ta zama ƙasar Afirka ta baya-bayan nan da ta ɓullo da ɗaya daga cikin dokoki mafiya tsauri kan auren jinsi a duniya.

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta

Mahara sun kai wa Sarkin Nupen Lokoja hari a fadarsa