Auren Naira miliyan 7 ya mutu cikin mako 2

Wani magidanci ya kai matarsa kara a gaban Kotun Lardi ta Shari’ar Musulunci da ke Kasuwar Kurmi, inda ya nemi kotun ta tilas wa matar tasa ta biya shi kudin da ya kashe a wjen aurenta har kimanin Naira miliyan bakwai, sakamakon kin amincewa da ci gaba da zama da shi a matsayin mijinta da […]

Auren Naira miliyan 7 ya mutu cikin mako 2
Auren Naira miliyan 7 ya mutu cikin mako 2

Wani magidanci ya kai matarsa kara a gaban Kotun Lardi ta Shari’ar Musulunci da ke Kasuwar Kurmi, inda ya nemi kotun ta tilas wa matar tasa ta biya shi kudin da ya kashe a wjen aurenta har kimanin Naira miliyan bakwai, sakamakon kin amincewa da ci gaba da zama da shi a matsayin mijinta da mata.

Mutumin mai suna Salisu Ibrahim ya bayyana wa kotun cewa ya auri matar tasa ce mai suna Mabruka Muhammad, ’yar asalin garin Agadez a kasar Nijar, kimanin mako biyu da suka gabata, sai dai matar ta ki yarda ta tare a gidansa. Don haka yake rokon kotu ta sanya matar tasa ta biya shi makudan kudin da ya kashe a wajen aurenta, inda ya ce tunda “ba kira ba abin da zai ci gawayi.”

Mai karar ya shaida wa kotun cewa a lokacin auren, ya kashe kudi kamar haka: “Na biya sadaki Naira miliyan uku da rabi. Kudin kayan lefe Naira miliyan daya da rabi sai kudin abincin biki Naira dubu dari bakwai, sai Naira dubu dari takwas don ta sayi sarka, sai Naira dubu dari biyar na gyaran jiki.”

Sai dai lokacin da kotun ta waiwayi wacce ake kara Mabruka, ta amsa cewa dukan da’awar da mai kara ya yi gaskiya ne, sai dai ta bayyana cewa ita dai ba ta ra’ayin zama da shi.

Hakan ya sa Alkalin Kotun, Mai Shari’a Faruk Ahmad ya umarci matar ta mayar masa da dukiyar aurensa. Sai dai ta ce dukan kayayyaki da kudaden suna can wurin iyayenta a garin Agadez.

Daga nan Alkalin ya umarci a kai ta kurkuku har sai ta samu mai yi mata lamuni kafin ya bayar da belinta.