Auren Tata: Wata mai takaba ta samu Naira miliyan daya
Wata mai takaba mai suna Husaina Lawal da ke Unguwar Tudun ’Yan Lafidda da ke Katsina, ta samu Naira miliyan daya a shirin mai-rabo-ka-dauka a wajen auren Alhaji Umar Abdullahi Tsauri da aka fi sani da Tata a garin Dutsinma. Husaina wadda ke cikin yin takaba sanadiyyar rasuwar mijinta, tana da ’ya’ya bakwai da mijin […]
Wata mai takaba mai suna Husaina Lawal da ke Unguwar Tudun ’Yan Lafidda da ke Katsina, ta samu Naira miliyan daya a shirin mai-rabo-ka-dauka a wajen auren Alhaji Umar Abdullahi Tsauri da aka fi sani da Tata a garin Dutsinma.
Husaina wadda ke cikin yin takaba sanadiyyar rasuwar mijinta, tana da ’ya’ya bakwai da mijin ya bar ta da su, kuma ta barke da kukan murna lokacin da ta ji an ce ta dauko kuri’ar Naira miliyan daya daga cikin Naira miliyan 20 da aka ware wa mata mabukata 20.
Husaina a cikin kuka ta shaida wa manema labarai cewa za ta yi amfani da kudin wajen sayen muhalli da daukar karatun ’ya’yanta da kuma sayen abinci.
Ta gode wa Allah tare da yin addu’ar alheri ga mutumin da ya aiwatar da wannan taimako ga mabukata kuma ta yi kira ga masu dukiya su yi koyi da irin wannan aiki na alheri.
A ranar Alhamis din makon jiya ne Alhaji Umar Abdullahi Tsauri ya bayar da wadannan kyaututtuka a kofar gidansa da ke cikin garin Dutsinma domin nuna farin cikinsa a kan auren da ya yi.
Zabo matan da aka ba kudin an yi ne ta wata kafar labarai, inda aka zabo mata 16 da kowaccensu ta samu Naira dubu 10, sai mata uku kowacce Naira dubu 15, sai mata 15 Naira dubu 25 kowacce, sai mata tara kowace Naira dubu 30.
A rukuni na biyu an zabo mata 70 wadanda a cikinsu 50 suka samu Naira dubu 250, sai 20 da za su canki Naira miliyan daya. Sai dai ba kamar yadda aka saba gani a baya ba, wannan karo an yi cikin matakan tsaro.