Auren wuri na ‘kashe’ mata 60 kullum a Najeriya
Mata 22,000 ke mutuwa duk shekara a wajen matsalolin daukan ciki ko haihuwa.
Kungiyar Kare Hakkin Bil Adama ta Save the Children, ta ce auren wuri na sanadin rayuwar fiye da mata 60 kullum a Najeriya.
Save the Children ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar a daren Litinin yayin bikin ranar ’ya’ya mata ta duniya.
- Majalisa ta sahale wa INEC aika sakamakon zabe ta Intanet
- ’Yan sanda sun ceto uwa da ’yarta daga hannun masu garkuwa
Kungiyar a rahotanta, ta ce kashi 44 cikin 100 na ’ya’ya mata a Najeriya ana musu aure kafin su cika shekaru 18 a duniya, wanda wannan shi ne adadi mafi yawa a duniya.
Save the Children cikin sanarwar da shugabarta, Inger Ashing ta sanya wa hannu, ta ce mata a Najeriya na rayuwa mafi wahala a duniya.
Ta kuma shaida cewa mata 22,000 ke mutuwa a kowace shekara a wajen matsalolin daukan ciki ko haihuwa.
Cikin sabbin alkaluman da Kungiyar ta fitar, ta ce a Yammacin Afirka da kuma Afirka ta Tsakiya, ana samun kusan rabin matan da ke mutuwa saboda auren wuri da aka kiyasta a fadin duniya.