Auren ’Yan tagwayen da ya tattara ’yan biyu su biyar a wuri daya
Wasu angwaye ’yan biyu, Dinker da Dlraj sun auri tagwayen amarensu, Reena da Reema, a wani coci da ke Thrissur a Jihar Kerala ta kasar Indiya.Al’amarin da ya haifar da al’ajabi a wannan bikin aure shi ne, yaran ango da ’yan matan amarya da limaman coci duk tagwaye ne.Wadannan angwaye sun shafe shekaru biyar suna […]
Wasu angwaye ’yan biyu, Dinker da Dlraj sun auri tagwayen amarensu, Reena da Reema, a wani coci da ke Thrissur a Jihar Kerala ta kasar Indiya.
Al’amarin da ya haifar da al’ajabi a wannan bikin aure shi ne, yaran ango da ’yan matan amarya da limaman coci duk tagwaye ne.
Wadannan angwaye sun shafe shekaru biyar suna neman auren matansu, amma dai tun suna makaranta suka kuduri aniyar auren tagwayen mata, kamar yadda jaridar MailOnline ta ruwaito.
Sai dai wadannan ’yan uwa sun sha wahala wajen samun tagwayen matan da suka dace da su. Don haka suk sanya talla a jaridu na neman tagwayen mata, suka kuma bude shafin facebook na ’yan tagwayen Kerala, don neman amare.
A karshe dai suka dace da masoyansu. “Lokacin da muka hadu da Reena da Reema, mun fahimci irin su muke nema tsawon lokaci. Cikin sa’a kuwa, sai ta kasance su ma suna da tunani irin namu, bayan haduwarmu,” inji Dilraj.