Auren ’ya’yan sojoji da ke bariki abu ne mafi sauki – Kanar Sadik

Makarantar firamare ta Nurul Isamiyya da ke barikin sojoji na Dodon Barack da ke Ruduna ta 81 a Ikoyi a Jihar Legas, ta yi bikin yaye dalibai 24, 6 maza, 18 mata da suka sauke Alkur’ani Mai girma a ranar Asabar da ta gabata tare da kaddamar da kalandar Musulunci da nufin kara zaburar da […]

Auren ’ya’yan sojoji da ke bariki abu ne mafi sauki – Kanar Sadik
Auren ’ya’yan sojoji da ke bariki abu ne mafi sauki – Kanar Sadik

Makarantar firamare ta Nurul Isamiyya da ke barikin sojoji na Dodon Barack da ke Ruduna ta 81 a Ikoyi a Jihar Legas, ta yi bikin yaye dalibai 24, 6 maza, 18 mata da suka sauke Alkur’ani Mai girma a ranar Asabar da ta gabata tare da kaddamar da kalandar Musulunci da nufin kara zaburar da mutane sanin watannin Musulunci.

Babban Limamin Masallacin Juma’a na barikin, wanda har wa yau shi ne Mataikin Daraktan Harkokin Addinin Musulunci na Runduna ta 81, Laftana Kanar Sadik Abubakar ya ce makarantar da aka kafa fiye da shekara 60 ta samu nasarori da dama. “A da can ana gudanar da tsarin karantawar ne kadai ta yin amfani da alluna kawai, amma a yanzu an koma tsarin karantawar ta amfani da littattafai, wanda bayan karatun Alkur’ani, an sanya littattafai irin su Sira da Hadisi da Fikihu da Tajwidi da karatun sanin zamantakewa a tsarin addinin Musulunci,” inji shi.
Da ya tabo batun kalubale da makarantar ke fuskanta, ya koka kan yadda akasarin iyaye ke yi wa makarantun Islamiyya rikon sakainar kashi. Kuma ya shawarci iyaye su kula da karatu da tarbiyyar ’ya’yansu. Haka ya yi tsokaci game da fahimtar da wasu mutanen gari farar hula ke yi game da auren ’ya’yan sojoji mata, suna cewa auren ’yar soja sai soja ko dan bariki. Ya ce ba haka ba ne.
“Ina so in sanar da mutane cewa duk mutumin da yake so ya ga yadda ilimi da tarbiyyar Musulunci suke, to ya shigo bariki. ’Ya’yanmu suna da ilimi na addini da sanin yadda za su zauna da maigida idan sun yi aure. Mu ba ma bukatar komai sai sadaki kawai ga duk mutumin da ke bukatar auren ’yarmu. Saboda Manzon Allah (SAW) ya ce auren da aka yi da sadaki mai sauki ya fi albarka. Saboda haka duk mutumin da ke son auren ’yarmu, kofa a bude take,” inji shi.
Limamin sojan ya ce kada mutum ya ji shakkar zuwa bariki neman auren ’ya’yansu. Ya ce abin da mutum kawai zai yi, ya tuntubi malaman makarantar, su za su hada mutum da iyayen yarinya don ganin an yi auren cikin tsarin da shari’ar Musulunci ta tanada.
Shi ma babban bako a wurin yaye daliban, wanda ya wakilci Babban Kwamandan Rundunar, Kanar Garba ya yaba wa daliban game da kwazon da suka nuna na sauke Alku’ani Mai girma tare da yin kira ga iyayen yara su kara himma wajen kulawa da tarbiyra da ilimin ’ya’yansu.