Auren zawarawa na Tata: dan banga ya tsinci dame a kala
A ranar Juma’ar da ta gabata ne wani dan sintiri mai suna Abdulkadir Dikke da ke Funtuwa a Jihar Katsina ya tsinci dame a kala. Abdulkadir ya samu mace ne a cikin ruwan sanyi inda aka daura musu aure nan take a harabar Masallacin Juma’a na rukunin Gidaje Masu Saukin Kudi a garin Daura, wurin […]


A ranar Juma’ar da ta gabata ne wani dan sintiri mai suna Abdulkadir Dikke da ke Funtuwa a Jihar Katsina ya tsinci dame a kala. Abdulkadir ya samu mace ne a cikin ruwan sanyi inda aka daura musu aure nan take a harabar Masallacin Juma’a na rukunin Gidaje Masu Saukin Kudi a garin Daura, wurin da aka daura auren ’yan mata da samari 400.
Ana gama daura auren amarya Hauwa’u ta shaida wa Aminiya cewa,”Mun hadu a inda Tata ya yi rabon kaya a Katsina kwanakin baya inda ya ce yana sona, ni ma na ce ina sonsa. A haka soyayya ta kullu kuma bai wuce kwana biyu da haduwarmu ba aka gama raba kayan. Mun rabu ba tare da tunanin ko za mu sake haduwa ba, kwatsam sai ga wannan taro. Hakika zuciyata ta ba ni cewa za mu hadu a nan. Sai ga shi Allah Ya hada mu a nan masallacin da ake daura wa ’yan mata aure, inda na yanke shawarar a daura mana aure a nan.”
Hauwa ta ce kasancewarta bazawara ta san ba za a ki daura mata aure a nan ba, tunda dai cikin harabar masallaci a Katsina suka fara haduwa kuma ga shi a nan Daura ma a masallacin suka hadu ga kuma wanda ta dalilinsa ne suka hadu wato Alhaji Umar Abdullahi Tsauri (Tata). Ta ce, za ta bi mijinta sau da kafa tare da jan hankalin sauran zawarawa su yi wa kansu fada a kan halin da ake ci.
Shi kuwa ango Abdulkadir ya ce, bai san abin da zai ce ba kan farin cikin da yake ciki. Ya ce,”A lokacin da Hauwa ta ce mu je a daura mana aure na shaida mata cewa ba ya ga Naira dubu 2 ba ni da ko sisi, amma ta ce za ta sadaukar mini da kusan duk kudin sadakin nata. Duk kokarin da na yi don ganin mun ba abin wani lokaci ya ci tura. Nan take wata baiwar Allah ta dauki nauyin sadakin na sama da Naira dubu 9 bayan an jiyo daga malamai.” Ya yi alkawarin zai rike matarsa da mutunci tare da yin adalci.
Nana Mustafa dandagoro wadda ta dauki nauyin biyan sadakin ta ce, ta yi haka ne saboda raya sunnar Manzon Allah (SAW) kuma hakan zai taimaka wajen rage yawan zawarawan da ake da su.
Wanda ya wakilci ango wajen karbar auren Hauwa daga hannun waliyanta ya ce, a rayuwarsa bai taba ganin faruwa ko daura aure irin wannan ba.” Ban san ni’ima da rahama da albarkar da ke tattare da wannan aure ba, bisa lura da irin yadda abubuwa suka taho, inda Hauwa ta nace kan koda bashi ne a daura musu auren. Fatarmu Allah Ya ba su zaman lafiya.”
Umar Abdullahi Tata ya ba amarya Hauwa’u gudunmawar Naira dubu 100 don ta fara sayen kayan tarewa.
An dai daura auren samari 200 da ’yan mata 200 da suka fito daga kananan hukumomi 12 na yankin Daura a kan sadakin Naira dubu 20 ga kowace budurwa da shi Tata ya biya, sannan ya yi wa kowace amarya kayan daki da suka hada gadaje da kujeru da sauran kayan jeren daki. Su kuma angwaye ya ba su tallafin kudin da za su ja jari.
Alhaji Ibrahim Mohammad Yamel daya daga cikin iyayen da aka daura wa ’ya’yansu aure, ya gode wa Alhaji Tata kuma ya yi kira ga masu hali su yi koyi da abin da Tata ke yi don tsamo rayuwar matasa daga matsalolin fitsara.