Australiya na neman tsare Djokovic
Australiya na yunkurin tsare gwarzon dan wasan tennis na duniya, Novak Djokovic
Gwamnatin kasar Australiya na yunkurin tsare gwarzon dan wasan kwallon tennis na duniya, Novak Djokovic, a ranar Asabar zuwa ranar Asabar.
Wani lauya gwamnati, Barista Stephen Lloyd ya shaida wa wani zaman gaggawa da kotu ta yi a ranar Juma’a cewa Gwamnatin Australiya na bukatar haka ne bayan ta soke takardar izininsa ta shiga kasar a karo na iyu.
Hakan na nufin za a tsare gwarzon dan wasan kwallon tennisn na duniya, in ba haka, sai dai ya halarci zaman kotun ta intanet daga ofishin lauyansa tare da jami’an shige da fice.