‘Awakai biyu’
Barkanmu da warhaka Manyan gobe, tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin wasu ‘Akuyoyi biyu’ ne. Labarin ya kunshi yadda rashin dabara ke sanya mutum cikin wahala. A sha karatu lafiya.Akwai wasu awaki biyu a wani kauye wadanda ba su shiri da junansu. A kullum suna cikin […]
Barkanmu da warhaka Manyan gobe, tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin wasu ‘Akuyoyi biyu’ ne. Labarin ya kunshi yadda rashin dabara ke sanya mutum cikin wahala. A sha karatu lafiya.
Akwai wasu awaki biyu a wani kauye wadanda ba su shiri da junansu. A kullum suna cikin nuna isa ga junansu. Ga tsana ga magana mara dadi kuma babu wani kwakwarar dalilin yin hakan.
Rannan sai suka hadu a wata gada wacce ba za ta ishi su biyu su wuce a lokaci daya ba. Da dayan ta hangi dayan tana kokarin hawa kan gadar ton ta wuce, maimakon daya ya tsaya har sai wani daga cikin ya tsallake kafin ita ma ta wuce sai kowa ya shigo saboda girman kai.
Nan fa kowa ya rika matsowa har suka kusa da juna. A tsakiya gadar ce sai cacar baki ta sarke a tsakaninsu inda nan take suka kaure da fada. Kafin ka ce kwabo sun yi wa juna jina-jina kuma saboda tsananin fada suka fada kogin da ke kasan gadar.
Kafin ka ce kwabo ruwa ya yi gaba da su inda kowane daga cikinsu ya halaka.
Don haka darasin wannan labari shi ne Manyan Gobe ku zama masu hakuri da son junanku da mawabtanku.
Sai makon gobe zan sake kawo muku wani labari mai dadi.