Awaki sun shiga motar dan sanda sun cinye takardunsa

Lamarin ya faru a jihar Alabama ta Amurka

Awaki sun shiga motar dan sanda sun cinye takardunsa

Bidiyon wasu awaki da suka shiga motar sintiri ta ’yan sanda suka cinye takardunsa a garin Alabama da ke Amurka ya karade kafafen sada zumunta.

Dan sandan wanda ya fito daga ofishin ’yan sanda na Madison County Sheriff bayan ya kai wasu takardun aiki ya dawo ya tarar da awakin sun shiga cikin motar sun yi masa barna.

Daya daga cikin awakin ta shiga cikin motar ta kofar da direban ya bari a bude, sannan ta fara cin wasu takardu.

Daya akuyar kuwa saman motar ta hau ta yi dare-dare abinta, kamar yadda dan sandan ya bayyana.

Dan sandan ya ce saboda yawan gidajen da yake ziyarta a kullum, a wasu lokuta yakan bar kofar motarsa a bude sakamakon hare-haren da ’yan bindiga suka taba kai masa a baya.