AWEDI ta tallafa wa marayun rikicin Jos da kayan abinci da sutura
karar da Kabir Mohammed Jibiya ya shigar inda yake neman Hindatu Yusuf da ta fito masa da mijin da ta ce matarsa Amina Kabir take da shi a Katsina tare kuma zarginta da bata mata suna a kotun Shari’a da ke Jibiya da Mai shari’a Alhaji Kabir Hamisu Bello ya fara saurare tun a ranar […]
karar da Kabir Mohammed Jibiya ya shigar inda yake neman Hindatu Yusuf da ta fito masa da mijin da ta ce matarsa Amina Kabir take da shi a Katsina tare kuma zarginta da bata mata suna a kotun Shari’a da ke Jibiya da Mai shari’a Alhaji Kabir Hamisu Bello ya fara saurare tun a ranar 3/5/2016 ya dauki sabon salo.
A wancan zaman dai har wadda ake kara Hindatu Yusuf ta fara gabatar wa kotu da shaidun kariya a kan furucin da ta yi na cewa,”mijin Amina da ke Katsina,” wanda aka dage cigaba da sauraren wannan kara har zuwa 9/5/2016 amma zaman da bai yiwu ba a wannan rana saboda dalilai na tsaro, wanda hakan ya sanya alkali ya sake bayar da wata ranar domin cigaba da sauraren shari’ar,amma sai aka maido shari’ar a wata kotun a cikin garin Katsina kafin zuwan waccan rana da aka sanya. Ba a dai samu damar cigaba da sauraren wannan shari’a da aka kawo ba a wannan kotu da ke Katsina saboda sake mayar da ita waccan kotu da ke Jibiya, wadda ita ce ta fara sauraren karar domin ta cigaba da ita.
Kotun shari’ar da ke garin Jibiya wadda Mai shari’a Alhaji Kabir Hamisu Bello ke jagoranta ta cigaba da sauraren wannan kara wadda Kabir Mohammed Jibiya ya shigar inda yake neman Hindatu Yusuf da ta fito masa da miji na biyu da ta ce matarsa Amina Kabir na da shi a Katsina, a yayin da ita Hindatun ta yi wannan furuci a wata karar da ta shigar, inda take neman Amina da ta biya kudin da take binta bashi wadda ta ce tayi amfani da kudin inda ta bai wa mijinta na Katsina ya cika ya sayi mota. Wancan furucin da Hindatu ta yi ne, wanda ya fado a cikin kunnen Kabir wanda yake cikin kotu a lokacin da ake sauraren karar da ita Hindatu ta shigar, ya ba Kabir damar shigar da kara a kan ita Hindatun.
Kamar yadda Aminiya ta jiyo daga wata majiya da ke da kusanci da kotun (da ta nemi a boye suna),ta shaida mana cewa,bayan an kai wannan shari’a a Katsina a lokacin da aka ce an sake maido ta a wancan kotun ta Jibiya,shi Kabir ya rubuta takardar janye wannan kara da ya shigar amma kotu ta ki amincewa da haka har sai an tattaro duk wadanda shari’ar ta shafa, wadanda kuma suka hadu a ranar 6/6/2016 domin cigaba da sauraren shari’ar, wadda aka zauna a dakin alkali(chamber)saboda matakan tsaro.
Da kotu ta juya kan Kabir mai kara don jin ko yana da sauran wata alaka da Amina? Kabir ya amsa da cewa, “yanzu babu sauran wata alaka tsanina da Amina, saboda na ba ta takarda tun ranar 17/1/2015.” Har’ila yau,alkali ya tambaye shi ko wancan auren da tayi halak ne? Ya amsa da cewa, na halak ne. Da alkali ya tambaye shi cewa,to me ya sa ya yi mamakin maganar Hindatu? Sai ya amsa da cewa, “saboda ban sani ba,ba ta sanar da ni ba.” Amma kuma ya shaida wa kotu cewa,wannan saki da ya yi na biyu ne,kuma ta zauna a gidansa ne bayan ya sake ta, saboda tana dauke da ciki wanda shi ne ya bata damar ta zauna don ta yi idda, wanda yayi zaton ko sun shirya. Har wayau,alkali Kabir ya tambayi Kabir, ko shi ne waliyin Amina,kuma yanzu ya ga sabon mijin? Kabir dai ya amsa cewa ba shi ne waliyin Amina ba kuma ya ga sabon mijin da ya nemi Hindatu da ta kawo masa. A lokacin da kotu ta nemi jin cewa,ya san ya ba matarsa takarda tsawon shekara guda cewa ta yi wani auren? Sai Kabir ya amsa da cewa, “saboda ba ta fada mani ta yi aure ba, kuma tana zaune a gidana”.
Mai karar dai ya ce ya shigar da kara ne duk da bai yi bincike ba, saboda ita Amina ba ta gaya masa ta yi auren ba. Ya ce ya yi jayayyane a kan maganar Hindatu ne da farko,amma yanzu ya yi bincike ya kuma gano gaskiyar magana. Da alkali ya tambaye shi cewa,haka zasu cigaba, tana Katsina tana gidansa? Sai Kabir ya ce,wannan zabinmijinta ne, domin shi ne yake iko da ita.
Da kotu ta juya kan Hindatu wadda ake kara don jin ko tana da wata magana? Sai ta ce, “tun da ya san babu wata alaka tsakaninsu tana neman kotu ta bi mata hakkinta a kan ya san ba ya auren Amina amma ya yi kararta, wanda hakan ya bata mata suna. Kabir mai kara ya shaida wa kotu cewa,” na riga na yi bayanin dalilin karata da abin da na gano da dalilin janye karata da nayi. Idan kuma tana neman hakkinta sai ta shigar da kara domin kotu ta bincika.
Mai kara har ila yau ya shaida wa kotu hujjar da ta sa Amina take zaune a gidansa, “Babanta ya yi mani wasiya kan cewa ko ba ni auren Amina in ba ta wurin zama.”
Da aka juya a kan batun ciki da aka saki Amina da shi wanda daga bisani ya lalace kuwa,Kabir mai kara yace,a gidansa cikin ya lalace kafin ta yi wancan auren.
Kamar yadda alkali Kabir ya ce,bisa binciken da kotu ta yi, aikata hakan ya sa Kabir yin laifi babba yadda ya dauki fushi da Hundatu don ta ce,”sabon mijinta na Katsina. Kabir a nan ba Hindatu ya kamata ya kai kara ba,iyayen ita Amina ya kamata ya kai kara domin jin shin Amina ta yi wani auren ne? Kazalika, kotun ta binciko cewa,a cikin lafazin karar Kabir bai gitta kallar tsohuwar matarsa ba. Saboda haka Kabir ya cutar da Hindatu har ya sa ta biya kudi domin kiran mutane 3 da za su ba da sheda. A matsayin Hindatu na mace, ya tayar mata da hankali ba tare da ta yi masa laifin komai ba. A kan haka kotu ta yi Allah wadai da halin Kabir.
Alkalin kotun ya kawo wata aya daga cikin Alkur’ani(suratul Saffi,aya ta 2)wadda ke jan hankali da a guji yin wasa da abu 3, wanda aure na cikinsu, wanda shi Kabir ya yi wasa da shi, inda ya ce,”matata,” inda kuma ya hakikance a kan haka bayan kuma karya yake yi,bayan a can baya ya nemi lamuni na kudi a kotu,kuma ya nemi afuwa a wajen kotu cewa zai kawo Amina a ranar dawowa kotun,daga baya ya zo ya ce ba ta da lafiya, kamar matarsa.
A kan wancan bincike na kotu ya sa alkali Kabir Hamisu Bello ya yanke wa Kabir Jibiya, wanda ya yi karar Hindatu, hukuncin cewa,bisa dogaro da wadancan hujjoji kotun ta samu Kabir da laifin boye matar aure da kuma yin karyar cewa matarsa ce,alhali ya sake ta tun ranar 17/1/2015,ta yi idda har ta yi wani auren shi yana tare da ita a gidansa. Zai kuma biya Hindatu Yusuf Naira dubu 10 saboda bata mata suna da ya yi da kuma tayar mata da hankali. Kazalika,zai gyara wa kotu gilassan da aka fasa mata,zai kuma tafi gidan yari sati 2 ko ya biya tarar Naira dubu 5,kuma ya ji tsoron Allah.
Alkali Kabir ya bayar da dama daukaka kara ga duk wanda bai yarda da hukuncin ba a cikin kwanaki 30 da yanke wannan hukunci.