Ayo da Jona: Sai hali ya dace ake abota
Bisa ga dukkan alamu za a dade ana ta hayagaga da cacar baki game da batun jirgin saman Shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN), Pastor Ayo Oritsejafor da aka damke a kasar Afrika ta Kudu cike da miliyoyin dalolin sayen makaman da ke jibge a ciki. Dalili kuwa shi ne dangantakar kut-da-kut da ke tsakanin shugaban […]
Bisa ga dukkan alamu za a dade ana ta hayagaga da cacar baki game da batun jirgin saman Shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN), Pastor Ayo Oritsejafor da aka damke a kasar Afrika ta Kudu cike da miliyoyin dalolin sayen makaman da ke jibge a ciki. Dalili kuwa shi ne dangantakar kut-da-kut da ke tsakanin shugaban kungiyar da kuma Shugaban kasa, Goodluck Jonathan. Da ma an dade ana ta rade-radin cewa kungiyar Kiristocin na shisshige wa gwamnatin Jonathan, har ma ta kai bai iya tabuka komai sai abin da kungiyar ta kitsa masa, sa’annan kuma hatta manufofi da tsare-tsaren gwamnatinsa ma a coci-coci yake bayyanawa, domin kuwa a can ne ake ja masa gora bayan da aka makantar da shi.
Babu wani abin takaicin da ya wuce ganin yadda wannan kungiya mai alfarma ga mabiya addinin Kirista, kuma mai kwarjini a idanun sauran ‘yan Najeriya za ta zame ‘yar koren fadar shugaban kasa, wacce ake amfani da ita a matsayin ‘yar barandar masu kwanzarta bambance-bambancen addini a kasar nan. Tun daga lokacin da Pastor Oritsejafor ya zame shugaban kungiyar CAN sai ga shi nan shi da Shugaba Jonathan sun zame tamkar tib da taya, kuma dangantakar da ta kullu tsakaninsu na ta zubar da mutuncinsu a idanun ‘yan Najeriya. Dalili kuwa shi ne Pastor Oritsejafor da mukararrabansa sun mayar da kungiyar Kiristoci ta CAN wani bangare ne na fadar Shugaban kasa, kuma dandalin gudanar da harkokin siyasarsa.
Ana cikin jin takaicin yadda shugabannin kungiyar CAN suka zarme cikin son abin duniya da sayar da mutuncinsu ga gwamnatin da ke amfani da addini don biyan bukatarta, sai kuma Cocin Anglican Communion, wanda Shugaba Jonathan ke halarta, ya ba shi wata babbar kyautar girmamawa. Babu dalilin bai wa Shugaba Jonathan kyauta irin waccan domin bai cancanci haka ba. Babu wata shaida kuma da ta nuna cewa an taba bai wa wani mahaluki irin wannan kyautar a wannan cocin. Wannan dai wata kyauta ce da aka yi, walau dai don a tatsi wani abu daga Shugaba Jonathan, ko kuma a kara karfafa masa gwiwa wajen bin tafarkin amfani da addini don biyan wata kazamar bukatarsa.
Baicin haka nan kuma ‘yan Najeriya ba su gamsu da wannan kyautar da aka yi wa Jonathan ba, domin kuwa sai da aka ce shugabannin bangarorin jam’iyyar PDP sun amince masa sake tsayawa takara ne aka yi haka. Shin wai shugabannin Cocin Anglican sun yi la’kari da halin rashin tsaro da ya hana Jonathan ceto ‘yan matan Chibok da ake cewa an mayar da su sa-daka, har ma wasu na da juna biyu kafin girmama shi? Sun taba tunanin cewa Jonathan bai cancanci irin waccan kyautar ba, domin babu wani abin alherin da ya tsinana wa kasar nan tun darewarsa karagar mulki shekaru shida da suka shude? To, idan kuwa Cocin Anglican na sane da haka da wane dalili ne shugabanta zai karrama shi da waccan kyautar da ba a taba girmama wani da irin ta ba? Dangane da haka ana iya cewa Cocin Anglican ya shiga cikin harkar yakin neman zaben Shugaba Jonathan ke nan gadan-gadan, tun daga yanzu.
Ba shakka da walakin, wai goro a miya, kuma biri ya yi kama da mutum. Shi dai shugaban wancan Cocin na Anglican, Primate Nicholas Okoh, mataimakin Pastor Ayo Oritsejafor ne a kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN), kuma shi ma dan asalin Jihar Delta ne. To ga shi nan sun yi watsi da yin wa’azi sun zame ‘yan koren gwamnatin da ta mayar da addini makamin yakar wadanda take adawa da manufa ko akidarsu. To idan har Pastor Oritsejafor da Primate Nicholas Okoh na sha’awar siyasa ne sai su fito fili, firi-falo, su shige ta, amma ba su dinga fakewa da addini suna cutar da wasu bayin Allah ba.
Sa’ilin da aka fara surutai game da badakalar jirgin Oritsejafor da kuma kudaden da aka samu a ciki wanda abokin huldarsa, Shugaba Jonathan ya ce gwamnatinsa ce ta yi sautun makamai da su, sai shugaban CAN din ya ce wai ana nema a shafa wa addinin Kirista kashin kaji ne kawai. Jin haka ya sa kungiyar CAN din ta bayar da sanarwar da hatta ma magoya bayanta ba su ji dadinta ba, domin kuwa cewa ta yi wai ‘yan siyasa ne, musamman ma ‘yan kungiyar All Progressibe Congress ta adawa suka haddasa haka. Sanarwar kungiyar CAN din ta kara da cewa jam’iyyar APC ta Musulmi ce zalla. To ta mance cewa akwai miliyoyin Kiristoci a cikinta, wadanda kuma ke kishinta fiye da kima. To wai yaushe ne aka daukaka wata jam’iyya bisa addini da har za a ce wata jam’iyyar ta kafurce wa manufofinta?
To amma idan har Pastor Ayo na cewa jam’iyyar APC ce ke haddasa masa fitina domin ta Musulmi ce, me za a ce game da yadda shi da kansa ya kasance limami ko kuma malamin Shugaba Jonathan da kuma yadda ya shiga siyasa tsundum, yana goyon bayan Jonathan? Kowa na sane da yadda Pastor Oritsejafor ya tsoma kungiyar CAN cikin jam’iyyar PDP tsundum, amma kuma babu wanda ya zarge shi game da dagula harkokin kungiyar da batutuwan siyasa. Ya dai tabbata cewa Pastor Oritsejafor ya kasance dan baya ga ‘yanuwansa, sauran limaman Kirista, domin kuwa sun wanke masa hannu akai, sun nuna cewa ya zame wake guda da ya bata garin Kiristoci a kasar nan. To, Allah Ya sa mabiyasa da kuma sauran Kiristoci za su fahimci haka, su kuma guji ci gaba da hada siyasa da addini.