Ayodele Fayose zai tsaya takarar shugabancin Najeriya

Gwamnan Jihar Ekiti Ayodele Fayose ya bayyana aniyyarsa ta tsayawa takarar shugabanci qasa a zaben 2019. Fayose wanda dan jam’iyyar PDP ne, ya dade yana sukan ayyukan gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari. Fayose dai ya fara zama gwamnan Jihar Ekiti a shekarar 2003 sannan ya sake zama gwamnan jihar a shekarar 2014. Zuwa yanzu dai shi […]

Ayodele Fayose zai tsaya takarar shugabancin Najeriya

Gwamnan Jihar Ekiti Ayodele Fayose ya bayyana aniyyarsa ta tsayawa takarar shugabanci qasa a zaben 2019.

Fayose wanda dan jam’iyyar PDP ne, ya dade yana sukan ayyukan gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

Fayose dai ya fara zama gwamnan Jihar Ekiti a shekarar 2003 sannan ya sake zama gwamnan jihar a shekarar 2014.

Zuwa yanzu dai shi ne mutum na farko da ya bayyana aniyyarsa ta neman shugabancin kasar a hukumance duk da cewa ana tunanin mutane da yawa suna sha’awar mulkin qasar, musamman daga yankin Arewa inda jam’iyyar ta PDP ta yi alkawarin fito da dan takara.

A cewarshi “Duk da cewa jam’iyyar PDP ta yi alkwarin fitar da dan takarar shugabancin qasa daga Arewa ne, babu wanda ya fito ya nuna a fili cewa zai yi takara daga yankin. Wannan ne ya sa na fito fili na bayyana aniyata na neman shugabancin qasar,” inji shi.