‘Ayyuka za su wadata idan aka bunkasa kere-kere’

Aminiya: Me ye ya ja hankalinka ka rungumi wannan sana’a kuma a wane lokaci ne ka bude wannan masana’anta?Mun bude wannan masana’anta ta sarrafa karafa  ne shekara 12 da suka gabata, kuma babban abin da ya karfafa mini gwiwar rungumar wannan sana’a shi ne ni tun ina karami Allah Ya sa mini sha’awar kere-kere,  domin […]

‘Ayyuka za su wadata idan aka bunkasa kere-kere’
‘Ayyuka za su wadata idan aka bunkasa kere-kere’

Aminiya: Me ye ya ja hankalinka ka rungumi wannan sana’a kuma a wane lokaci ne ka bude wannan masana’anta?
Mun bude wannan masana’anta ta sarrafa karafa  ne shekara 12 da suka gabata, kuma babban abin da ya karfafa mini gwiwar rungumar wannan sana’a shi ne ni tun ina karami Allah Ya sa mini sha’awar kere-kere,  domin a lokacin da nake karami hatta wasanni irin na yara babu abin da nake sha’awa, kamar abubuwan da suka shafi karafa. A lokacin da nake karami nakan je na nemo gwangwanaye na hada motoci.
A lokacin da nake karatun Islamiyya, sai Allah Ya hada ni da wasu Larabawa wadanda suka zo suka kafa wata masana’antar sarrafa karafa a unguwar Mai Adiko da ke   nan kusa da garin  Jos, inda suke kera kayayyakin aikin noma, kamar garmar shanu da sauran karafuna aikin gona. A lokacin da Allah Ya hada ni da su a ranar da na  fara zuwa kamfanin, sai na yi sha’awar abubuwan da suke yi a wannan kamfani. Sai na nemi na yi kasuwanci da su, sai suka ba ni dama na rika kai masu karafa daga nan cikin  garin Jos.
Muna nan muna  wannan harka da su har ta kai ga ni ma ina sayen kayayyakin da suke sarrafawa ina sayar wa a cikin garin Jos da sauran wasu garuruwa, wato na zama kamar dilansu.
Muna cikin tafiya da wannan kamfani sai aka zo aka sami rikicin Jos na shekarar 2001. Wannan rikici ya sanya suka rufe ayyukansu har ya zuwa wannan lokaci. Wannan ne ya karfafa mini gwiwar  kafa wannan masana’anta tawa ta kaina.

Aminiya:Kamar yaya kuke yi wajen gudanar da wannan sana’a?
To muna samo karafa ne mu zuba su a wuta, mu  narka su su zama ruwan karfe, mu yi abin da muke son mu yi da su.

Aminiya: Kamar wadanne irin kayayyaki ne kuke kerawa a wannan masana’anta?
Muna kera  hakoran injinan nikan garin tuwo da injinan markaden tumatur da gyero da hakoran garmunan shanu  da dai sauransu, muna kai wa kasuwa mu sayar kuma muna kera  kayayyakin mota  da ake sawa mu kera, kamar kamfanin NASCO da ke nan garin Jos, suna samu mu kera masu kayayyakin motocinsu da suka lalace. Haka akwai kamfanoni da dama da suke kawo mana kayayyakinsu da suka lalace mu gyara masu.

Aminiya: A ina ne kuke samun karafan da kuke sarrafa a wannan masana’anta?
Kamar yadda muke samun kayayyakin da muke sarrafawa muna samun wadannan kayayyaki ne a wuraren da ake gyaran motoci. Muna samun karafan da suka lalace wadanda ake cirewa a motoci a wadannan wurare na gyaran motoci. Irin wadannan karafa ne muke saya a wuraren masu gyaran motoci mu zo mu narka su, bayan  sun zama ruwa, mu sarrafasu zuwa irin karfen da muke bukata mu yi.

Aminiya: Daga lokacin da kuka bude wannan masana’anta zuwa yanzu, wadanne irin nasarori ne kake ganin kun samu?
A gaskiya mun samu nasarori da dama a wannan masana’anta. Domin a lokacin da muka bude wannan masana’anta dukkan ma’aikatan wannan masana’anta ba mu fi mu hudu ba, amma a yanzu mun kai mutum 15 zuwa 17.
Bayan haka akwai dalibai da ake kawo mana daga manyan makarantun kasar nan daban-daban, da suke zuwa suna ganin yadda muke narka karafa tare da sarrafa su  a wannan masana’anta. Sannan muna samun dillalai wadanda suke zuwa daga waje suna sayen karafan da muke sarrafawa.

Aminiya: Wadanne irin matsaloli ne kuke fuskanta a wannan masana’anta?
A gaskiya rikice-rikicen da aka samu a wannan jiha su ne babbar matsalar da muka  fuskanta a wannan masana’anta, domin da dama abokan cinikinmu da suke zuwa daga waje sun daina zuwa, sakamakon wadannan tashe-tashen hankulan da aka yi fama da su a baya.

Aminiya: Wace gudunmawa ce irin wadannan masana’antu  suke bayar wa a kasar nan?

Gudunmawar da muke bayarwa tana da yawa kwarai da gaske, musamman ta wajen samarwa da matasa ayyukan yi.  Duk  wata kasa da ka ga ta ci gaba a duniya,   ta yi amfani da wannan sana’a ce  ta kere-kere. Don haka idan har gwamnati ta rungumi harkokin kere-kere tattalin arzikin Najeriya zai bunkasa, kuma Najeriya za ta shiga sahun kasashen da suka ci gaba ta fuskar tattalin arziki.

Aminiya: A karshe me ye sakonka ga gwamnati?
Ina kira ga wannan sabuwar gwamnati kan ta yi kokari ta samar da yanayi mai kyau ga irin wadannan kananan masana’antu namu, domin mu samu damar bunkasa. Ta hanyar samar mana da fasaha irin  ta zamani da na’urori irin na zamani.