Ayyukan Ƙungiyar NAFOWA a faifan nazari

An assasa kungiyar Matan Rundunar Sojojin Sama ‘NAFOWA’ ne jim kaɗan da kafa rundunar ta sojojin Saman Nijeriya.  Mutum na iya kallon wannan cibiya tamkar sauran kungiyoyi, sai dai yana da kyau a san cewa, baya ga ayyukan raya kasa da kungiyar ke yi, kungiya ce da ke la’akari da irin halin kuncin da marasa […]

Ayyukan Ƙungiyar NAFOWA a faifan nazari

An assasa kungiyar Matan Rundunar Sojojin Sama ‘NAFOWA’ ne jim kaɗan da kafa rundunar ta sojojin Saman Nijeriya.

 Mutum na iya kallon wannan cibiya tamkar sauran kungiyoyi, sai dai yana da kyau a san cewa, baya ga ayyukan raya kasa da kungiyar ke yi, kungiya ce da ke la’akari da irin halin kuncin da marasa karfi suke ciki, ta hanyar tallafa musu da inganta rayuwarsu. Ƙungiyar NAFOWA ta kasance mai mutunta marasa galihun da suka ci moriyar ayyukanta. Wadannan ayyukan alheri da kungiyar ke gudanarwa, na nuna irin wakilcin da matan sojojin saman ke yi.

A yayin da mazajensu ke fafatawa a fagen fama, don ganin maketata da azzalumai ba su yi nasara akan Najeriya da iyakokinta ba, ita kuma kungiyar NAFOWA na iya kokarinta wajen ganin ta rage radadin talauci da fatara a tsakankanin al’umma, musamman ma yin abubuwan da za su tsamo marasa galihu da matasa daga rayuwar talauci, ta hanyar ba su gudummawar jari ko horon sana’a da za su dogara da kawunansu. Tare kuma da ba su horo a fannonin daban-daban domin rayuwarsu ta inganta, su iya tsayuwa da kafafuwansu a rayuwa ba tare da sun dogara da wasu ba.

NAFOWA kungiya ce da ta kunshi iyaye kuma matan sojoji nagartattu, wadanda suka sauya fasalin rayuwar mata da yara masu ɗimbin yawa a Nijeriya, ta hanyar koya musu sana’o’i da jari. kungiya ce da ayyukanta suka yi tasiri a garuruwan Legas da Barno da Fatakwal da Benin da Abuja da Binuwai da Bauchi da sauransu.

Kwanan nan, kungiyar NAFOWA ta yaye mata da matasa 150, wadanda suka samu horon sana’o’i a garin Fatakwal ta Jihar Ribas, inda Shugabar kungiyar take da zama, wato Hajiya Hafsat Sadikue Abubakar.

Shugabar ta bayyana cewa, sun bayar da wannan horo ne domin tallafa wa iyalan Sojojin Sama da ke Barikin Makurdi, wadanda yawancin Mazajensu ke fagen yaki da ‘yan kungiyar Boko Haram masu tayar da kayar baya.

Ta ce, kungiyar NAFOWA za ta fadada wannan shiri zuwa wasu barikokin, saboda ana matukar bukatar hakan. A ta bakinta, cikin shekaru biyu, ƙungiyar ta horas tare da tallafa wa sama da mutum 800, tun daga watan Mayun 2016.

Wannan shiri karo na shida an buɗe shi ne a garin Bauchi a ranar 13 ga watan Oktobar 2017. kungiyar NAFOWA ta yi imanin cewa idan aka ba mata horo da tallafi, tamkar an tallafa wa dukkanin iyali ne. Sannan kuma tallafin da ake bayar wa ga wadanda suka samu horo, ana ba su ne don su kafa kansu.

Wannan shiri na NAFOWA ana gabatar da shi ne cikin makonni 10. Inda ake horas da fannonin da suka hada da dinkin zamani, girke-girke, kitso da aski, ilimin kwamfuta, kera kofofin zamani da tagogi, takalma, jakkunan hannu, ruwan sabulu, omo da man shafawa da dai sauransu. Bayan an kammala horaswar, ana ba wadanda aka yaye tallafi don su bude sana’o’insu su dogara da kansu. Cikin abubuwan da ake ba su sun hada da keken dinki (ga daliban da suka koyi dinki), na’urar yin kek mai girman lita 40 (ga ɗaliban da suka koyi girke-girke), na’urar wanke gashi da gyara shi, kwamfutoci, kayan kwalliya, kayan haɗa takalma, sinadaran haɗa ruwan sabulu, da sauransu.

Kuma an ba da shawarwari na musamman ga wadanda suka samu nasarar kammala bayar da horo a cikin shirye-shiryen da aka koya musu karkashin tsarin wannan kungiya, domin dai ya kasance sun yi amfani da abubuwan da suka koya ta hanyar da ta dace. Wannan kungiya ba ta takaita kanta ga ayyuka a tsakanin gidan soja kadai ba, ta faɗaɗa harkokinta zuwa sauran yankunan al’umma, domin a rika samun kyakkyawar dangantaka tsakanin matan sojoji da farar hula. 

Ayyukan NAFOWA kullum kara habaka suke yi, kuma shugabanninta sun himmatu wajen ganin an gudanar da komai yadda ya kamata. Wannan tasa suka mayar da hankali tare da bullo da sababbin shirye-shirye na jin-kai da taimakon al’umma; saboda haka ne ma take ziyartar gidajen marayu, asibitoci da sansanin ‘yan gudun hijra a fadin kasar nan. kungiyar ta riƙe kambinta na jagaba wajen koya sana’o’i ga mata da maza domin nuna masu hanyoyin dogaro da kai. Har ila yau, tana ɗaukar karatun ƙananan yara, kula da masu cutar daji, tabbatar da adalci tsakanin mata da abokan zamansu ta hanyar haɗa kai da kungiyoyin mata na sauran kasashen duniya.

Kasancewar NAFOWA kungiya mai zaman kanta, tana samun kudin gudanar da ayyukanta daga mutanen kwarai, waɗanda suke da tausayi, kungiyoyi da kuma mambobin kungiyoyin jin-kai. Baya haka, Rundunar Sojin Sama tana ba da tata gagarumar gudunmawar don tabbatar da samun daidaito. Kasancewar NAFOWA tana hulda da al’umma daban-daban, shi ya sa hukuma ta shigo ciki, wanda hakan yana taimakawa ƙwarai wajen samun kyakkyawar dangantaka tsakanin sojojin sama da kuma farar hula.

Yayin yaye wasu daga cikin daliban da wannan kungiya ta yi a kwanan baya, Shugabar NAFOWA ta yi wani jawabi mai ratsa zuciya, inda ta ce, “Goyon bayan da nake samu daga maigidana Hafsan Sojin Sama, Sadikue Baba Abubakar shi ne ƙashin bayan nasarar wannan kungiya. Gudunmawarsa ta bangarori daban-daban na harkokin wannan ƙungiya hakika ba mu da abin da za mu iya biyan sa. Gudunmawarsa ta fuskar ba da tallafi da koyawa matasa sana’o’i abun yabawa ne. Dukkan waɗannan abubuwan da muke bugar kirjin mu ce mun yi, suna kasantuwa ne sakamakon gagarumar rawar da yake takawa kasancewarsa mutum mai son ci gaban al’umma.

 “Zan yi amfani da wannan dama, a madadin mata, maza, matasa da kananan yara da suke Rundunar Sojin Sama, mu gode wa maigida bisa namijin kokarin da yake ga wannan ƙungiya. Hakika ya zamo uba garemu baki-ɗaya.”

NAFOWA ta nuna wa duniya himmar da take da ita na bada taimako da jin-kai ga mata, tabbatar da kyakkyawar dangantaka mai cike da soyayya a tsakanin mata, da kuma karfafa masu gwiwa a fannoni daban-daban na rayuwa, ta hanyar rage masu raɗaɗin da yake damunsa a wannan kasa da take fama da matsaloli iri-iri. Hakika labarin nasarorin NAFOWA abin yaba wa ne da kowane mutum zai so ji; tabbas zai ci gaba da kasancewa cikin labarai masu kayatarwa na ayyukan da matan kwarai ke yi. 

Hauwa ta rubuto ne daga Mabushi, Abuja