Ayyukan kungiyar Kwankwasiya sun wuce siyasa kawai – Alhaji Abdulhadi
Jagoran kungiyar Kwankwasiya na Jihar Katsina wanda kuma shi ne shugabanta na kasa Alhaji Abdulhadi, wanda aka fi sani da suna Kila, ya ce ayyukan kungiyar sun wuce batun siyasa kawai, a tattaunawar da ya yi da Aminiya a Katsina. Ga yadda tattaunawar ta kasance: Ka bayyana mana matsayar wannan kungiya a Jihar Katsina? […]
Jagoran kungiyar Kwankwasiya na Jihar Katsina wanda kuma shi ne shugabanta na kasa Alhaji Abdulhadi, wanda aka fi sani da suna Kila, ya ce ayyukan kungiyar sun wuce batun siyasa kawai, a tattaunawar da ya yi da Aminiya a Katsina. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
Ka bayyana mana matsayar wannan kungiya a Jihar Katsina?
To zan fara da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai. To kamar dai yadda mafi yawan jama’a suke dauka wa wannan kungiya ta siyasa ce kuma ta masu goyon bayan Sanata Kwankwaso. E, haka ne. Sai dai kuma abin da wasu basu sani ba akan wannan kungiya shi ne ba ta tsaya a kan batun harkokin siyasa ba kawai, musamman a Jihar Katsina. Muna amfani da wannan kungiya wajen aiwatar da duk wasu ayyukan da sauran kungiyoyi suke yi. Misali, muna aiwatar da aikin gaiya irin na tsabtace muhalli, gyaran makabartu, taimakon gajiyayyu, tallafawa ‘yan makaranta wajen batun ilminsu musamman wadanda muka lura iyayensu basu da karfi. Sannan muna kokarin samarwa matasa yiyukan yi, misali kaisu wajen koyon sana’o’in hannu da sauransu. Kuma wannan duk ya samo asali da irin halayen shi Sanata Kwankwaso na ganin cewa al’umma musamman marassa karfi basu tagayyara ba. Ba sai mun sake maimaitawa ba, kowa ya ga irin rawar da ya taka wajen kwato hakkin talakawa musamman ‘yan Arewa tun kafin jam’iyyarsa ta hau mulki. Munga irin rawar da ya taka a Jihar Legas da kuma abin da ya faru a Mambila, baya ga ‘yan kanana wadanda basu lissafuwa. Wadannan misalai da muka yi la’akari da su sun kara mana kwarin gwiwa a nan Jihar Katsina da kuma tunanin yadda zamu mayar da kungiyar ta zamo mai amfani ce ga al’umma ba wai sai batun siyasa ba. Hakan ne kuma yasa a yanzu cibiyar ita wannan kungiya ta Kwankwasiya amana take da mazauni a nan Katsina maimakon Kano kamar yadda wasu za su yi tsammani.
Ta yaya kake jagorantar wannan kungiya a matakin kasa maimakon jiha?
To acan baya na sha jagorantar kungiyoyi musamman na siyasa a matakin jiha, amma a yanzu saboda irin yadda aka ga ina taka rawa a wajen harkokin kungiya shi ne ya sa na samu damar jagorantar wannan kungiya wadda take da rassa a kasa baki daya. A matsayinmu na matasa mukan tsaya mu lura da cewa wanene yake tare da mu har yake damuwa da irin halin da muke ciki? Sai muka lura da cewa, a wannan iskan mai bugawa Sanata Kwankwaso ne mutumin da ya damu da mu. Shi ya sa muka yanke shawarar yin wannan kungiya. Sanata Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso sai dai kin gaskiya, amma kowa ya san cewa shi mutun ne wanda yake kula da mutane, musamman ma matasa. Ba wai ka dauki kudi ka ba matashi shi ne taimako ba, bashi abin da zai nemi kudin ko tallafa masa in ya shiga yanayi shi ne taimako.
Amma wasu na ganin ta siyasa ce duk cewa ga irin ayyukan da kuke yi?
Ba zance siyasa bace, kamar yadda ba zan cire ta daga sauran kungiyoyi na sa kai ba. Sannan kowa ya sani cewa irin jam’iyyar da shi Kwankwaso yake cikinta, amma abin da zai baka mamaki shi ne babu ruwanta da bambancin jam’iyya ko irin jam’iyar da danta yake ciki. Ina tabbatar maka da cewa, kowane irin dan jam’iyya akwai cikin kungiyar Kwankwasiya Amana mai amfani da jar hula ga maza, ko jan kallabi ga mata. Wannan kuma ba alamar wata jam’iyya bace, alama ce ta sanin dan kungiya wanda aka yi mata rajista kamar sauran kungiyoyi.
Baka ganin za ace baka yi daidai ba rungumar wannan kungiya a jihar Shugaban kasa Buhari?
An zo wajen. To bari kaji wani abin da mafi yawan mutane masu irin wannan tunanin basu sani ba. Shin idan ance Shugaba Buhari dan Jihar Katsina ne, kuma shike shugabancin kasa a yanzu, mu kalli abin a siyasance wanda kuma rashin daukar irin wannan matakin na tunda wuri ya rika cutar da mu a nan Arewa. Tunda har munga irin yadda Shugaba Buhari yake tafiyar da mulkinsa wanda kuma mun gamsu a kan haka, shin ashe bai kamata tunda wuri mu fara tunanin wanda muke ganin zai iya maye gurbin Buhari a lokacin da baya nan ba? Ko sai lokutansa sun kare sannan mu zo muna lalube a cikin duhu? Idan ma har in an kalli wannan kungiyar a siyasance. Kaga kowace irin jam’iya kake tunani akwai mutanan ta a cikin wannan kungiya, kaga ke nan tun yanzu mun fara tunani da kuma kama hanyar da muke ganin za ta taimakemu, ba wai sai lokaci ya kure ba azo a nufo mu da kudi ba a mana sakiyar da babu ruwa.
To a karshe menene fatanka ga wannan kungiya?
To babbar fata nan a nan shi ne, jama’a musamman ‘yan Arewa matasa su gane masu son cigabansu da kuma kokarin kai wannan kasa ga matsayar da kowa ke bukata. Sannan jama’a su gane kungiyar Kwankwasiya ba ta tsaya ga harkokin siyasa ba ne kadai ba, kamar yadda shi Dokta Kwankwaso bai tsaya a nan bangaren ba, mu fito mu bayar da duk wata gudunmuwar da ta dace. Mu kuma tsaya mu yi nazari ga kowane irin dan takarar da ya fito neman goyon bayanmu kafin mu bashi kuri’armu. Ba wai cewa muka yi idan anyi zabe a sakawa wannan kungiya da bata wata kwangila ba, a’a, a saka mata ta hanyar ciyar da matasanmu gaba domin su yi dogaro da kansu.