Azancin azargagiyar amawali

Azancin amawali Azargagiyar takunkumin hankali Alamta alamun mulkin asali A daidaita komai yai fasali Ai sasancin sassaucin daga kansakali   Sukuwar ingarma kan akawali Ranar ruguntsimin idar da idi  ai tozali Jan linzami sai mai sunkutar sumbuli Mahaya masu kwalkwali Jan daga jiran jidali   Fuffukar fafatawar falali Jagaliyar jimurdar jangali Faske-fasken falle falalen fili […]

Azancin azargagiyar amawali

Azancin amawali

Azargagiyar takunkumin hankali

Alamta alamun mulkin asali

A daidaita komai yai fasali

Ai sasancin sassaucin daga kansakali

 

Sukuwar ingarma kan akawali

Ranar ruguntsimin idar da idi  ai tozali

Jan linzami sai mai sunkutar sumbuli

Mahaya masu kwalkwali

Jan daga jiran jidali

 

Fuffukar fafatawar falali

Jagaliyar jimurdar jangali

Faske-fasken falle falalen fili

Felken fifita fadan fi’ili

Kugin kulalen kundumemen kulli

 

Surutu marar misali

Kowa ya kwashi kudi yai shagali

Sanin cewa ba hali

Alhali

Babu haraji da jangali

 

Akwakun aku kuturu

Cakwaikwaiwa ta ki yin shiru

Sai aka zarga mata turu

Gundumi yai mata zuru

A gandun gunduma aka gwaru

 

Sai sansanin sa-in-sa

Sunkurun siyasa

Sake-sake saisa-saisa

Sulalewar sulallan salansa

Sai sussukar soshe-soshen susa

 

Murkusun murabus

Kulle-kullen kus-kus

Karshen karashe kiris

Alayen alkakin algaragis

Cika-cikin cin cukubus

 

Dagin dangar Dabo

Kwakwazo kwabo-da-kwabo

Kwaramniyar kwazazzabo

Tataburzar tarairayar tabo

Zage-zagen zilliyar zabarin zabo

 

Mai martaba Masanin Sisi-da-sisi

Salonsa saisaita sulallan sisi

Kwakwazon kwafsi

Aika-aikar asassa asarar asasi

Wa-ka-ci-ka-tashin wasi-wasi

 

Gwamna gwarangwam

Gular guduma gum

Garkame gambu gararam

Gaba-da-gaba gam-gam

Gundumin gundumar gardama gingim

 

Mutanen fada

Ku ke rike kambin mulki

Babban mutum yai kirki

Kun san magada

Masu gada-gada

 

Sunkurun sasarin sarauta

Gargajiyar gawurta

Ga garajen gajarta

Gantsare-gantsaren gata

Sauke-sauken sukurkucewar shammata

 

Masoya

Masu musaya

Mafadatan motsa murya

Makaryata na ta buya

Munafukan buruntun kurya

 

Al’umma

An yi rashin makama

An zo ana ta fama

Rigingimun jan ragama

Rudanin rikici ya girmama

 

An karke da tsigau

Ga gaggabar gadarar Gogau

Rangajin rayuwar Rawayau

Kambin kariyar Kumayau

Jimamin jimirin Jimirau

 

Akwai rashin azanci

Butu-butun babatun batanci

Sakacin sakatar sakarci

Iskokan iskar iskanci

Solobiyon sulutun sokwanci

 

Mutanen birni da  kauye

’Ya’ya da iyaye

’Yan dugwi-dugwi da dan nagoye

Har ma da ’yan tagwaye

A bar batun waye-waye

 

A daina ce-ce-ku-ce

Ko tashe-tashen zance

Nadin mai sarauta an mance

Kone-konen kuntatacce

Ga tsigau ta sa an birkice

 

A makon da ya rare a gurguje, an yi ta ce-ce-ku-ce kan tataburzar turka-turkar taho-mu-gamar tunkude Mai martaba Masanin Sisi-da-sisi daga kan karagar mulkin birnin Dabo inda ba a dabo. Lamarin larurar lakume kambin mulki daga hannun Masanin motsin matsabban sulai da sisi ya auku ne sanadiyyar ja-in-jar jimurdar jayayyar da mai kambin sarautar birnin Dabo ya yi wa Gwamna gwarangwam Gundumin gandun gula gundumar aikin al’umma, shi kuwa ya yi lamo, wai Malam lamma ya yi lamo, amma yayin da ya yunkuro ya tunkari mai rawanin na-zomo, sai aka fasko cewa, ‘ba fa zai lamunta ba.’ Don haka dai karshen majigin magagin mamungar manyan mutane ta sauke babban mutum mai rawani da ke kan karagar jan ragamar al’ummar birni da kewayen birnin Dabo.

 

Laifin mai kambin mulki dai bai wuce, rashin fasko azancin azargagiyar amawalin tattakin takun takunkumin haihata-haihatar hattarar hankali da ke alamta alamun mamakon mulkin asasin asali wajen daidaiton komai-da-komai da  fasali, ta yadda za a samu sassaucin sasanta dirkaniyar daga karafkiyar kafta kansakali. Kodayake Mai martaba Masanin Sisi-da-sisi ya sha yin sukuwar ingarma kan akawali, musamman a ranakun ruguntsimin idar da idi jama’a jingim su yi taron tozalin baje na-mujiyar kallo.

 

Jan linzamin mai sunkutar sambalelen solsalin kayatawar kawar kawanyar rinannen rawani. Ga mahaya masu kawalniyar kwalkwalin koli-kolin jan dagar dogewar jiran jidali.

 

Daga bisani aka zo aka karke da fuffukar fafatawar falalin Jagaliyar jimurdar janjanin jangalin faske-fasken falle falalen filin felken fifita fadan fi’ilin kugin kulalen kundumemen kullin kulla-kullar kyale-kyalen kyalli-kyalli.

 

Shi kuwa uban al’umma sai ya yi ta surutu rututu marar misali, wai ba ya son ganin kowa ya kwashi kudin shagali, a tsakanin mai hali da marar hali, alhali ba a karbar haraji da jangali. Haka dai Mai martaba ya shige akwakun aku kuturu, inda ya yi ta carin caccakar cakwaikwaiwa ya ki yin shiru, har ya yi azarbabiyar afka wa azargagiyar tururuwar turun tunkarar garnakakin gundumi, shi kuwa ya yi masa zuru, har ta kai ga an yi gwagwagwar gwaramar gwaruwar gadarar gandun gunduma a  sansanin sa-in-sar sasarin sarke-sarken sunkurun siyasar sulalewar sulallan salansar sussukar soshe-soshen susa.

 

Da aka samu wani dan tsaikon tashirtawa, sai Gwamna gwarangwam ya kirkiri masarautun gamayyar Gayya-gayya da Kare-kare da Rinin-ranin-raunin-runo da Bini-binin bin-cici, in an hada da Daben dangar dagin Dabo, masu rike da kambin rikon ragamar al’umma kan turbar tafarkin gangariyar gadon gargajiya adadinsu ya kai babban lauje.

 

Karshen majigin mahangar Mai martaba Masanin Sisi-da-sisi dai ya tado da murkusun muku-mukun murabus a kulle-kullen kus-kus, inda aka zo ana ta alayen alkinta alkakin algaragis, kuma aka karke da cika-cikin cin cukubus. Shi ke nan aka haifar da dumuiniyar dungurar dagin daben dangar Dabo, tare da kwakwazo kwabo-da-kwabo a kwaramniyar kwazazzabon tataburzar tarairayar tabon zage-zagen zilliyar zabarin zabo.

 

Daukacin wadannan al’amura da aka tsuwurwurta na tada jijiyar juwa-juwar jigata waiwayen wuyar watayawar wuya, hakika ba su da dadin ji da gani, amma dai ya kamata a lalubo bakin azargagiyar zarge zare, ta yadda za a iya warware turnukun tarnakin tufka, tare da saurin shawo kan irin wannan turka-turkar tabargaza in ta taso nan gaba. A farfajiyar wannan makaranta ta Dodorido a kan shorido, an sha yin tsokale-tsokalen tsokaci kan yadda MAI MARTABA MASANIN SISI-DA-SISI YA WANCAKALAR DA AMAWALIN MALAM MAWALI. Bisa la’akari da irin ta’adar babban mutum mai rawani na birnin Dabo da aka sauke shi daga karaga, muna iya yanke cewa alamu sun nuna duk wanda ya kwata irin wannan ta’ada da wuya a wanye sumul kalau. Saboda haka wajibi ne a zaman zamaninmu masu rike da kambin gangariyar gadon gargajiya, lallai su kasance masu faskekiyar fahimtar fasko AZANCIN AZARGAGIYAR AMAWALI.

 

Shi kuwa gwamna gwarangwam ya sani ba a yanke hukunci cikin gaugawar garaje, sai an bi matakai na DOKAR DAKATARWAR JIMIRIN JURIYA, ta yadda idan LAFTUN LUGUDEN LADAFTARWA bai yi tasirin tarbiyantarwa ba, ai sai a yi mai yiwuwa, amma ba mai gaba gadi ba. Domin irin wannan aika-aikar ta tunzuro tabe-taben tabon da masu mulki ke da shi. Ni dai ba na son shiga sharo ba nagge da karsana da bujimi. Mai martaba dai an ce ya rankaya Jihar Lallaga sisi, babban birnin su Lasisi, inda ake lallaga lagen lasisin lakume sisi.

 

’Yan ba-ni-na-iya, ahir dinku da tafka muhawara kan makomar masu mulki, domin idan aka kyale su, su za su wancakalar da kansu; ko kuma su yunkura wajen saisaita rayuwar al’umma, don tabbatar da lullumin lumana.

 

Haurobiyawa, mu yasar da kisisinar kissar kisan kishiya. Ban da kishin kassara kasa. Kishiyar kirki ta tarbiyantu da ta’adar karsashin kanbama kasaitar kasa.

 

’Yan makaranta mu himmatu ka’in da na’in wajen leke-leken laluben luguiguita mafitar murkushe makakin mikin duddufniyar dawuwurin dogewar dagar kawanyar kwakwar kadondoniyar muku-mukun musifun dundumin damuwar dumuiniyar duniya. Ga dai KWARKWARON KURNAR KYAURON-BORIS, cumuimiyar cutar da ta share fagen fama SASARIN SUNKURUN SANSANIN SINAWA, tare da farfadiyar faduwar gingimemeyar gangar tatsar titsiye tunkuza a kaso-kason kakarin kassara kasuwancin dungun doron duniya, inda aka ci kasa wasa-wasan wuntsila-gudi-gudin wuntsilawa warwas!

 

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos