Azumi (1)
A yau ina so mu soma bincike kadan a kan Azuma irin na masu bin Yesu Kiristi. Azumi yana da muhimmanci sosai a cikin rayuwar kowane mai bin Yesu Kiristi. Babu yadda mai bi zai iya rayuwa cikakke idan bai san asirin samun ikon rayuwa da ke cikin yin azumi ba. Za mu dubi abubuwa […]
A yau ina so mu soma bincike kadan a kan Azuma irin na masu bin Yesu Kiristi. Azumi yana da muhimmanci sosai a cikin rayuwar kowane mai bin Yesu Kiristi. Babu yadda mai bi zai iya rayuwa cikakke idan bai san asirin samun ikon rayuwa da ke cikin yin azumi ba. Za mu dubi abubuwa kima domin mu iya shirya kanmu yayin da za mu shiga yin azumi. Idan mun saba yin azumi, za mu gan cewa akwai wani abin da mai yin azumi zai iya yi a sauwake fiye da wanda ba ya da lokacin yin azumi; ga wanda ke yin azumi, ikon da zai zama da shi musamman bisa ikon Iblis zai fi na wanda ba ya da lokacin yin azumi, ko da yake shi ma mai bin Yesu Kiristi ne. Babu kayadajjen lokaci na yin azumi; ya danganta ne ga yadda mutum ya yi shiri tsakaninsa da Allah. Zai iya zama na kwana daya kawai ba ci ba sha, ko kwana biyu; ko kwana uku ko fiye da haka.
Za mu bincika shi sosai a gaba cikin nazarin da muke yi. Yayin da za mu yi magana a kan yaya za mu dauki azumi, tsawon kwanakin da ya kamata mu dauka domin yin azumi da makamantansu, za mu yi cikakken bayani domin mu sami ganewa sosai. Dukan masu bada gaskiya ga Allah, sun gane muhimmancin yin azumi tun ma idan ya zo ga yi ibada ga Allah.
“Tada murya, kada ka saukaka; daukaka muryarka kamar kaho, ka shaida wa jama’ata laifinsu, gidan Yakub kuma zunubansu. Lallai kuwa suna nemana kowace rana, murnarsu ne su san tafarkunsa; sai ka ce al’umma mai yin adalci ne, wadda ba ta rabuwa da shari’ar Allahnsu ba, sukan roka a gare ni shika-shikai na adalci; suna murna su guso wurin Allah. Don mene ne mun yi azumi, inji su, kai kuwa ba ka duba ba? Don mene ne mun wulakanta ranmu, ba ka kuwa lura ba? Ga shi, a ranar naku na azumi kuna samun naku annashuwa, kuna matsa dukan ma’aikatanku. Ga shi domin husuma da fada kuke azumi, domin ku yi naushi da hannun mugunta; ba ku yi azumi yanzu ba, yadda za a sa muryarku ta jiwu a sama. Ko shi ne irin azumi da na zaba? Ranar da mutum zai wahalar da ransa? A sunkuyar da kansa kamar iwa, a shimfide tsummoki da toka a karkashinsa? Za ka ce da wannan azumi ke nan, rana abin karba ga Ubangiji? Ko ba shi ne irin azumin da na zaba ba? A kwance sarkoki na mugunta, a babballe madamra na karkiya, a saki wulakantattu, ku karya dukan karkiya? Ko ba shi ba ne, a rarraba abincinka ga mayunwata, fakirai da an yar da su ka kawo su cikin gidanka? Sa’adda ka ga matsiraici, ka yi masa sutura; ba ka buya ga ’yan uwanka ba? Sa’annan haskenka zai bullo kamar wayewar gari, warkewarka kuma za ta zabura da sauri; adalcinka kuma zai ci a gabanka: darajar Ubangiji kuma za ta zama kariyar bayanka. Sa’annan za ka kira, Ubangiji kuwa zai amsa; za ka tada murya, shi kuwa zai ce ga ni. Idan ka kawar da karkiya daga cikinka, da nuna yatsa, da yin maganar mugunta; idan ba ka mayunwata marmarin ranka, ka kosar da mutum wanda ransa ya sha wuya; sa’annan haskenka zai fito cikin duhu, duhunka kuma zai zama kamar tsakiyar rana: Ubangiji kuma zai ja maka hanya tutur, ya kosar da da ranka a cikin kekasassun wurare, ya karfafa kasusuwanka: za ka zama kamar lambu wanda an yi masa ban ruwa, kamar mabubular ruwa kuma, wadda ruwayenta ba su sarewa ba. Wadanda suke naka kuma za su gina kangaye na da: za su sake ginin gindaye na tsararaki da yawa; za a ce da kai mai gyaran kufai, Mai mayar da tafarkun da za a zamna a ciki. Idan an kawar da kafa ga barin aikin garalin kanka a ranar asabbar, ranata mai tsarki; ka kuma ce da asabbar, abin marmari ne; mai tsarki na Ubangiji; abin girmamawa; idan kuwa ka girmama ta, ba ka aika sha’anin kanka ba, ba ka bidi naka nashatsi ba, ba ka kuwa fadi zancen kanka ba: sa’annan za ka faranta zuciyarka cikin Ubangiji; ni kuwa zan sa ka hau bisa madaukakan wurare na duniya; zan yi kiwonka da gadon ubanka Yakub kuma; gama bakin Ubangiji ne ya furta.” (Ishaya: 58: 1 – 14)
“Kuma lokacin da kuke yin azumi, kada ku kwansare fuskarku, kamar yadda masu riya ke yi; gama suna bata fuskokinsu, domin mutane su gane suna azumi. Gaskiya nake ce maku, sun rigaya sun karbi ladarsu. Amma kai lokacin da kake yin azumi, shafe kanka da mai, ka wanke fuskarka, domin kada ka bayyana ga mutane kana azumi, sai Ubanka da ke cikin boye ya gani: Ubanka da ke gani daga cikin boye kuwa za ya saka maka.”( Matta: 6:16 – 18).
Tambaya ta farko da za mu yi ita ce, mene ne azumi irin na Kirista?
A takaice, azumi ita ce lokacin da mutum ya kebe kansa daga cin abinci domin yin ibada. Wato lokaci ne da mutum ya yarda ya rufe bakinsa daga ciye-ciye. Lokaci ne kuma na neman nufin Allah game da abin da ya sa muka ma soma wannan azumin. Azumi ba zai taba zama cikakke ba in ba tare da addu’a suka tafi ba. Lokacin azumi; lokacin addu’a ne. Dukan azumin da mai bi zai yi ba tare da yin addu’a ba; yunwa ne kawai ya ji; watakila yana son ya rage jiki (kiba) ne kawai, amma ba ibada ba ne. Za mu iya kasa azumi a kashi biyu; na farko: Azumin da Mai bin Yesu zai yi ba tare da ci ko sha ba kwata-kwata. Irin wannan ba ta wuce kwana uku da garaje, akwai mutane kima da Allah Ya yi masu magana su yi azumi ba tare da ci ko sha ba na tsawon kwanaki arba’in. Misali Annabi Musa: shi bisa ga umurnin Allah ya yi kwanaki arba’in a bisa dutse a gaban Allah. Amma irin wannan umurni ba ga kowa ba ne; kwanakin da jinkin mutum zai iya jimrewa ba tare da ci ko sha ba – shi ne na kwana uku. Akwai kuma azumin da an saba yi wanda babu cin abinci sai dai shan ruwa kawai, ba kunun zaki ko surki ba, na duk tsawon azumin. Akwai kuma wanda mutum zai iya yi; wato babu cin abincin da ka saba ci, ko kuwa kyale wasu nau’o’in abinci, kana cin mai yiwuwa ’ya’yan itatuwa amma ba abinci ba. Za mu yi karin bayani a kansu idan Allah Ya yarda. Kada mu manta da cewa son cin abinci ne ya kawo wahala bisa dukan duniya.