Azumi (10)

Amfanin azumi A makon da ya shige, mun soma koyarwa ne a kan amfanin yin azumi, muka kuma soma bincike a kan yadda hasken mu za ya bullo kamar wayewar gari; babu wata irin wahala wadda ta zama kamar duhu mai tsanani a kan mutum, wadda Allah ba zai iya kawar da ita ba, daya […]

Azumi (10)
Azumi (10)

Amfanin azumi

A makon da ya shige, mun soma koyarwa ne a kan amfanin yin azumi, muka kuma soma bincike a kan yadda hasken mu za ya bullo kamar wayewar gari; babu wata irin wahala wadda ta zama kamar duhu mai tsanani a kan mutum, wadda Allah ba zai iya kawar da ita ba, daya daga cikin hanyoyin da za mu iya samun tagomashin Allah, ita ce yin Azumi. Abin takaici guda shi ne masu Bi da dama ba su dauki azumi abu mai muhimmanci a cikin rayuwar su ba. Irin wadannan mutane sun dade cikin wahala wadda suke fuskanta. Ina so mu ci gaba yau da nazari a kan amfanin yin azumi.
WARKEWAR KA KUMA ZA TA ZABURA DA SAMRI:-A Littafin Ishaya 58 : 8 inda muke nazari a kai yanzu, maganar Allah na cewa “ Sa’annan hasken za ya bullo kamar wayewar gari, warkewar ka muna za ta zabura da samri; adilcin ka kuma za ya ci gaban ka: darajar Ubangiji kuma za ta zama kariyar bayanka” Idan ka ji ana maganar warkewa a wuri, to ka sani ana zancen wani wadda ba shi da lafiya ne; ba za ka ji ana irin wannan zance ba idan babu ciwo: abu na biye kuma shi ne; mutane suna fama da cutattuka daban-daban, wadansu su na fama da cuta ta jiki, suna kan jinya, mai yiwuwa sun je asibiti likita ya ba su magani suna kan sha, domin su ji sauki, suna fama da yin jinya, wadansu kuwa nasu na ruhu ne, misali masu fama da aikin zunubi, duk inda ka ga wani yana cikin gaba da aikata zunubi, shi ma yana fama ne da rashin lafiya, zunubi cuta ne, ko ma wane irin zunubi ne. duk cuta za ta iya kai ga mutuwa, ko na jiki, ko kuwa na ruhu. Allah cikin alherinsa ya sa cewa ta wurin bangaskiya za mu iya neman fuskarsa cikin kwanakin yin azumi, a hakan nan kuma za mu samu warkarwa. Akwai shaida da dama na mutane wadanda Allah cikin alherinsa ya warkar dacutattukansu bayan sun dauki tsawon kwanaki na yin azumi da addu’a. cuta wadda ta fi kisa ita ce cutar zunubi. Maganar Allah na koya mana da cewa ‘gama hakkin zunubi mutuwa ne, amma kyautar Allah rai na har abada ne; akwai mutane da dama wadanda suka ce sun karbi Yesu Kristi a matsayin Mai ceto daga bautar shaitan da zunubi, amma har yanzu suna fama da aikata zunubi, sun gagara tsamo kansu daga cikin irin wannan bautar; hanya guda wadda za ta yi taimako ita ce mu kawo kanmu cikin azumi da addu’a da kaskancin kai, Allah kuma cikin jinkansa zai taimake mu cin nasara. Mai yiwuwa kai ma haka ne, kana ta fama da ciwo ko kuwa aikin zunubi; kuma ba ka san yadda za ka yi da wannan jaraba ba, bari in baka shawara, ka dauki kwanaki na addu’a da azumi; ka kaskantar da kanka gaban Ubangiji Allah, ka roke shi ya taimake ka, za ka ga abin da zai faru. Rayuwarka za ta canza, sunan Allah kuma ya samu daukaka.
Za ka kira, Ubangiji kuwa za ya amsa: sau da dama na kan yi tunani game da yin Addu’a, kamar yadda muka sani a cikin Littafi Mai Tsarki, cewa Allah ya igaya ya yi alkawari ga dukan masu binsa cewa, dukan abin da muka roka, shi Ubangiji Allah zai ji, kuma amsa addu’ar mu, amma idan mutane za su fadi gaskiya, amsoshin nawa ka samu a cikin dukan rokon Allahn da ka yi? Watakila kima ne kawai; tambayar ita cee mene ne ya sa haka? Sai mu tuna fa, Ubangiji Allah bai gaji da jin addu’a ba, shi mai iko duka ne; babu abin da ya fi karfinsa ko kadan, kuma shi Allah ba ya yaudara kamar shaidan ko mutum, kowane mutum wanda ya dogara ga Allah yana so ya ga cewa duk lokacin da ya rusuna a gaban Allah cikin addu’a, ya ga cewa abin da ya rokan nan ya samu, sai ya yi farin ciki ya na godiya. Sai mu lura; duk lokacin da ka yi addu’a sai ka ji shiru daga wurin Allah, ba ka amsa ba- sai ka tuna da abin da maganar Allah ta ce cikin Littafin Ishaya 59 : 1 – 4; wadda take cewa, “Duba, Hannun Ubangiji ba ya yi gajarta ba, har da ba ya iya ceto ba; Kunnensa kuwa ba ya yi nauyi ba, har da ba za ya iya ji ba, amma laifukanku sun raba tsakaninku da Allahn ku, zunubanku kuma sun rufe muku fuskatasa, da ba za ya ji ba, Gama hanuwanku sun kazantu da jini, yatsunku kuma da laifi, lebbanka sun yi karya, harshenku ya na rada mugunta. Babu wanda ya ke kai kara cikin Adilci, ba kwa mai da’awatasa da gaskiya: suna dogara ga aikin banza, suna fadin karya, su kan dauki ciki da keta, su haifi zamba”. Maganar Allah na cewa ‘addu’ar mai zunubi, abin kyama ne a gaban Allah, Shi Allah Mai tsarki ne, idanunsa ba sa kallon kazamta musamman ma na zuciya, wadda ita ce ke sa gaba tsakanin Allah da mutum, amma duk lokacin da mutum ya gane kuskuren sa ya tuba ya nemi gafara daga wajen Ubangiji Allah, Allah mai jinkai ne zai gafarta maka, ya wanke sarai, to a daidai wannan lokaci idan ka kebe kanka cikin azumi, kana rokon Allah, maganarsa ta ce “sa’annan za ka kira, Ubangiji kwa za ya amsa, za ka tada murya, shi kwa za ya ce, Ga ni, idan ka kawas da karkiya daga cikin ka, da nuna yatsa, da yin maganar mugunta.” Yin addu’a yana da kyau, amma dole ne ya fito daga zuciya mai tsarki, mai tsoron Allah kuma. Yin azumi ya kan jawo hankalin mu zuwa wurin Ubangiji Allah, ta kan sa mu natsu, mu yi tunani a kan maganar Allah, mu iya gane kowace irin tafiya muke yi da Allah, inda muka ka yi kuskure kuma Allah zai bayyana mana su duka, sai mu tuba mu ci gaba da tafiya cikin adilci.
Yayin da muke kammala binciken mu na yau, ina so mu dauki lokaci mu yi tunani a kan irin kalubalen da muke fuskanta a wannan kasar mu Najeriya; wannan kasa cike take da wahalhalu iri-iri, kuma idan muka duba a hankali, mutane da yawa suna fama da rokon Allah, amma sai ka ce abin karuwa yake yi, ina so mu binciki kanmu da kanmu, ya ya tafiyarka take a gaban Ubangiji Allah? Idan har zuciyar mutum tana cike da mugunta ko zunubi; babu yadda Allah zai ji mu. Mu yi tunani!! Mu ci gaba da yin addu’a domin wannan kasa ta kasance cikin adalci. Ubangiji Allah ya ci gaba da tsare nasa. Amin.