Azumi (3)
Dalilan yin azumi: Yin azumi yana da kyau sosai, amma idan mutum bai gane dalilin da ake yin azumi ba, Allah ba zai ma kula da abin da yake yi ba balle ya samu albarkar azumin da yake yi. A cikin littafin Ishaya 58:2 – 7, maganar Allah tana koya mana cewa “Lallai kuwa suna […]
Dalilan yin azumi:
Yin azumi yana da kyau sosai, amma idan mutum bai gane dalilin da ake yin azumi ba, Allah ba zai ma kula da abin da yake yi ba balle ya samu albarkar azumin da yake yi. A cikin littafin Ishaya 58:2 – 7, maganar Allah tana koya mana cewa “Lallai kuwa suna nemana kowace rana, murnarsu ne su san tafarkuna; sai ka ce al’umma mai yin adilci ne, wadda ba ta rabuwa da shari’ar Allahnsu ba, sukan roka a gare ni shika-shikai na adilci; suna murna su guso wurin Allah. Don mene ne mun azumi, in ji su, kai kuwa ba ka duba ba? Don mene ne mun wulakanta ranmu, ba ka kuwa lura ba? Ga shi a cikin ranar taku azumi kuna samun naku annishuwa, kuna matsa dukan ma’aikatanku. Ga shi, domin husuma da fada kuke azumi, domin ku yi naushi da hannun mugunta; ba ku yi azumi yanzu ba, yadda za a sa muryarku ta jiwu a sama. Ko shi ne irin azumin da na zaba? Ranar da mutum zai wahalar da kansa? A sunkuyar da kansa kamar iwa, a shimfide tsummoki a karkashinsa? Za ka ce da wannan azumi ke nan, rana abin karba ga Ubangiji? Ko ba shi ne irin azumin da na zaba ba? A kwance sarkoki na mugunta, a babballe madaura na karkiya, a saki wulakantattu, ku karya dukan karkiya? Ko ba shi ba ne a rarraba abincinka ga mayunwata, fakirai da an yada su ka kawo su cikin gidanka? Sa’anda ka ga matsiraici, ka yi masa sutura: ba ka buya ga ’yan uwanka ba?”
Yayin da azumi ke da muhimmanci a cikin rayuwar kowane mai bada gaskiya ga Yesu Kiristi, amma mutum ba zai taba samun albarkar da ke cikinsa ba sai idan ya san cikakken dalilin da ya sa yake yin azumin. Mutane da yawa suna yin azumi ba don komai ba, sai dai domin su yi fahariya cewa ai su ma suna yin azumi na kwana kaza da kaza; ga wadansu mutane kuwa; sai ka sa ido sosai kafin ka iya gane manufarsu; a inda muka yi karatu yanzu, idan muka duba a hankali; sai ka yi tsammani kamar wadannan mutane suna da shauki cikin zuciyarsu na neman nufin Allah a cikin rayuwarsu ta yau da kullum, idan ka gan su za ka yi tsammani da gaske ne suke yin azumin, amma a aya ta biyu sai muka ga ainihin abin da ke cikin rayuwarsu wanda Allah ne kadai ke gani “….sai ka ce al’umma mai yin adilci ne wanda ba su rabuwa da shari’ar Allahnsu…..suna murna su guso wurin Allah:” abin lura a nan shi ne, kodayake za mu iya boye wa mutum abin da ke cikin zuciyarmu, amma a gaban Allah, babu abin da ke a boye, komai a sarari ne a gare Shi. Mutane sun saba da rudin jama’a a kullum: yawancin lokaci mutane da yawa suna so ne su nuna wa sauran jama’a kamar su ne masu son ibada, kamar da gaske suna tsoron Allah, amma gaskiyar ita ce cikinsu fanko ne kawai.
Abin lura daga farko shi ne, azumi, dole ne ya zam bisa ga nufin Allah, wato mu bari Allah da kansa ta wurin ikon Ruhu Mai tsarki ya bishe mu zuwa daukar azumi. Mu bar shi ya sa a cikin tunaninmu, ba wai ganin damarmu ba ne, haka nan azuminmu zai zama abin karba ga Allah, akwai wata tambaya da almajiran Yohanna mai Baptisma suka yi wa Yesu Kiristi a cikin Littafin Matta 9:14 – 15 wadda ta ce “Sa’annan almajiran Yohanna suka zo gare shi, suka ce, Don mene ne mu da Farisawa mukan yi azumi da yawa, amma almajiranka ba sukan yi azumi ba? Yesu ya ce masu, Ya yiwu ’ya’yan dakin amarya su yi bakin ciki muddar ango yana tare da su? Amma kwanaki za su zo inda za a dauke masu ango, sa’annan za su yi azumi.”
Ina so mu duba a hankali wannan sashin Littafi Mai tsarki da muka karanta; a wurin mun ga cewa almajiran Yohanna sukan yi azumi sosai; haka Farisawa, sukan yi azumi sau biyu a mako suka yi tsammani almajiran Yesu Kiristi su ma ya kamata su yi azumi amma ba su taba ganinsu suna yi azumi ba ko a fili ko a boye. Ubangiji Yesu Kiristi bai ce masu sun yi kuskure da wannan tambaya ba; amma ya ce musu lokaci ne kawai ake jira; akwai lokacin da ba sai an gaya masu ba za su yi azumi. Yayin da Yesu Kiristi yana duniya tare da masu binsa, ba su da dalilin yin azumi; haka kuma lokacin da Yesu Kiristi ya dawo domin masu binsa a nan duniya, a lokacin ba mu da bukatar yin azumi kuma. Amma tsakanin zuwansa na farko wanda ya mika kansa a matsayin dan rago na Allah, ya bada kansa hadaya domin ya ceci mutum daga bautar zunubi, wato tsakanin mutuwarsa bisa gicicye da tashinsa daga kabari har zuwa hawansa zuwa cikin sama da kuma lokacin da zai dawo domin masu binsa na gaskiya, wannan rata da ke tsakanin tafiyarsa zuwa sama da kuma dawowarsa cikin wannan duniya a lokacin ne Yesu Kiristi ya ce masu binsa za su yi azumi. Wato a wannan zamanin ekklesiya.
Lokacin azumi lokacin ibada ne kwarai da gaske; a cikin Littafin Ishaya: 58 inda muka yi karatu a baya; za mu gani cewa azumi akan yi shi domin dalilai kamar haka:
“…a kwance sarkoki na mugunta:” Ma’anar wannan wuri ita ce; idan kana nuna iko da bai dace a bisa talakawa, kana dora masu nauyi da bai kamata ba sai ka daina, idan kana nuna musu iko da bai dace da shari’ar Allah ba, sai ka daina yi. Lokacin azumi lokacin tunani ne game da irin abin da muke yi ko kuwa muke sa wadansu su yi koda bai dace da maganar Allah ba. Ko da mutumin bawa ne, ya dace ne mu yi masa adilci cikin dukan komai. Sarkokin mugunta su ne abubuwan da mukan yi amfani da su mu daure wani; ko ta wurin bada umurni domin muna da ikon yin haka, ko ta wurin kuntatawa wasu domin muna da ’yancin yin haka. Sai mu lura, duk lokacin da mutum ya kudurta cikin zuciyarsa zai yi azumi kada ya yi tsammani Ubangiji zai ji shi ba tare da canja hali ba.
“…a babbale madaura na karkiya:” a cikin littafin Zabura 105:17 – 20, maganar Allah na cewa “ya aiki wani mutum a gabansu, Aka sayar da Yusufu ya zama bawa: Suka raunata kafafunsa da mari, Aka sa shi a cikin bakin karfe, Har lokacin da maganatasa ta cika; Maganar Ubangiji ta inna ce shi. Sarki ya aike a kwance shi wato mai mulkin dangogi, ya fa sake shi. Sai mu tuna cewa Iblis a koyaushe yakan so ya daure mutane da halayensa da ayyukansa. Azumi, lokaci ne na babbale irin wadannan madaurin.
Za mu ci gaba daga nan mako mai zuwa idan Allah Ya bar cikin masu rai. Ubangiji Ya taimake mu, amin.