Azumi (5)
A wannan mako za mu ci gaba da koyarwan a kan dalilan yin azumi kafi mu ci gaba da duba irin albarkokin da ke cikin yin azumi. A cikin Littafin Ishaya 58: 6 – 7 maganar Allah tana koya mana cewa: “ ….ko ba shi ne irin azumin da na zaba ba? A kwance sarkoki […]
A wannan mako za mu ci gaba da koyarwan a kan dalilan yin azumi kafi mu ci gaba da duba irin albarkokin da ke cikin yin azumi.
A cikin Littafin Ishaya 58: 6 – 7 maganar Allah tana koya mana cewa: “ ….ko ba shi ne irin azumin da na zaba ba? A kwance sarkoki na mugunta, a babballe madaurai na karkiya, a saki wulakantattu, ku karya dukan karkiya, ko ba shi ba ne, a rarraba abincinka ga mayunwata, fakirai da an yar da su ka kawo su cikin gidanka? Sa’adda ka ga matsiraici, ka yi masa sutura, ba ka buya ga ’yan uwanka ba?” A kan wannan binciken ne muke kuma za mu ci gaba.
…A babballe madaurai na karkiya:- Mene ne karkiya? Idan mutum manomi ne a Arewa, ya san abin da ake nufi da karkiya, ita dai karkiya, ita ce ce wadda ake dora ta bisa wuyan shanu biyu a daure ta sosai da igiya wadda aka sa daga hancin shanun; a ja garma da ita domin huda ko jan amalanke. Domin daurin karkiyan nan, babu yadda wadannan shanu za su rabu, dole ne su yi tafiya tare da juna, muddin ba a balle madauran ba. Ina so ne mu gane sarai abin da Iblis magabcin mutum yake yi kullum da ’yan Adam. Gaskiyar ita ce Shaidan ne yake mulki cikin zuciyar mutum wanda bai samu ’yanci ba cikin jinin Yesu Kiristi; a kullum Shaidan yakan yi abin da ya ga dama da su, ba su da ’yanci su yi jayayya da shi, domin ya rigaya ya sa karkiyarsa bisa wuyansu, ba su da ra’ayin kansu kuma. Duk inda Shaidan ya nufa wurin ne za su bi; ba domin suna so su je wurin ko su aikata zunubi ba ne, a’a amma domin akwai karkiyar Shaidan a rataye bisa wuyansu wadda ta sa dole sai sun yi abin da shi yake so su yi. Dalili ke nan da za ka ga mutane da yawa za su yi kudiri cikin zuciyarsu, su ce wa kansu – daga yau ba zan sake wannan abin ba, amma ina; za su ga cewa ba su da ikon rike wannan alkawari: dalilin daya ne kawai, akwai karkiyan Shaidan a bisa zuciyarsu wadda ba za ta ba su izini su iya rike wannan alkawari ba. Tushen cin nasara bisa zunubi ko aikata kowane mugunta shi ne sanin Yesu Kiristi a matsayin Ubangijinmu da kuma mai cetonmu. Yesu ne mai iya ’yantar da kowa wanda ya ba da gaskiya gare shi. Yayin da mutum yana da Yesu cikin zuciyarsa, yin azumi zai sa a koyaushe mu lizima, mu kuma kusato ga Ubangijinmu cikin tunani da duk sauran ayyukanmu. Yin azumi yana daya daga cikin hanyoyin nasara bisa dukan ayyukan Iblis; musamman ma bayan da mutum ya karbi Yesu Kiristi a matsayin Ubangijinsa da kuma mai cetonsa.
….A saki Wulakantattu: Su wane ne wulakantattu? Dukan wadanda ake zaluntarsu. Mutanen da ake danne masu hakkinsu; kuma ba su da ikon yin magana a ji, a koyaushe wadanda suke kansu; su suke yin abin da suka da damu, su danne masu abin da ya kamata nasu ne, Shaidan yana yin wannan sosai, kuma yawancin lokaci yakan yi amfani ne da mutane ya aiwatar da irin wannan zambar; mu dauki misali, a wannan kasa tamu a wannan lokaci na siyasa, azalumai nawa muke da su cikin mulkin gwamnatin wannan kasa? Mutane nawa ne suka fito cewa za su taimaki talakawa idan aka zabe su? Wadansun su lokacin yakin neman zabe za su yi magana har da rantsuwa cewa za su yi kaza da kaza da kaza, da zarar sun samu sun ci, ba za a ma sake ganinsu sai loto-loto, idan suka zo, sai ka ga cewa sun ciro dan kudi kadan su yaudari mutane da shi, amma ainihin hakkin mutane suna dannewa. Wani lokaci mukan yi kuka da su, muna guna-guni, hanya daya ta cin nasara ita ce, mu koma ga Allah cikin addu’a da azumi; mu kai kararsu ga Allah cikin addu’a da azumi, Allah Yana jin addu’a har yau har gobe. Yawancin lokaci mukan dauki damuwa a kanmu ba tare da sanin abin da ya kamata mu yi ba. A wannan kasa tamu Najeriya, na gane cewa mun iya guna-guni a kan abubuwan da suke faruwa da mu, amma abu guda da ba mu iya yi ba, shi ne mu dauki lokaci mu yi addu’a da azumi game da su. Shin wannan wulakancin bai isa ba ne? Kada mu yi tsammanin iyawarmu ko kuwa saninmu, ko dabararmu za su iya kawo mana sassauci cikin irin wahalar da muka iske kanmu a ciki. Yin azumi irin wanda yake gamsar da Ubangiji Allah; shi ne hanyar cire azalumai da masu cin amana.
….ku karya dukan karkiya: Shaidan ba ya da dabara da za ta dauwama, ashe duk sarka da karkiyar da yake amfani da su, za a iya karya su gaba daya: Aikin Allah kadai ke dauwama. Idan Iblis ya takura maka har yanzu, za ka iya fuskantar shi ta wurin ikon Ruhu Mai tsarki da kuma ikon da ke cikin jinin Yesu Kiristi ka rusa dukan ayyukansa cikin rayuwarka. Kada mu ba shi damar yin abin da ya ga dama muna kallo kamar babu abin da za mu iya yi. Mu farka daga barci mu bar yin tagumi kamar marayu; mu yi namu fanni, mu roki Allah cikin azumi da addu’a Allah zai ji kukanmu, Shi ba kamar mutum ba ne, zai amsa mana zai kuma biya mana dukan bukatunmu.
….A rarraba abincika ga mayunwata: Wani lokaci nakan yi mamaki idan na ga wani wai yana azumi, amma sai ka gani yana jiki kawai, akwai irin mutanen nan da yawa, wadanda suna azumi ba don komai ba, sai dai don abinci da kayan kwadayi akwai wadansu wadanda bayan sun yi azumi; misali na kwana daya, za su tattara abin safe da na rana su hada da na daren su cinye duka; wannan ba shi ba ne. Ya kamata ka san cewa akwai wadansu a waje wadanda ba su da abinci, kamata ya yi ka dauki wannan abincin da ba ka ci din nan ba, ka ba su. Su ma su iya gode wa Allah domin alherin da ka yi masu. Ba kawai ka hada komai kamar mai hadama ka cinye kai kadai ba.
Ban san yadda rayuwarka take ba, amma ko ma mene ne, idan akwai matsala cikin rayuwarka wadda ta ki ci ta ki cinyewa; akwai hanya guda da za ka iya gwadawa ka ga ikon Allah. Idan kana da tushen ceto cikin Yesu Kiristi, sai ka dauki azumi da addu’a da muhimmanci sosai.
Mu dauki lokaci a wannan mako mu yi addu’a domin kasarmu Najeriya; kada mu tsaya yin guna-guni kawai, yin guna-guni ba ya kawo canji cikin komai. Allah ne Mai taimako. Ubangiji Allah Ya taimake mu. Amin.