Azumi (6)

Muna ci gaba ne da nazari a kan azumi irin na masu bangaskiya cikin Ubangijinmu Yesu Kiristi. Addinai da yawa suna yin azumi domin dalilai daban-daban, amma ga masu bin Yesu Kiristi, akuwai dalilai da Littafi Mai tsarki ya rigaya ya shimfida mana; idan kuwa azumin da mai bi zai yi ko yana so ya […]

Azumi (6)
Azumi (6)

Muna ci gaba ne da nazari a kan azumi irin na masu bangaskiya cikin Ubangijinmu Yesu Kiristi. Addinai da yawa suna yin azumi domin dalilai daban-daban, amma ga masu bin Yesu Kiristi, akuwai dalilai da Littafi Mai tsarki ya rigaya ya shimfida mana; idan kuwa azumin da mai bi zai yi ko yana so ya yi, ko kuma yana kan yi; muddin azumin da yake yi bai kunshi wadannan dalilai ba, gaskiyar ita ce, duk azumin da ya yi; amfaninsa kadan ne. Sai mu lura yayin da muka yi niyyar za mu yi azumi. A cikin Littafin Ishaya, 58: 7 tana cewa “Ko ba shi ba ne, a rarraba abincinka ga mayunwata, fakirai da an yada su ka kawo su cikin gidanka? Sa’adda ka ga matsiraici, ka yi masa sutura: ba ka buya ga ’yan uwanka ba?” 

Fakirai da an yada su ka kawo su cikin gidanka. Akwai mutane da yawa wadanda suna cikin mawuyacin hali; suna rayuwa cikin talauci, abin mamaki shi ne, kodayake suna da makwabta masu hannu da shuni amma da kyar wani lokaci suke iya samun abinci su ci da iyalansu. Akwai iyalai da dama wadanda ba su da wurin kwana, ko gidajensu idan ka gani ba su bambanta sosai da wadanda suke karkashin rumfa ba; suna nan zube kamar kara, mai yiwuwa kuma kai makwabcin irin wannan mutum ne, mai yiwuwa Allah Ya albarkace ka sosai, amma ko cikin sanyi ko cikin zafi, yanayin irin wadannan matalautan ba ya damunka ko kadan; daya daga cikin dalilan yin azumi da zai samu karbuwa a gaban Allah, shi ne azumin da za ka yi domin matalauta su samu wuri don kansu. Za ka iya hana kanka jin wasu dadin domin ka samu wani abu da za ka kunsa ka taimaki irin wadannan fakiran. Zamanin da muke ciki, cike yake da mutane masu son kansu. Za ka iya yin azumi domin ka roki Ubangiji Allah Ya ba ka kudi domin ka iya taimakon irin wadannan mutane. Akwai wasu kuwa da talaucinsu na Ruhaniya ne, suna nan kamar tumaki ne a daji babu mai kiwonsu. Shaidan yakan so ya sa mutane cikin kunci da kowane irin wahala; idan haka ya ci gaba kuma sai ka ga cewa mutane sun rude sun rasa mene ne za su yi? Irin wannan lokacin ne masu bin Yesu Kiristi su kan samu damar karya ikon Iblis wanda ya sa mutane bauta. Yesu Kiristi ya yi magana a cikin Littafin Matta 9: 36 cewa “Amma sa’anda ya ga taron, ya yi juyayi a kansu, domin suna wahala, suna watse kuma kamar tumakin da ba su da makiyayi.” Dukan masu bada gaskiya ga Yesu Kiristi, sun rigaya sun ci nasara bisa ikon Iblis har abada, Shaidan ba ya da iko a kansu, dalilin kuwa daya ne – Yesu Kiristi ya mutu dominmu, ya kuma ci nasara bisa Shaidan da mutuwa. Masu bi duk suna cin moriyar wannan nasara da Yesu Almasihu ya samu ta wurin mutuwarsa. Duk wanda bai san Yesu Kiristi a matsayin mai cetonsa ba; yana rayuwa ne kamar yadda tumakin da ba su da makiyaya suke yawo, ba za su san inda suke zuwa ba, suna kan tafiya ne kawai sai inda hanyar ta kare. daya daga cikin dalilan yin azumi ke nan; mu iya rokon Allah Ya taimaki dukan batattu su iya zuwa ga samun ceto, kuma babu abin da ya gagari Ubangiji Allah. Da zarar sun karbi Kiristi Yesu a matsayin mai cetonsu, duk ikon Shaidan a kansu ya kare. Sun samu ’yanci daga kuncin Shaidan. Iblis ba zai iya yi da su yadda ya dama ba.
Ka yi wa matsiraici sutura:
Allah zai ji dadin kowane mai ba da gaskiya ga Yesu Kiristi idan ya yi azumi domin wani ya samu sutura, ko kuwa ka ki cin abinci domin ka iya tara kudin ka sayi sutura wa wani wanda ba ya da kayan sawa; ko kuwa ka lura cewa, a duk lokaci kana ganin wani ko wata da kaya daya kawai, babu canji, sai ka ce wa kanka zan roki Allah cikin azumi domin in samu kudin da zan yi amfani da shi in sayi sutura ga wannan mutum ko ga wannan matar, Allah zai ji dadinka sosai. A yau; muna ganin tsiraici ba na fatar jiki ba kawai, amma mafi tausayi wato tsiraici na zuciya ko na ruhu. Mutane da dama suna bayyana tsiraicin nan na ruhu ta wurin irin zunubin da suke aikatawa a fili ba tsoro ba kunya: mai yiwuwa suna so su bar aikata irin wannan zunubi amma ba su da karfin da za su iya ciro kansu daga cikin irin wannan karkiya ko tarkon Shaidan. Idan har za su canja; to, suna bukatar a yi musu addu’a da azumi domin maganar Allah ta ratsa su; haka nan karkiyar da Shaidan ya daura a wuyansu za ta karye su samu ’yancinsu.
Wani lokaci kai da kanka ko ke da kanki za ki bukaci yin azumi domin yawan surutu, irin masu magana da yawa a ko’ina da ko yaushe, ba su da asiri. Idan har ka gane cewa wannan shi ne damuwarka; ka gudu zuwa wurin Allah cikin azumi domin Ya taimake ka. A takaice kana azumi domin ka roki Ubangiji Allah Ya juyo da tunanin masu aikata zunubi zuwa ga aikata adalci.
Neman fuskar Ubangiji Allah domin cikawar alkawarinsa:
A cikin Littafin Daniel 9 : 2 – 3, maganar Allah na cewa “A cikin shekara ta fari ta mulkinsa, ni Daniel ta wurin littattafai na gane lissafin yawan shekaru, wadanda maganar Ubangiji ta ambace su ga Annabi Irmiya, kafin risbewar Urushalima ta cika, shekara saba’in ke nan. Na kuwa kafa fuskata zuwa wajen Ubangiji Allah, domin in yi bida gare shi ta wurin addu’a da roke-roke tare da azumi, da tsummoki da toka….” 20 – 23 “Ina nan ina cikin magana, ina addu’a, ina furta zunubaina da zunubin mutanena Isra’ila, ina kawo godona a gaban Ubangiji Allahna saboda dutse mai tsarki na Allahna; eh, tun ina magana cikin addu’a, sai Jibrailu, wanda na gani cikin ruya tun da fari, da aka sa shi ya tashi da sauri, ya taba ni a wajen sa’ar hadayar yamma. Ya kuma fahimtar da ni, ya yi zance da ni ya ce, Ya Daniel, yanzu na fita domin in ba ka hikimar ganewa. Tun farkon roke-rokenka doka ta fito, yanzu kuma na zo domin in fada maka; gama kai kaunatace ne kwarai; ka lura fa da matsalar, ka gane ruyan,”…Haka nan cikin Littafin Timathawus ta fari sura biyu aya daya zuwa hudu maganar Allah na koya mana cewa “A farkon farawa dai, ina umarni a yi bide-bice da addu’o’i, da roke-roke da godiya, saboda dukan mutane domin sarakuna da dukan wanda ke cikin matsayin manya; domin mu yi ranmu mai natsuwa da hankali kwance cikin dukan ibada da kimtsa fuska, wannan mai kyau ne, abin karba kuwa ga Allah Mai cetonmu; Shi wanda Ya nufi dukan mutane su tsira, kuma su kawo ga sanin gaskiya.”
Za mu yi nazari a kan wadannan ayoyin mako na gaba idan Allah Ya bar mu cikin masu rai.
Kada mu manta; mu ci gaba da yin addu’a domin kasarmu, kuma za mu ci nasara bisa dukan dabarun Shaidan, amin