Azumi (9)
Amfanin yin Azumi Mu sake duba cikin Litaffi Mai tsarki, inda mu ke nazari; Ishaya 58 : 8 – 14 “Sa’annan hasken ka za ya bullo kamar wayewar gari, warkewarka kuma za ya Zaburar da samari, adalchinka kuma za ya ci gabanka: darajar Ubangiji kuma za ta zama kariyar bayanka. Sa’annan za ka kira, Ubangiji […]
Amfanin yin Azumi
Mu sake duba cikin Litaffi Mai tsarki, inda mu ke nazari; Ishaya 58 : 8 – 14 “Sa’annan hasken ka za ya bullo kamar wayewar gari, warkewarka kuma za ya Zaburar da samari, adalchinka kuma za ya ci gabanka: darajar Ubangiji kuma za ta zama kariyar bayanka. Sa’annan za ka kira, Ubangiji kwa za ya amsa, za ka tada murya, shi kwa za ya ce, Ga ni. Idan ka kawar da karkiya daga cikin ka, da nuna yatsa, da yin maganar mugunta. Idan ka ba mayunwata marmarin ranka, ka kosar da mutum wanda ya sha wuya, sa’annan haskenka za ya fito cikin dufu, dufun ka kuma za ya zama kamar tsakiyar rana. Ubangiji kuma za ya ja maka hanya tuttur, ya kosadda a cikin kekasassun wurare, ya karfafa kasusuwanka: za ka zama kamar lambu wanda an yi masa ban ruwa, kamar mabulbulan ruwa kuma, wadda ruwanta ba su sarewa ba. Wanda su ke naka kuma za su gina kangaye na da: za ka sake gina gindaye na tsararaki da yawa, za a ce da kai mai gyaran kufai, mai mayar da tafarkin da za a zauna a ciki. Idan ka kawar da kafa ga barin aikin gararin kanka a ranar Asabar, rana ta mai tsarki; ka kuma ce da Asabar abin marmari ne; mai tsarki na Ubangiji, abin girmamawa; idan kuwa ka girmama ta, baka aikata sha’anin kanka ba, ba ka bidi naka nishadi ba, ba ka kwa fadi zancen kanka ba: sa’annan za ka faranta zuciyar ka cikin Ubangiji; ni kuwa zan sa ka hau bisa madaukakan wurare na duniya; zan yi kiwonka da gadon ubanka Yakub kuma: gama bakin Ubangiji ne ya furta.”.
Ina so ne mu yi nazari sosai a kan wannan sashin Littafi Mai Tsarki, wanda muka karanta. Masu bi da dama ba su san irin hasarar da suke yi ba; domin kawai ba su dauki lokaci sun yi azumi da addu’a ba. Yesu Kiristi ya hau bisa dutse mai tsawo tare da almajiransa guda uku a kadaice, a wurin kamarsa ta sake a gabansu; fuskarsa tana ta haskakawa kamar rana, tufafin sa kuma suka zama farare kamar haske, a lokacin ne kuma wani ya kawo dansa, wanda ya ke da ciwon farfadiya wurin almajiran Yesu Kristidomin su yi masa addu’a ya warke, amma ba su iya warkadda shi ba, bai dade ba sai ga Yesu yana saukowa tare al’majiransa uku; da suka isowujen sauran almajiranda wannan mutum tare da dansa, mutumin ya zo wurinsa, yana durkusa masa yana cewa, “Ubangiji ka yi ma da na jinkai: gama mai farfada ne, yana kwa shan azaba kwarai; gama dayawa ya kan fadi cikin wuta, da yawa kuma cikin ruwa. Kuma na kawo shi wurin almajiranka, amma ba su iya warkar da shi ba. Yesu ya amsa ya ce, ya tsara mara bangaskiya, mai karkacewa, har yaushe zan zauna tare da ku?har yaushe zan jimre da ku? Ku kawo shi daga nan wurina. Yesu ya tsawata masa; aljan fa ya fita daga cikinsa: daga sa’annan fa yaron ya warke.” Ga inda ina so mu sa hankali sosai a kai; matakin da almajiran Yesu Kristi su ka dauka bayan da yaron ya warke: “Sa’annan almajiran suka zo wurin Yesu waje daya, suka ce, Don me mu ba mu iya fitar da shi ba? Ya ce musu, Saboda karantar bangaskiyar ku: gama ina ce muku, Hakika, idan kuna da bangaskiya kwatancin kwayar mustard, sai ku ce wa wannan dutse, ka kawo daga nan ka koma can, sai shi kawu; kuma babu abin da ba zai yiwu gareku ba. amma wannan iri ba shi fita ba sai ta wurin addu’a da azumi” wannan duka za a iya samu a cikin Littafin Matta 17 : 1 – 21.
Yesu Kristi ya yi magana ya ce ‘wannan iri ba shi fita ba sai ta wurin addu’a da azumi’ sai mu lura da cewa; akwai irin wadansu kalubale, ko damuwa, ko bukatu wadanda muke da su kuma muna rokon Allah ya yi mana jinkai ya yaye mana su, ko da shi ke muna addu’a sosai, amma sai muna gani har yanzu damuwar tana nan, almajiran Yesu Kristi ba su karaya ba cikin zuciyarsu, suka zo wurin Yesu dukkansu, suka ce mene ne ya sa ba mu iya warkar da da yaron ba? su na neman asirin da Yesu yake da shi wadda ya sa ya warkar da yaron ba tare da wata wahala ba, Yesu Kristi bai boye musu asirin ba, ya gaya masu cewa, akwai wadansu irin damuwa ko ciwo, ko bukatu wadda ba za ta kawu ba sai tare da addu’a da azumi. Masu bi da yawa suna fama da wahalhalu daban-daban ba domin kamai ba; amma domin rashin yin azumi.Akwai ayyukan al’ajibai masu yawa, wadanda ba za mu taba morarsu ba cikin rayuwar mu; idan ba mu son yin azumi bisa ga tafarkin Allah ba. Mai yiwuwa a yanzu haka kana da damuwa sosai, ka yi ta rokon Allah ya yaye maka shi, amma har yanzu babu abin da ya sake, bari in baka shawara; ka dauki ’yan kwananki domin addu’a tare da azumi, ka sake kawo wannan bukatu gaban Ubangiji Allah, za ka ga tabbaci abin da zai faru. Ka gwada ka gani. Mu zama masu bangaskiya cikin dukkan abin da Yesu Kiristi Ubangijin mu ya fada, haka nan za mu ci nasara. Mu sake komawa cikin Littafin Ishaya 58, inda muke yin wannan koyarwar. Za mu dauki zarafi mu duba a hankali
Sa’annan Hasken ka za ya bullo kamar wayewar gari: A cikin Littafin Ishaya 60 : 1, Maganar Allah na cewa“tashi ki bada haske, gama haskenki ya zo; darajar Ubangiji kuma ya hau bisa kanki.”Sau da dama mu kan fuskanci matsalolin da sun fi karfin mu, mu damu kwarai da gaske, mukan yi tambaya ko da yaushe ma Ubangiji Allah – cewa Ubangiji har yaushe zan ci gaba haka? Maimakon mu yi ta tunani wadda ba shi da amfani ko kadan, akwai abu guda daya da za ka iya yi AZUMI. Wani lokaci idan kana cikin jama’a, sai ka ga kamar ba ka da damuwa ko kadan, amma da zarar ka koma gida, sai hawaye ya cika maka idanu, dukkan kokarin ka sai ka ce banza kawai, ba ka da bege ko kadan: shawara daya wadda zan ba ka ita ce; ka dauki kwanaki na yin azumi da addu’a, labarin ka zai sauya. Hasken ka za ya bullo kamar wayewar gari. Za ka ci nasara da izinin Allah. Darajar Ubangiji Allah zai hau bisa kanka, ‘gari zai waye maka’.