Azumi da abubuwan da yake koyarwa (3)

3. Sadaka da ciyarwa da sauran ayyukan alheri:An karbo daga Abu Huraira (RA) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Kowace sulhu daga mutane akwai sadaka a kanta. Kowane yinin da rana ta fito a cikinsa idan ka yi adalci a tsakanin mutum biyu sadaka ce. Ka taimaki mutum a kan dabbarsa ka dora shi […]

Azumi da abubuwan da yake koyarwa (3)
Azumi da abubuwan da yake koyarwa (3)

3. Sadaka da ciyarwa da sauran ayyukan alheri:
An karbo daga Abu Huraira (RA) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Kowace sulhu daga mutane akwai sadaka a kanta. Kowane yinin da rana ta fito a cikinsa idan ka yi adalci a tsakanin mutum biyu sadaka ce. Ka taimaki mutum a kan dabbarsa ka dora shi a kanta ko ka dora masa kayansa a kanta sadaka ce. Kalma mai kyau sadaka ce, kuma kowane taku da kake yi zuwa Sallah sadaka ce, kuma ka dauke abin cutarwa daga kan hanya sadaka ce.” Buhari da Muslim suka ruwaito. Annawawi ya ce, “Malamai sun ce: “Abin da ake nufi: Sadaka ta nadabi da kwadaitarwa ne, ba ta wajibci da lizimtarwa ba.” (Sharhu Muslim, Mujalladi na 7 shafi na 95).
4.Ramadan watan Alkur’ani da tsayuwar dare:
Alkur’ani da watan Ramadan
Allah Madaukaki Ya ce: “Watan Ramadan ne wanda aka saukar da Alkur’ani a cikinsa yana shiriya ga mutane da hujjoji bayyanannu daga shiriya da rarrabewa.” k:2:185).
An karbo daga Ibnu Abbas (RA) ya ce: “An saukar da Alkur’ani dukkansa a dunkule lokaci guda zuwa saman duniya a daren Lailatul kadari cikin watan Ramadan, sai ya kasance idan Allah Ya yyi nufin wani abu ya faru a duniya sai Ya saukar da shi daga gare shi, har Ya gama tara shi.” Ibnu Jarir Addabari ya fitar da shi a cikin Tafsirinsa mujalladi na 2 shafi na 145 da isnadi ingantacce.
Kuma daga gare shi ya ce: “Manzon Allah ya kasance mafi kyauta da alheri a tsakanin mutane, kuma ya kasance ya fi yin kyauta a cikin watan Ramadan, lokacin da Jibrila ke ganawa da shi. Ya kasance yana ganawa da shi a kowane dare na Ramadan, sai su yi darasun Alkur’ani. Kuma Manzon Allah (SAW) wajen yin kyauta ya fi iskar sarfa.” Buhari da Muslim suka ruwaito.
Annawawi ya ce: “Abin da za a amfana daga wannan Hadisi na hukunce-hukunce shi ne: An so mudarasar Alkur’ani a wannan wata mai albarka.” (Sharhu Sahihil Muslim, Mujalladi na 15 shafi na 69).
Ibnu Hajrin kuma ya ce: “Daga cikin fa’idojin da za a cirao daga Hadisin akwai: Girmama watan Ramadan ta hanyar kebance shi da fara saukar Alkur’ani a cikinsa, sai kuma sake bijiro da karatun abin da ya sauka daga gare shi. Hakan ya hada da yawan saukar Jibrilu (AS) a cikinsa, kuma a cikin yawan saukarsa akwai karuwar alherai da albarkoki marasa kidayuwa. Kuma wata fa’idar ita ce: lallai falalar lokaci na samuwa ne sakamakon karuwar ayyukan ibada, kuma akwai cewa yawaita tilawa na haifar da karuwar alheri. Kuma a cikinsa an so yawaita ibada a karshen rayuwa da muzakirar alheri da ilimi, domin ba boyayye ba ne karuwar tunatarwa da wa’azantarwa a cikinsa. Kuma a cikinsa akwai dalilin cewa, lallai daren Ramadan ya fi yininsa, kuma abin da ake nufi da tilawa shi ne halarto da zuciya da fahimta yayin karatu, kuma ana zaton hakan ya fi samuwa a cikin dare, saboda abin da ke cikin yini na shagulgula da bijirowar ababen duniya.” (Fathul Bari, mujalladi na 9 shafi na 45).
Wannan ya sanya magabatan kwarai suke tashi tsaye wajen tilawar Alkur’ani, misali Ibrahim An-Nakha’i ya ce, “Al-Aswad yana sauke Alkur’ani a kowane dare biyu na Ramadan, inda yake barci a tsakanin Magariba da Isha’i kawai, kuma yana sauke Alkur’ani a dare shida na sauran watanni.” (Siyar A’alamin Nubla’i, Mujlladi na 4 shafi na 51). Shi kuma Salam bin Abu Mudi’u ya ce: “kattada yana sauke Alkur’ani a (kwana ko dare) bakwai, amma idan Ramadan ya zo a kowane uku. Idan goman karshe suka zo, sai ya rika saukewa a kowane dare.” .” (Siyar A’alamin Nubla’i, Mujlladi na 5, shafi na 276).
Rabi’u bin Sulaiman ya ce: “As-Shafi’i ya kasance yana sauke Alkur’ani sau sittin a cikin watan Ramadan.” (Siyar A’alamin Nubla’i, Mujlladi na 10 shafi na 36). Akwai misalan haka da dama.
Tsayuwar Ramadan:    
An karbo daga Abu Huraira (RA) cewa: “Lallai Manzon (SAW) ya ce: “Wanda ya yi tsayuwar Ramadan (Sallar Tarawihi ko Asham) yana mai imani kuma domin Allah kawai, an gafarta masa abin da ya gabata na zunubinsa.” Buhari da Muslim suka ruwaito.
Aliyu bin Al-Madani ya ce: “Suwaidu bin Ghafalata ya rika yi mana limanci a tsayuwar Ramadan har ya kai shekara 120 a duniya.” (Siyar A’alamin Nubla’i, Mujlladi na 4 shafi na 72).
Yin azumin Ramadan bisa imani kuma domin Allah kawai da yin nafilfilin dare bisa imani kuma domin Allah kawai da raya daren Lailaul kadari bisa imani kuma domin Allah kawai, suna sa mutum ya samu gafara da ’yantuwa daga wuta. Saboda Manzon Allah (SAW) ya ce duk wanda ya yi wadannan abubuwa uku an gafarta masa abin da ya gabata na zunubinsa. Kamar yadda Buhari da Muslim suka ruwaito daga Abu Huraira.
Kafin mu karkare dan wannan rubutu, za mu tunatar da kanmu kan wasu hadisai guda biyu: Hadisi na farko shi ne wanda Manzon Allah (SAW) ya ce: “Idan watan Ramadan ya zo akan bude kofofin Aljanna a rufe kofofin wuta kuma a daure shaidanu.” Muslim ya ruwaito a Babin Falalar Watan Ramadan, a duba Hadisi na 1079. Alkali Iyal ya ce: “Ana iya daukar bude kofofin Aljanna da abin da Allah zai bude ga bayinSa na su samu damar gudanar da ayyukan da’a a wannan wata, wadanda ba a samunsu a waninsa, kamar yin azumi  da tsayuwar dare. Haka kuma kulle kofofin wuta da daure shaidanu na nufin hana mutane damar aikata ayyukan sabo.” (An cirato ne daga Sharhin Muslim na Annawawi, Mujalladi na 7 shafi na 188).
Hadisi na biyu shi ne wanda Manzon Allah (SAW) ya ce: “Allah Ya tubude hancin mutumin da aka ambace ni a wurinsa, amma bai yi min salati ba. Allah Ya tubude hancin mutumin da Ramadan ya shigo masa sannan ya fita amma bai yi abin da za a gafarta masa ba. Kuma Allah Ya turbude hancin mutumin da tsufa ya riski iyayensa suna tare da shi, amma ba su yi sanadin shigarsa Aljanna ba (saboda rashin kyautatawarsa gare su)” (Tirmizi Hadisi na 3545 da Ahmad Hadisi na 7402, kuma Ibnu Khuzaima ya ruwaito makamancinsa, Hadisi na 1888).
’Yan uwa da wannan ya kamata wadannan Hadisai biyu su tayar da tsiminmu wajen ganin mun yi tilawar Alkur’ani da tsayuwar dare da sauran ayyukan alheri a cikin wannan wata mai albarka, domin neman yardar Allah kawai, ba domin riya ko jiyarwa ba.
A karshe muna yi wa ’yan uwa masu yin tahajjud cikin lasifika suna hana sauran mutane yin barci, su yi kokari su guji hakan, domin kada garin neman lada a samu zunubi. Saboda sallar dare ana so ne mutum ya yi ta a boye, a lokacin da sauran mutane suke barci. Idan aka bude lasfika ya zamo an tashi mutane daga barci ke nan, kuma hana mutane barci ko Musulmi ko wadanda ba Musulmi ba, ya saba wa koyarwar Musulunci. Mutane suna da ’yancin yin barci Musulmi ko wadanda ba Musulmi ba a cikin dararen watan Ramadan, kada a tashe su saboda ibadar da Musulunci ya fi so a yi ta a boye.
Allah Ya sa duk ibadar da za mu gudanar a wannan wata mai albarka ta zamo dominSa muka yi, kuma Ya karba mana, Shi Mai iko ne a kan haka, kuma Shi Mai iko ne a kan komai.