Azumi da hukunce-hukuncensa (1)

Daga Umar Ahmed ’Yanleman Ma’anar Azumi: Azumi shi ne kamewa daga cin abinci da abin shad a jima’i da sauran abubuwan da za su iya karya azumi tun daga fitowar alfijir har zuwa faduwar ranar da niyyar da’a da biyayya ga Allah Madaukaki. Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma ku ci, ku sha har silili fari […]

Azumi da hukunce-hukuncensa (1)
Azumi da hukunce-hukuncensa (1)

Daga Umar Ahmed ’Yanleman

Ma’anar Azumi:

Azumi shi ne kamewa daga cin abinci da abin shad a jima’i da sauran abubuwan da za su iya karya azumi tun daga fitowar alfijir har zuwa faduwar ranar da niyyar da’a da biyayya ga Allah Madaukaki. Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma ku ci, ku sha har silili fari ya bayyana a gare ku daga silili baki daga alfijir, sa’annan kuma ku cika azumi zuwa ga dare…”
Wadanda ya kamata su sha azumi:
Shari’a ta amince tsofaffi; maza ko mata su sha azumi, haka marasa lafiya da ba a tsammanin warkewarsu su ma za su sha azumi. Wadanda suke yin aiki mai tsanani za su sha azumi ko wadanda ba su da wata hanyar samun abinci face ta hanyar aiki mai tsanani. Allah Ya ce: “Kuma a kan wadanda suke yin sa da wahala (saboda tsufa ko wata lalura) akwai fansa; su ciyar da mataluci, sai dai wanda ya kara da alheri; to shi ne mafi alheri a gare shi…” (k:2:184).
Duk wadanda aka ambata a sama za su iya shan azumi, musamman idan yana wahalar da su. Don haka aka ba su zabin su rika ciyar da matalauci, a kowace ranar azumi. An kiyasta matalauci zai iya koshi da mudu daya ko rabin mudu na kayan amfanin gona, sai dai idan har za su iya yin azumin an fi son hakan kuma ya fi musu. Allah Ya ce: “Kuma ku yi azumin shi ne mafi alheri gare ku, in kun kasance kuna sani.” (k:2:184).
Ibnu Abbas ya ce: “An umarci tsofaffi su sha azumi, amma su ciyar da matalauta kowace ranar azumi, babu kuma wani abu a kan haka.” Darul- kudni ya ruwaito shi, kuma Hakim ya inganta shi.
Mace mai juna biyu da mai shayarwa idan har suna tsoron yin azumi zai haifar musu da matsala a kansu ko ’ya’yansu, za su iya shan azumi, daga baya su rama, babu wani abu kuma a bayan haka. Wannan shi ne ra’ayin Ibnu Abbas (RA) da Ibnu Umar (RA).
Abu Dawud ya karbo daga Ikrama cewa Ibnu Abbas (RA) yana cewa game da: “Ga wadanda suke yin azumi cikin wahala.” An yi sassauci ga tsofaffi maza ko mata su ajiye ko su sha azumi, amma su ciyar da matalauta a kowace ranar azumi, ga mace mai juna biyu ko mai shayarwa kuma za ta iya ajiye azumi ko ta karya azumin idan tana tunanin wani abu zai iya haifar mata da matsala ko abin shayarwarta, daga baya ta rama.” Bazzar ya ruwaito.
Wadanda za su ajiye azumi amma su biya:
Marar lafiya da rashin lafiyyar ta hana shi azumi amma ana tsammanin warkewarsa ko matafiyi za su iya ajiye azumin amma daga baya za su rama Allah Madaukaki Ya ce: “Sai ya biya adadi daga wasu kwanuka na daban.” (k:2:184).
Rashin lafiyar da aka amince a sha azumi ita ce wacca ta zama dole a sha azumin kuma rashin shan azumin zai iya haifar da matsala wajen samun saukin marar lafiyar. Amma koda azumi zai wahalar da marar lafiya, idan har zai iya yin azumin, to babu laifi ya yi, haka hukuncin yake ga matafiyi.
Fa’idojin azumi:
Sahur:
Yana daga cikin fa’ida ga wanda zai yi azumi ya yi sahur (wato ya ci ko ya sha wani abu), sai dai babu wani abu idan mutum ya bar sahur, sai dai ya bar sunnah, domin Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ku yi sahur, domin akwai albarka a cikin sahur.” Buhari da Muslim suka ruwaito.
Lokacin yin sahur:
Za a iya fara cin abincin sahur daga tsakiyar dare zuwa lokacin da alfijir zai keto. Zaidu bin Sabit ya ce: “Mukan ci abinci sahur da Manzon Allah (SAW) kafin mu shiga Sallar Asuba. Da aka tambayi lokacin da ke tsakanin yin sahur da shiga Sallah. Sai ya ce: “lokacin da za a iya karanta matsakaitan ayoyi hamsin.” Buhari da Muslim suka ruwaito.
Buda baki yayin azumi:
Ana bukatar wanda ya yi azumi ya hanzarta buda baki da zarar rana ta fadi. Manzon Allah (SAW) ya ce: “Mutane ba za su tabe ba matukar suna gaggauta buda baki.” Buhari da Muslim suka ruwaito.
Goge baki da aswaki:
Goge baki da aswaki ana yin azumi, ba ya karya azumin, an ma fi son mai azumi ya rika aswaki yayin da yake azumi. Saboda Manzon Allah (SAW) ya yi umarni da yin aswaki a yayin da ake yin azumi. Haka ya halatta mutum ya yi amfani da man goge baki matukar ba zai hadiye shi ba.
Yawaita kyauta da kuma karatun Alkur’ani:
Akwa fa’ida mai yawa ga mutum ya karanta Alkur’ani da kuma yawaita kyauta a kowane lokaci, amma an fi samun lada mai yawa idan aka aikata su a lokacin azumin watan Ramadan. Nuhari ya ruwaito Ibnu Abbas (RA) yana cewa: “Manzon Allah ya fi kowa kyauta, kuma ya fi aikata haka a lokacin azumin watan Ramadan. Lokacin da yake ganawa da Jibilu yana mai yi masa darasun Alkur’ani. Manzon Allah ya fi iskar sarfa kyauta.”
Ba da abincin buda baki ga mai azumi:
Zaid bin Khalid Al-Juhli ya ce: “Na ji Manzon (SAW) yana cewa: “Duk wanda ya samar da abincin buda baki ga mai azumi, to zai samu cikakken ladan azumin wanda ya ciyar, ba tare da an rage komai daga ladan mai azumin ba.” Tirmizi ya ruwaito, kuma ya ce Hadisi ne ingantacce.
Anas ya ce, wata rana Manzon Allah ya ziyarci Sa’ad bin Ubadah, sai ya kawo masa gurasa da man zaitun, sai Manzon Allah (SAW) ya debi kadan daga ciki, sannan ya ce, “Wadanda suke azumi sun yi buda baki da kai, kuma mutanen kwarai sun ci abincin da ka samar, mala’iku suna roka maka albarka.” Abu Dawuda ya ruwaito.
Sallar Tarawihi ko Asham:
Sallar nafila a cikin dare a lokacin azumin watan Ramadan tana farawa ne daga zarar an idar da Sallar Isha’i har zuwa lokacin da za a yi wutri (wato kafin ketowar alfijir). Ana kiran wannan sallar da Tarawihi ko Asham ko kiyamur Ramadan. Kuma ita Sunnah ce mai karfi ga maza da mata. Manzon Allah (SAW) ya yi Sallar Tarawihi kuma sahabbai da mabiyansa sun gabatar da ita. Abu Huraira ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wanda ya yi tsayuwar Ramadan (ya yi sallar tarawihi ko nafila daga farko har zuwa karshen watan) yana mai imani kuma don Allah kawai, to an gafarta masa dukkan zunubansa da suka gabata.” Muslim ne ya ruwaito.  
Yawan raka’o’in Sallar Tarawihi:
Sallar Tarawihi raka’a goma sha daya ne har da wutri. Wato Sallar Tarawihi raka’a takwas, sai Shafa’i da Wutri guda uku, idan aka hada sun zama raka’a 11. A’isha matar Manzon Allah (SAW) ta ce: “Manzon Allah bai taba wuce raka’a goma sha daya a lokacin Sallar kiyamul Lail a Ramadan ba.”
Sai dai Mazhabar Shafi’iyya da Hanafiyya da kuma Hambaliyya sun ce hakikanin raka’o’in Sallar Tarawihi raka’o’i goma sha biyu ne ban Wutri. Kuma an ruwaito cewa lokacin Amirul Mumina Umar bin Khaddabi (RA) mutane kan yi raka’a 20, kamar yadda Sa’ib ibnu Yazid Sahabi ya ruwaito a cikin littafin Baihaki.

Umar Ahmed ‘Yanleman
Cibiyar Yada A’adun Musulunci (ICC),
Abuja
08066441995