Azumi da hukunce-hukuncensa (1)

Ma’anar Azumi: Da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Shugabanmu Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa. Bayan haka, kasancewar muna shirin shiga watan Azumin Ramadan, nan da ’yan kwanaki muka ga ya dace mu fara gabatar da wani abu kan wannan ibada mai girma. Kamar haka: […]

Azumi da hukunce-hukuncensa (1)
Azumi da hukunce-hukuncensa (1)

Ma’anar Azumi:

Da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Shugabanmu Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa.

Bayan haka, kasancewar muna shirin shiga watan Azumin Ramadan, nan da ’yan kwanaki muka ga ya dace mu fara gabatar da wani abu kan wannan ibada mai girma. Kamar haka:

Ma’anar Azumi:

Azumi shi ne kamewa daga cin abinci da abin sha da jima’i da sauran abubuwan da za su iya karya azumi tun daga fitowar alfijir har zuwa faduwar rana da niyyar yin da’a da biyayya ga Allah Madaukaki. Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma ku ci, ku sha har silili fari ya bayyana a gare ku daga silili baki daga alfijir, sa’annan ku cika azumi zuwa ga dare…”

Wadanda ya halatta su sha azumi:

Shari’a ta wajabta azumi a kan dukan Musulmi baligi mai hankali mace (wadda ta kubuta daga haila ko jinin biki) ko namiji. To amma ta yi wa tsofaffi; maza ko mata sassaucin su sha azumi, haka marasa lafiya da ba a tsammanin warkewarsu. Allah Ya ce: “Kuma a kan wadanda suke yin sa da wahala (saboda tsufa ko wata lalura) akwai fansa; su ciyar da mataluci, sai dai wanda ya kara da alheri; to shi ne mafi alheri a gare shi.” (K:2:184).

Duk wadanda aka ambata a sama za su iya shan azumi, musamman idan yana wahalar da su. Don haka aka ba su zabin su rika ciyar da matalauci, a kowace ranar azumi. An kiyasta matalauci zai iya koshi da mudu daya ko rabin mudu na kayan amfanin gona, sai dai idan har za su iya yin azumin an fi son hakan kuma ya fi musu. Allah Ya ce: “Kuma ku yi azumin shi ne mafi alheri gare ku, in kun kasance kuna sani.” (K:2:184).

Ibn Abbas (RA) ya ce: “An umarci tsofaffi su sha azumi, amma su ciyar da matalauta kowace ranar azumi, babu kuma wani abu a kan haka.” Darul- Kudni ya ruwaito shi, kuma Hakim ya inganta shi.

Mace mai juna biyu da mai shayarwa idan har suna tsoron yin azumi zai haifar musu da matsala a kansu ko ’ya’yansu, za su iya shan azumi, daga baya su rama, babu wani abu kuma a bayan haka. Wannan shi ne ra’ayin Ibn Abbas (RA) da Ibn Umar (RA).

Abu Dawud ya karbo daga Ikrama cewa Ibn Abbas (RA) yana cewa game da: “Ga wadanda suke yin azumi cikin wahala.” An yi sassauci ga tsofaffi maza ko mata su ajiye ko su sha azumi, amma su ciyar da matalauta a kowace ranar azumi, ga mace mai juna biyu ko mai shayarwa kuma za ta iya ajiye azumi ko ta karya azumin idan tana tunanin wani abu zai iya haifar mata da matsala ko abin shayarwarta, daga baya ta rama.” Bazzar ya ruwaito.

Wadanda za su ajiye azumi amma su biya:

Marar lafiya da rashin lafiyyar ta hana shi azumi amma ana tsammanin warkewarsa ko matafiyi za su iya ajiye azumin amma daga baya za su rama Allah Madaukaki Ya ce: “Sai ya biya adadi daga wasu kwanuka na daban.” (K:2:184).

Rashin lafiyar da aka amince a sha azumi ita ce wacce ta zama dole a sha azumin kuma rashin shan azumin zai iya haifar da matsala wajen samun saukin marar lafiyar. Amma koda azumi zai wahalar da marar lafiya, idan har zai iya yin azumin, to babu laifi ya yi, haka hukuncin yake ga matafiyi.

Fa’idojin azumi:

Sahur:

Yana daga cikin fa’ida ga wanda zai yi azumi ya yi sahur (wato ya ci ko ya sha wani abu), sai dai babu wani abu idan mutum ya bar sahur, amma dai ya bar sunnah, domin Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ku yi sahur, domin akwai albarka a cikin sahur.” Buhari da Muslim suka ruwaito.

Lokacin yin sahur:

Za a iya fara cin abincin sahur daga tsakiyar dare zuwa lokacin da alfijir zai keto. Zaidu bin Sabit (RA) ya ce: “Mukan ci abinci sahur da Manzon Allah (SAW) kafin mu shiga Sallar Asuba. Da aka tambayi lokacin da ke tsakanin yin sahur da shiga Sallah. Sai ya ce: “lokacin da za a iya karanta matsakaitan ayoyi hamsin.” Buhari da Muslim suka ruwaito.

Buda baki yayin azumi:

Ana bukatar wanda ya yi azumi ya hanzarta buda baki da zarar rana ta fadi. Manzon Allah (SAW) ya ce: “Mutane ba za su tabe ba, matukar suna gaggauta buda baki.” Buhari da Muslim suka ruwaito.

Goge baki da aswaki:

Goge baki da aswaki ana yin azumi, ba ya karya azumi, an fi son ma mai azumi ya rika aswaki yayin da yake azumi. Saboda Manzon Allah (SAW) ya yi umarni da yin aswaki a yayin da ake yin azumi. Haka ya halatta mutum ya yi amfani da man goge baki matukar ba zai hadiye shi ba.

Yawaita kyauta da kuma karatun Alkur’ani:

Akwai fa’ida mai yawa ga mutum ya yawaita karanta Alkur’ani da yawaita kyauta a kowane lokaci, amma an fi samun lada mai yawa idan aka aikata su a lokacin azumin watan Ramadan. Buhari ya ruwaito Ibn Abbas (RA) yana cewa: “Manzon Allah ya fi kowa kyauta, kuma ya fi aikata haka a lokacin azumin watan Ramadan. Lokacin da yake ganawa da Jibilu yana mai yi masa darasun Alkur’ani. Manzon Allah ya fi iskar sarfa kyauta.”

Umar ’Yanleman

Cibiyar Al’adun Musulunci a Najeriya (ICCN) Abuja Za a iya samunsa ta: 08066441995