Azumi da hukunce-huluncensa (2)
Limamin Masallacin Izala, Mary Slessor, Kalaba Huduba ta biyu Godiya ta tabbata ga Allah Makadaici, Mai tankwarawa, Mabuwayi. Na shaida babu wanda za a bauta masa da gaskiya sai Allah Mai girma Mai yawan gafara, kuma na shaida Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, wanda aka aiko shi a matsayin rahama ga dukkan duniya, […]
Limamin Masallacin Izala, Mary Slessor, Kalaba
Huduba ta biyu
Godiya ta tabbata ga Allah Makadaici, Mai tankwarawa, Mabuwayi. Na shaida babu wanda za a bauta masa da gaskiya sai Allah Mai girma Mai yawan gafara, kuma na shaida Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, wanda aka aiko shi a matsayin rahama ga dukkan duniya, mai bushara da gargadi, Allah Ya kara tsira da aminci a gare shi da alayensa da sahabbansa tsarkaka da aminci mai yawa.
Bayan haka, ya bayin Allah! An so mai azumi ya gaggauta buda-baki da zarar an tabbatar da faduwar rana, kuma ya jinkirta sahur saboda fadinsa (SAW), “Al’ummata ba za ta rabu da alheri ba matukar tana gaggauta buda-baki tana jinkirta sahur.” Ba za a tsaya sai jan da ke sama ya gushe ba bayan faduwar rana. Hakika Manzon Allah (SAW) ya ce, “Idan dare ya juya daga nan rana ta fadi, to hakika mai azumi ya sha ruwa.”
Ku sani mai azumi yana iya karya azuminsa idan ya ci abinci ko ya sha abin sha da gangan da rana, ko ya yi jima’i ko ya yi wasa da matarsa har ya kawo maniyyi, ko ya maimaita kallo har ya zubar da maniyyi, ko ya jawo amai kuma ya hadiye shi. Haka azumi na karyewa saboda fitar jinin haila ko na biki ko ridda ko mutuwa, amma ba ya karyewa saboda fitar maniyyi ta hanyar mafarki. Kuma ya halatta ga mai azumi ya dandani abinci don maslaha ko bukata matukar bai hadiye abincin ba, amma wadansu malamai sun ce makaruhi ne. Idan abincin ya wuce makoshinsa wadansu malamai sun ce azumin ya karye zai rama.
Wanda ya karya ko ya sha azumi daya a watan Ramadan ba tare da uzuri ba, hakika ya aikata babban zunubi kuma ya auka wa babban hadari, koda zai yi azumi na tsawon rayuwarsa, ba zai riski ladar da ya tozartar ba. Saboda abin da aka ruwaito daga Abu Huraira (RA) cewa Annabi (SAW) ya ce: “Wanda ya sha ko ya karya azumin rana daya a Ramadan ba tare da uzuri ko rashin lafiya ba, azumin zamani (shekara) dukkansa ba zai biya shi ba, koda ya azumce shi.”
Ya halatta mai azumi ya yi wanka ko ya kwara ruwa a kansa, ko ya kurkure baki ko ya yi shakar hanci, sai dai kada ya zurfafa a cikinsu, saboda abin da Malik da Ahmad da Abu Dawuda (Allah Ya rahamshe su) suka ruwaito cewa “Manzon Allah (SAW) ya kasance yana kwara ruwa a kansa alhali yana azumi saboda tsananin kishi ko zafin rana.” Sannan a cikin Sahihaini (Buhari da Muslim) an karbo daga A’isha (RA) cewa Annabi (SAW) yakan yi asubanci da janaba alhali yana azumi, sannan sai ya yi wanka.”
Don haka ku ji tsoron Allah ya ku bayin Allah! Ku yi kwadayi zuwa ga Ubangijinku, ku yi azumin watanku, ku yi tsayuwarsa da niyya ta ikhlasi ga Allah Madaukaki. Kuma ku da limamanku ko gabatar da natsuwa a cikin sallolin farilla da tarawihi. Ku san girma da kimar wannan wata. Ku yawaita tilawar Alkur’ani da zikiri da nafilfili da addu’o’i da istigfari da tuba da kyautata wa mabukata da masu uzuri a cikinsa. Kada ku yarda rayuwarku ta zama daidai da lokacin da ba na azumi ba.
Allah Ya sadar da mu ga dukkan abin da muke fata na alherin azumin watan Ramadan da tsayuwarsa. Ya datar da mu zuwa ga dukkan aikin da’a da alheri da kyautatawa. Ya ’yantar da mu daga wuta ’yantarwar da za ta tabbatar mana da shiga Aljanna da samun yardarSa, Shi Allah Majibincin haka ne, kuma Mai iko a kan hakan, don rahamaSa da afuwarSa da karimcinSa da kyautatawarSa.
Ya Ubangiji! Ka daukaka Musulunci da Musulmi, Ka kaskantar da shirka da mushirikai. Ya Ubangiji! Ka kyautata karshenmu a cikin dukkan al’amura, Ka tserar da mu daga dukkan jin kunya da kaskancin duniya da azabar Lahira. Ya Ubangiji! Don iliminKa na gaibu da ikonKa a kan halitta, Ka rayar da mu idan Ka san rayuwa ce mafi alheri a gare mu, kumka Ka kashe mu idan Ka san mutuwar ce mafi alheri a gare mu.
Ya Ubangiji! Muna rokonKa, Ka sanya mana jin tsoronKa a boye da bayyane da furta gaskiya a cikin fushi da yarda da yin adalci (daidaito) a lokacin talauci da wadata. Muna rokonKa ni’imar da ba ta yankewa da sanyin idon da ba ya gushewa da yarda da kaddara da rayuwa mai dadi bayan mutuwa da jin dadin ganin fuskarKa Mai girma da son haduwa da Kai ba a cikin wadata mai cutarwa, ko fitina mai batarwa ba.
Ya Ubangiji! Ka kawata zukatanmu da adon imani, Ka sanya mu daga cikin shiryayyu. Ka sanya mu masu mika wuya ga Sunnar ManzonKa Annabi Muhammad (SAW).
Ya Ubangiji! Ka kara tsira da aminci a kan Annabi Muhammad da alayen Annabi Muhammad kamar yadda Ka yi a kan Annabi Ibrahim da alayen Annabi Ibrahim, Ka yi albarka a kan Annabi Muhammad da alayen Annabi Muhammad, kamar yadda Ka yi a kan Annabi Ibrahim da alayen Annabi Ibrahim a cikin talikai, lallai Kai abin godewa ne Mai girma.
Ya bayin Allah! “Lallai Allah Yana yin umurni da adalci da kyautatawa da bai wa ma’abucin zumunta, kuma Yana hani daga alfasha da abin da aka ki da rarrabe kan jama’a. Yana yi muku gargadi tsammaninku, kuna tunawa. Kuma ku cika alkawarin Allah idan kun yi alkawari, kada ku warware rantsuwoyinku bayan karfafa su, alhali kuma hakika kun sanya Allah Mai lamuncewa a kanku. Kuma lallai Allah ne Yake sanin abin da kuke aikatawa.” (k:16:90-91)
Ku ambaci Allah Mai girma, Ya tuna da ku, ku gode maSa a bisa ni’imominSa, sai Ya kara muku, kuma ambaton Allah ne mafi alherin ayyuka, kuma Allah Yana sanin abin da kuke aikatawa. Tsira da amincin Allah su kara tabbata a kan Manzanni. Kuma godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai.