Azumi: Ganduje ya bukaci a sassauta dokar kulle a Kano

Gwamnan jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje, ya nemi a yi gaggawar sassauta dokar kulle a jihar. Gwamna Ganduje ya nemi gwamnatin tarayya ta sassauta dokar kullen ta mako biyu da Shugaba Muhammadu Buhari ya ayyana ne a jawabin da ya yi wa ‘yan Najeriya ranar Litinin. A cewar gwamnan, sassauta dokar na da mutukar […]

Azumi: Ganduje ya bukaci a sassauta dokar kulle a Kano

Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje, ya nemi a yi gaggawar sassauta dokar kulle a jihar.

Gwamna Ganduje ya nemi gwamnatin tarayya ta sassauta dokar kullen ta mako biyu da Shugaba Muhammadu Buhari ya ayyana ne a jawabin da ya yi wa ‘yan Najeriya ranar Litinin.

A cewar gwamnan, sassauta dokar na da mutukar muhimmanci domin a rage wa al’ummar jihar radadi a watan azumin Ramadan.

Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana haka ne ranar Alhamis a Gidan Gwamnati da ke Kano lokacin da ya kaddamar da wata tawaga ta masana da za ta dafa wa kwamitin yaki da coronavirus na gwamnatin jihar.

Ya ce ya mika bukatarsa ta ganin an saukaka kullen ga kwamitin yaki da cutar na fadar shugaban kasa.

“Muna roko ne a madadin jama’ar mu, wadanda zuwa yanzu ke fama da karancin kayan abinci”, inji gwamnan.

Ya kara da cewa zai so gwamnatin tarayya ta saukaka dokar zuwa wani lokaci domin al’ummar jihar su samu zarafin tanadar kayan abinci, musamman a lokacin da mafi yawan su ke yin azumin watan Ramadan.

“Wannan mataki ne da zai sarara matsanancin halin tattalin arziki a jihar”.

Tawagar masanan da gwamnan ya kaddamar tana karkashin jagorancin Dokta Musa Borodo, shugaban Kwalejin Ilimin Kiwon Lafiya Mai Zurfi ta Kasa, an kuma dora mata alhakin samar da shirye-shirye da tallafa wa kwamitin yaki da COVID-19 na jihar Kano.

Bukatar ta Gwamna Ganduje dai ta zo a daidai lokacin da jihar Kano ta zamo ta biyu a yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus, kana a lokacin da jihar ta fi yawan sabbin masu kamuwa da coronavirus a Najeriya.

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu

Sarakunan gargajiya ba sa tsoron gwamnoni — Sarkin Musulmi