Azumi: Gwamnatin Sakkwato ta bayar da umarnin biyan ma’aikata albashi
Bayanin ya ƙara da cewa, matakin fara biyan albashin zai fara aiki ne daga ranar Juma’a 13 ga watan na Fabarairu.
Gwamnan Jihar Sakkwato Dokta Ahmed Aliyu Sokoto
Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu ya bayar da umarnin biyan ma’aikatan jihar albashin watan Fabarairu nan take, saboda ƙaratowar watan azumin watan Ramadan.
Gwamnan wanda ya sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa ta hannun shugaban sashen yaxa labarai da hulɗa da jama’a na ofishin gwamnan, Abubakar Bawa a yau Alhamis.
- ’Yan sanda sun ceto wanda aka sace da farautar maharan a Gombe
- Fashewar tankar mai ta jikkata mutane da dama a Legas
Sanarwar ta qara da cewa, matakin ya shafi: “ma’aikatan Gwamnatin jiha, ƙananan hukumomi da ma’aikatan hukumar Ilimi ta ƙananan hukumomi, da kuma tsofaffin ma’aikata masu karɓar fansho a duk faɗin jihar”.
Bayanin ya ƙara da cewa, matakin fara biyan albashin zai fara aiki ne daga ranar Juma’a 13 ga watan na Fabarairu.