Azumi: Hasbahta kama samari gandaye 38 a Kano

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama matasa 38 wadanda ba sa yin azumi a kananan hukumomi biyu na jihar a cikin kwana goma na farkon azumi.  Samarin da aka kama sun fito ne daga unguwannin kofar-Ruwa da Kurna da Rijiyar Lemo da Gwammaja a yankin Dala da Fagge.Kwamandan Hisba na karamar Hukumar Fagge Malam […]

Azumi: Hasbahta kama samari gandaye 38 a Kano
Azumi: Hasbahta kama samari gandaye 38 a Kano

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama matasa 38 wadanda ba sa yin azumi a kananan hukumomi biyu na jihar a cikin kwana goma na farkon azumi. 

Samarin da aka kama sun fito ne daga unguwannin kofar-Ruwa da Kurna da Rijiyar Lemo da Gwammaja a yankin Dala da Fagge.
Kwamandan Hisba na karamar Hukumar Fagge Malam Salisu Umar Rijiyar Lemo ya ce a bangaransa sun kama mutum 20 kuma hudu daga cikinsu mata ne. Takwaransa na karamar Hukumar Dala, Mataimakin Kwamanda Malam Abubakar Mati ya ce sun kama mutum 18 a wadannan kwanaki.
Yawancin samarin an kama su da rana ne suna take cikinsu da abinci wasu kuma sun yi tatil da barasa.
Hukumar Hisbah ta ce sun samu nasarar kama samarin ne da taimakon mutanen gari kuma a wani lokacin iyaye da kansu suke kawo musu ’ya’yansu idan suka ki yin azumin.
danladi Aminu daya da ga cikin wadanda aka kama ya shaida wa wakilinmu cewa “A halin yanzu azumina uku amma na san na ragowar mutane ya fi goma. Lokacin da aka kama ni, an kama ni da kwalabar giya ’yar Naira 60 da shalisho da madarar sukudaye a aljihun wandona.”
Shi kuwa Sani Yahaya mai shekara 39 cewa ya yi ‘yan uwansa ne suka kawo shi, amma azumi daya kawai ya sha. Yayin da Yahaya Usman da aka kama yana kwankwadar Koka-kola ya yi zuru ne domin da aka kama shi ya nuna ya je makarantar Islamiyya ne.