Azumi: Mu yi kokari mu ribaci alheran da ke cikinsa

A ranar Litinin da ta gabata ce al’ummar Musulmin duniya suka fara Azumin Ramadan, daya daga cikin ginshikan Musulunci biyar. Kamar yadda kowace ibada take, tana da manufa, sharudda da rukunnai, azumi na daga cikin ibadar da ke sassaita ruhin mutane. Dalili ke nan GIZAGO (08065576011) ya bijiro da wannan tsokaci domin saita tunanin masu […]

Azumi: Mu yi kokari mu ribaci alheran da ke cikinsa

A ranar Litinin da ta gabata ce al’ummar Musulmin duniya suka fara Azumin Ramadan, daya daga cikin ginshikan Musulunci biyar. Kamar yadda kowace ibada take, tana da manufa, sharudda da rukunnai, azumi na daga cikin ibadar da ke sassaita ruhin mutane. Dalili ke nan GIZAGO (08065576011) ya bijiro da wannan tsokaci domin saita tunanin masu azumi. Allah Ya sa mu dace da albarkokin da ke cikin Ramadan, amin.

Ya ku al’umma masu albarka, mun shiga mako na farko a cikin wannan babban bakon wata. Wata mai alfarma da dimbin albarka, watan da wadansu za su dandani yunwa da kishirya masu albarka kuma masu alheri; a yayin da wadansu za su sha bakar yunwa da tsananin kishirwa, amma na banza da wofi.

“Ta yaya mutum zai sha yunwa da kishirwa da sunan ibadar azumi, amma ya tashi a banza ba tare da ya samu wani amfani ba? Kana nufin ba zai samu ladar da ake samu ba?” Na san wadansu za su yi wannan tambayar, don haka bari in sake nanata abin da na fada a baya. Kwarai kuwa, ka fadi da babbar murya, tabbas wadansu ba za su samu wani amfani ko wata lada ba daga azuminsu ba. Za su tashi a fankan-fayau, za su gama shan yunwa da kishirwa a banza. Wadansu kuwa babu shakka za su girbi alheri sakamakon azuminsu, sakamakon yunwarsu da kishirwarsu.

A wannan wata da muka shiga a makon nan, duk wanda ya azumce shi bisa kyakkyawan aiki, ta hanyar bin ka’idojin azumi, kamar yadda Allah Ya shar’anta, shi ne zai samu lada mai kima, zai girbi alheri mai danko. Irin wannan mutum, shi ne wanda ya tsaya kai-da-fata wajen kare hakkokin azumi, wanda ya tsare ibada yadda ya kamata, ya hana kansa aikata dukkan wasu ayyukan assha, ayyukan sabo, ayyukan da Allah Ya hana shi aikatawa. Mutumin da ya kyautata dangantakarsa da al’umma, wanda ya kyautata dabi’unsa, ya kyautata wa iyaye da ’yan uwansa na jini da makwabta da sauran al’umma. Duk mutumin da ya kyautata aikinsa da sana’arsa bisa koyarwar Manzon Tsira a cikin wannan wata da bayansa, shi ne zai dace da cin gajiyar yunwarsa da kishirwarsa. Duk mutumin da ya kare kansa daga cuta ko zaluntar dan uwansa a wannan wata, duk wanda ya kyautata wa iyalinsa a cikin wannan wata mai alfarma, shi ne za a yi wa san barka, domin kuwa zai dace da dukkan albarkokin da ke cikin watan Ramadan.

A hannu daya kuwa, kamar yadda na ambata a baya, akwai wadanda za su sha yunwa da kishirwar banza. Irin wadannan mutane, su ne masu kunnen kashi, wadanda suka kasa bin ka’ida da shari’ar azumi. Su ne za ka ga suna azumi, amma azuminsu bai hana su cutar al’umma ba. Idan ’yan kasuwa ne, irinsu ne za ka ga suna kara tsawwala farashin muhimman kayan bukatar al’umma. Irinsu ne za ka ji suna gulma suna giba suna la’antar bayin Allah. Irin wadannan mutane da za su zama asararru a cikin wannan wata, su ne za su kasance tare da Shaidan, domin kuwa ba za su yi wani yunkuri na kyautata wa al’umma ba.

Duk da suna dauke da azumi, irin wadannan karkatattun mutane, su ne za su kasance cikin sabon Allah da fajirci. Iyakar azuminsu zai kasance daga asuba ne zuwa magariba, daga nan kuma za su fantsama cikin aikata laifuka. Su ne zinace-zinace, su ne shan giya da sauran ayyukan tantiranci. Babu shakka, irin wadannan mutane, su ne za su kasance masu yunwa da kishiryar banza, domin kuwa babu albarka a cikin azuminsu.

Ya ku al’ummar Allah da Annabi, ga wata ’yar shawara nan daga dan uwanku: Mu kasance masu bin kadin gaskiya da adalci. Mu kasance tsarkaka, masu aiwatar da ibadar azumi cikin bin ka’idojin da addininmu ya tanadar. Mu kasance masu kyautata ayyukanmu da sana’o’inmu, mu yi adalci, mu nemi albarka ba yawan riba ba. Mu tausaya wa junanmu domin mu dace da rahamar Allah. Mu kyautata wa iyayenmu da ’yan uwanmu na nesa da na kusa, mu yada kauna da ziyartar juna. Mu yawaita ayyukan alheri a cikin wannan wata.

Fatarmu ita ce, mu dace da albarkar da ke kunshe a cikin wannan Mashahurin Wata – Ramadan Karim! Allah Ya sa mu dace, Ya ba mu ikon kammala ibadojin da ke cikin watan lafiya, Ya ba mu dacewa da aiwatar da dukkan ibadoji a cikinsa bisa dacewa da sunnar Manzon Tsira, Muhammadu (SAW). Allah Ya sanya mu kasance ’yantattun bayi a ciki da bayan Ramadan Karim. Amin, summa amin!