Azumi na gaskiya (2)
Daga Hudubar Sheikh Abdulbari bin Iwad As-SabitiyMasallacin Annabi (SAW), Madina Makarantar azumi tana tarbiyyantarwa kan karfin niyya da gaskiyar niyya. Wadannan su ne ke karya turakun son zuciya su mayar da igiyoyin sharri. Duk wani karfi ko tsari zai yi wuya ga mumini daga mafitar rana zuwa mafadarta yana ci abinci ko abin sha na […]
Daga Hudubar Sheikh Abdulbari bin Iwad As-Sabitiy
Masallacin Annabi (SAW), Madina
Makarantar azumi tana tarbiyyantarwa kan karfin niyya da gaskiyar niyya. Wadannan su ne ke karya turakun son zuciya su mayar da igiyoyin sharri. Duk wani karfi ko tsari zai yi wuya ga mumini daga mafitar rana zuwa mafadarta yana ci abinci ko abin sha na wani lokaci. Za ka gan shi yana rike da akalar rauwarsa yana hana ta fadawa ga sha’awoyi ko wasu abubuwa na son zuciya. Kai yana iya ce wa zuciyarsa na ki. Me ya fi dadi a ce ta kasance cikin neman yardar Allah. Ba ta jima’i da rana ba ta fasikanci. Kuma da jahili zai bata mata ya nemi tayar da hankalinta, zai ya yi linzami ga fisgar sharri da fadinsa: “Ni mai azumi ne!”
Azumi na gaskiya yana tsarkake zuciya daga miyagun kullace-kullace da zunubai da sharruka. Yana kange harsuna daga furta lagawu (maganganun banza) da hana ido ganin haram.
Amma daga cikin masu azumi akwai mai azumin da ba ya da komai sai yunwa da kishin ruwa. Eh, mana, domin muumin da ke barin abinci, amma ya ci naman ’yan uwansa da giba, yana kamewa daga shan abin sha, amma bai kamewa daga karya da algushu da zaluntar mutane, yunwa da kishi kawai ake sha.
Azumi na gaskiya yana sa Musulmi ya zama mai fadaddar zuciya da harshe mai laushi, ya zamo mafi gudu daga husuma da sharri, idan aka yi laifi ya hakura, in aka munanan masa ya yi hakuri. “Masu hakuri kawai ake cika wa ijararsu, ba da wani lissafi ba.” (k:39:10).
Daga cikin albarka wannan wata mai girma, akwai falalar ayyukan kirki. Daga ciki akwai tsayuwar dare, hakika Manzon Allah (SAW) ya kasance yana kwadaitarwa kan Tsayuwar Ramadan yana cewa: “Wanda ya yi Tsayuwar Ramadan yana mai imani da neman lada an gafarta masa abin da ya gabata na zunubinsa.” Sai yin sadaka, saboda Annabi (SAW) ya fi dukkan mutane yin kyauta, kuma ya fi yin kyautar da sadaka a cikin Ramadan lokacin da yake ganawa da Jibrilu kamar yadda Buhari da Muslim suka ruwaito. Kuma an so a gaggauta buda-baki da yin addu’a yayyin shan ruwa. hakika Tirmizi ya ruwaito cewa: “Lallai Annabi (SAW) ya ce: “Mutum uku ba a mayar musu da addu’arsu: Shugaba adali da mai azumi lokacin da yake buda-baki da kuma wanda aka zalunta.”
Ya bayin Allah! Ku yi salati ga Manzon shiriya. Hakika Allah Ya umarce ku da hakan a cikin LittafinSa: “Lallai Allah da Mala’ikunSa suna salati ga Annabi. Ya ku wadanda suka yi imani! Ku yi salati a gare shi, ku yi sallama domin amintarwa a gare shi.” Ya Ubangiji! Ka kara tsira da aminci a bisa bawanKa, kuma ManzonKa Muhammad da alayensa. Kuma Ka yarda da halifofin nan hudu masu shiryarwa…